Ƙirƙirar hadisai da yaɗa su daga cikin manyan hanyoyi da ƴan bidi’a suke bi domin yaɗa bidi’o’insu, musamnan hadisai na falalar mutane lokuta da wurare. Ranar Ashura da azuminta da yin kuka a ranar da shafa kan maraya da cika-ciki da sauransu, sun samu rabo mai tsoka a cikin hadisan ƙarya da raunana.
Shaihin malami Abul Faraj Abdurrahman Ibnul Jauzi Rahimahullahi (A.H.S. 510 Y.M.S 597) ya ce: “Waɗansu jahilai masu da’awar su Ahlul sunna ne, sun ƙirƙiro hadisai kan falalar Ashura wai don su muzgunawa ƴan shi’a, duka su biyun ba ruwanmu da su.
Duk da cewa hadisin ya inganta cewa Manzon Allah (S.A.W) ya yi umarni da yin azumin Ashura ya ce yana kankare zunubin shekara, amma ba su gamsu da wannan ba, sai da suka ƙirƙiri hadisai masu ɗimbin yawa a kan hakan.
Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu
Ga wasu daga cikin waɗannan hadisan ƙarya:
1-An karɓo daga Abu Huraira (RA) ya ce, “Haƙiƙa Allah ta’ala ya wajabta wa Banu Isra’ila azumin ranar Ashura, shi ne ranar 10 ga watan Muharram, kuma wanda ya yi azumin wannan yini kuma ku yalwata wa iyalinsa a cikin sa, Allah zai yalwata masa wannan shekarar, ku yi azumi a wannan ranar saboda a ranar Allah ya karɓi tuban Annabi Adam, a ranar Allah ya ɗaukaka Annabi Idris, a ranar Allah ya
kuɓutar da Annabi Ibrahim daga wuta, a ranar Annabi Nuhu ya fito daga jirgin ruwa, a ranar aka saukar da Attaura ga Annabi Musa, a ranar aka fanshi Isma’il daga yanka.
A ranar Allah ya fitar da Annabi Yusuf daga kurkuku, a ranar Allah ya dawowa da Annabi Yakub ganinsa, a ranar Allah ya yaye wa Annabi Ayuba bala’in da ya same shi.
A ranar Allah ya fitar da Annabi Yunusa daga cikin kifi, ita ce ranar da ruwa ya yi hanya ga Bani Isra ila, a ranar Allah ya gafarta wa Annabi Muhammad zunubansa waɗanda suka gabata da waɗanda suka jinkirta, a ranar Annabi Musa ya ƙetare ruwa, a ranar Allah ya karɓi tuban mutanen Annabi Yunusa wanda ya yi azumi a wannan rana, za a kankare masa zunuban shekara arba ‘in.
Ranar farko da Allah ya halitta,ita ce Ashura, ranar Ashura aka fara yin ruwan sama. Rahamar da ta fara sauka a duniya a ranar Ashura ta sauka. Wanda ya yi azumi a wannan rana, kamar wanda ya yi shi ne azumin gaba ɗayan watan ne. Shi ne azumin annabawa.
Wanda ya raya daren Ashura za a ba shi ladan ibadun halittun sammai bakwai. Wanda ya yi sallah raka’a huɗu ya karanta Fatiha da Suratul Ikhlass ƙafa hamsin, Allah zai gafarta masa zunuban shekaru hamsin da suka wuce, da shekaru hamsin masu zuwa, za a gina masa minbari dubu na haske a cikin mala’iku.
Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan
Wanda ya shayar da wani gurbi ɗaya na ruwa, zai kasance kamar wanda bai taɓa yin saɓo ba. Wanda ya ciyar da miskinai a ranar har suka ƙoshi, zai ƙetare siraɗi kamar walkiya. Wanda ya yi sadaka ranar Ashura zai kasance kamar wanda bai taɓa hana mai bara ba.
Wanda ya yi wanka ranar Ashura ba zai ƙara yin rashin lafiya ba, sai dai cutar ajali. Wanda ya sa kwalli ranar Ashura, ba zai yi ciwon idon ba a wannan shekarar. Wanda ya shafa kan maraya a ranar Ashura, za a ba shi ladan wanda ya kyautatawa gaba ɗaya marayun duniya. Wanda ya yi azumin Ashura za a ba shi ladan mala’iku dubu goma. Wanda ya yi azumin Ashura za a ba shi ladan shahidai dubu. Wanda ya yi azumin ranar Ashura za a rubuta masa ladan sammai bakwai.
A ranar aka halicci sammai da ƙassai da duwatsu da koguna da Al’arshi da Alkalami da Lauhul Mahfiz da mala’ika Jibrilu. A ranar Ashura aka ɗaga Annabi Isa zuwa sarna, a ranar aka ba wa Annabi Sulaimam mulki. A ranar Ashura za a yi tashin alƙiyama. Wanda ya gaishe da mara lafiya ranar Ashura za a ba shi ladan wanda ya gaishe da marasa lafiyar duniya.
Shaihin malami Ibnul Jauzi ya ce: “Babu wani mai hankali da zai yi kokonto kan cewa wannan hadisi ƙarya ne. Kuma wanda ya ƙirƙiro shi ya tona wa kansa asiri inda ya ce, “Ranar Ashura ita ce ranar farko da Allah yai halitta, alhali kwanaki tara ne suke gabatar ranar Ashura, to su kuma yaushe aka halicce su?
Kuma wai a ranar aka halicci sama da ƙasa da duwatsu ranar Juma’a, alhali wannan ya saɓawa sahihin hadisi”.
Sannan ga lada mai yawa wanda ya saɓawa ka’idojin shari’a, ya ya za a yi daga azumin rana ɗaya kawai a ba wa mutum ladan Hajji da Umra da shahidai dubu. 2- A wani hadisin na ƙarya, an ce wai a ranar Ashura aka halicci Annabi Adam, aka haifi Annabi lbrahim, aka haifi Annabi Muhammad! Kuma wai a ranar Allah ya daidaita a bisa Al-arshi, kuma wai wanda ya baiwa mai azumin Ashura abin buɗa-baki za a ba shi ladan wanda ya ciyar da gaba ɗayan al’ummar Annabi Muhammad (S.A.W).
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan