Yadda Ake Amfani Da Na’urar Gwajin Ciki (Juna Biyu)

0
7019

Za a iya gwajin ciki da na’ura a kowane lokaci na rana; amma dai da sassafe shi ne mafi dacewa. (fitsarin farko).

Ki yi fitsari a cikin roba ko kwano mai tsabta ko kofi ko duk abin da kike ganin fitsari zai iya zama a ciki.

  1. Sai ki yi fitsari a ciki, daidai gwargwado, wanda na’urar ba za ta lume duka a ciki ba
  2. Sai ki saka na’urar a cikin fitsarin; iya wajan tsinin ake so ya taɓa fitsarin.

Kar ki taɓa wajen nuna sakamakon ko wajan tsinin da hannunki

  1. Sai a tsaida na’urar a tsaye kada fitsarin ya wuce alamar (MAX)
  2. Sai ki bar shi ya ɗan jima a ciki kada ya yi ƙasa da sakon biyar (5)
  3. Bayan ya ɗan jima a ciki, sai ki ciro nau’rar daga cikin fitsarin.
  4. Sai ki sa na’urar ta kalli sama wajan ɓangaran da aka rubuta (MAX).

Idan ba za ki iya riƙe ta a hannu ba, za ki iya ajiye na’urar a waje mai tsafta domin jiran sakamako, ta yadda wajen alamar rubutun MAX din yana kallon sama.

Sakamako

  • Idan ki ka ga layi mai launi wanda ya turu sosai guda biyu; to kina da ciki kamar yadda aka nuna a hoton nan.
  • Idan kuma ki ka ga layuka guda biyu masu launi, amma ba turarru ba, kina da ciki.
  • Idan kuma ki kaga layi ɗaya, to ba ki da ciki.
  • Idan kuma ki ka ga layi ɗaya mai launi turarre ɗayan kuma ba turarre ba shi ma ba ki da ciki.

Karin bayani

  • Yayin da ki ke jiran sakamako, za ki iya lura da layi mai launi yana motsawa a cikin wajen nuna sakamakon, wannan ba matsala.
  • Kina buƙatar jira minti 10 don tabbatar da sakamakon.
  • Ba a amfani da sakamakon da gwajin ya bayar bayan minti 30.
  • Sakamako yakan iya canzawa ya danganta da irin na’urar da ki kai amfani da ita, amma wannan shi ne wanda aka fi amfani da shi.
labarin da ya wuceYadda Ilimi Zai Zama Hasken Rayuwarka
Labarin na GabaMene Ne Hukuncin Yi Wa Mace Kaciya?
Isa Uba Chamo
Nine wanda ya samar da wannan manhajar wikiHausa tare da abokaina domin taimaka hausawa wajen samon ilimin cikin harshen Hausa a sauƙaƙe