Hadisi Na Biyar A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musa

0
5

An karɓo daga Aliyyu (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Maganar ƙarshe da Manzon (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi ita ce: “Ku kula da sallah, ku kula da sallah, ku ji tsoron Allah ku kula da haƙƙoƙin waɗanda suke a ƙarƙashinku”.

Abu Dawud da Ibn Majah ne suka rawaito shi.

ƘARIN BAYANI

Wannan hadisi yana daga cikin wasiyyoyin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bar wa al’ummarsa dab da wafatinsa. Ya yi wasiyyar a kula da sallah kuma a kula da haƙƙoƙin bayi da barori da duk waɗanda suke ƙarƙashin mutum.

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A kan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikaken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceHadisi Na Huɗu A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu
Labarin na GabaHadisi Na Bakwai Akan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu