Ga Tsoro Ga Ban Tsoro

0
25

“Ubangiji (Allah) ya halicci mutane, Samuel Colt ya dai-daita su”

– Sammuel Colt (1836)

12/08/2024

SHIMFIƊA

Samuel Colt ya faɗi wancan maganar ce bayan ya ƙirƙiri ƙaramar bindigar hannu (Revolver), don ya nuna mahimmancin abin da ya ƙirƙira. Sannan dan ya nuna rashin fifikon wani a kan wani idan kowa ya mallaki bindiga.

Allah SWT ya ce: “Kada ku kashe kawunan ku, Allah mai rahama ne a gareku” (Q4:29). Allah Ta`ala ya ce: “Wanda ya kashe Mumini da gangan, sakamakonsa jahannama zai tabbata a cikinta…” (Q4:93). A Hadisi Manzon Allah SAW ya ce:” Baya tare da mu wanda ya ɗau makami a kan mu”

Waɗannan ayoyi da hadisi da wasu masu tarin yawa suna hani ne game da kisan kai. A ayar farko Allah sai da ya nuna shi kansa mai rahama ne ga bayinsa, wato rashin tausayi ne da imani a zuciya ya ke sanya wani ya kashe mutum ɗan uwansa.

A aya ta biyu kuma Allah ya nuna sakamakon wanda ya yi kisan kai ba da wani dalili na shari`ah ba. Manzon Allah ya faɗi cewa ba ya tare da Shi (Manzon Allah SAW) sannan ba ya tare musulmi gaba ɗaya wanda ya ɗau makami don zubar da jinin musulmi.

MAKAMI A HANNUN FARAR HULA

Hasashe ya tabbatar da cewa a duniya akwai ƙananan makamai kimanin milliyan ɗari Takwas da Saba`in da Biyar (875M) yawancin su a hannun fararen hula da gama-garin mutane.

Kimanin miliyan ɗari (100) daga cikin waɗannan makaman suna Afirka, har da ƙasar mu Najeriya. Sannan kashi Arba`in (40%) na daga cikin mace mace a duniya sanadiyyar amfani da waɗannan makaman ne.

Yaɗuwar ƙananan makamai musamman bindiga, wata matsala ce da duniya take fama da shi a yanzu. Bincike ya tabbatar da cewa abubuwan da suke ke janyo yaɗuwar ƙananan makamai sun haɗa da yaƙe yaƙe -rashin zaman lapiya a ƙasashe daban daban, da ayukan ta`addanci.

Na biyu taɓarɓarewar dokokin ƙasashe da rashin ƙarfin gwamnatoci. Na uku ƙaruwar kamfanonin ƙirƙiran makamai a duniya. Waɗannan dalilai suna janyo ƙaruwar laifuffukan da suka haɗa da kashe-kashe, fashi da makami, kashe kai, ƙaruwar ayyukan ta`addanci da sauransu.

Wannan matsalar ta shafi duniya gaba ɗaya, kullum ayyukan ɓarna da ke afkuwa cikin ƙasashe daban daban suna tabbatar da haka. Manyan ƙasashe irin su Amurka, kullum suna fama da irin waɗannan matsaloloin na amfani da ƙananan makamai wanda sanadiyyar su kullum ake rasa rayuka masu yawa.

Duk da Amurka tana da dokar mallakar makami. Amma wannan matsalar ta addabi Amurka. Babban misali a nan shi ne yadda wani matashi mai suna Thomas Mathew Crooks ya kai wa ɗan takaran shugabancin ƙasar Amurka Donald Trump hari da bindiga, hakan ya yi sanadiyyar tsinke masa saman fatan kunnensa na ɓangaren dama.

Wannan harin ya faru ne ranar 13 ga watan Yuli, 2024 a birnin Pennsylvania yayin da Donald Trump ya ke tsaka da yaƙin neman zaɓensa a zaɓen da ya gabata. Najeriya ɗaya ce daga cikin ƙasashen duniya da kuma Afirka da ke matuƙar fama da wannan matsala ta yaɗuwar ƙananan makamai a hannun gama-garin mutane da fararen hula, musamman a waɗannan shekarun.

Ƙaruwar yaɗuwar makamai a hanun gama-garin mutane a Najeriya za a iya danganta shi daga lokacin da aka fara fasa bututun mai da kuma masu sace fararen fata suna garkuwa da su, musamman a kudancin ƙasar nan a baya.

Zuwa rigingimun addini a Arewa ta tsakiya a farkon shekarun 90s, rigingimun Tibi da Jukun, sannan rigimar Boko haram/ISWAP da `yan ta`adda masu garkuwa da mutane a Arewa maso gabas na ƙasar nan, waɗannan rigingimu sun ta da zaune tsaye da kawo rashin kwanciyar hankali, sun janyo rasa rayuka masu yawa tun daga shekarun 2008 har zuwa yau.

Gwamnatoci, ba za a ce ba sa taɓuka komai ba, amma a gaskiya, ayyukan `yan bindiga daɗi da masu tarzoma sun yi tsanani fiye da ƙima. Mutane har gani suke kamar sun fi ƙarfin hukumomi saboda wasu dalilai.

Samuel Colt da ya ce Allah ya halicci mutane, shi kuma ya daidaita su. So yake ya fito da wani abu mai mahimmanci a fili. Duk wanda yake aikata aikin ta`adanci dan kawai yana riƙe da makami, toh ba fa ya fi wanda ya ke yi wa ta`addancin ƙarfi ba ne, kawai dan yana riƙe ne da makami.

Duk lokacin da wanda ake yi wa ta`addanci shi ma ya riƙe makami, to sai dai kowa yi ta kansa, a lokacin kowa daidai yake da kowa, ba wanda zai yi wa wani ta`addanci, sai dai a yi kare-jini-biri-jini. Don haka kowa sai ya sa kowa cikin zullumi da tsoro.

Masu riƙe da makamai sun sani, idan kowa zai sami makami toh su kansu ba za su ji daɗin rayuwar su ba kamar yadda suke yinta a yanzu, saboda yadda suke farautar sauran mutane, haka suma za a rinƙa farautar su.

A irin wannan yanayi, sai rayuwa ta zama tamkar rayuwar dabbobi a daji wanda Allah ya ba shi sa’a shi ke nan, ba wanda ya ke da tabbacin rayuwarsa. Kowa kullum cikin zullumi da rashin kwanciyar hankali. Rayuwa ta zama ba komai ba, mara daɗi, gajeriya mai cike da tsoro.

RUFEWA

Allah SWT ya sanya rahama a cikin zuciyoyin halittarsa musamman ɗan adam, shi yasa za a ga Uwa yadda take tarairayar `ya`yanta. Wannan rahamar ce ta ke sanya mutum ba ya iya kashe ɗan uwansa haka kawai idan wannan rahamar tana cikin zuciyarsa. Shi ne abinda Allah ya ke nuni da ayar a aka ambata a farko.

Shi kansa Allah da ya halicce mu, bai zama mai ɗaukan ranmu haka kawai ba, sai ajalin da rubuta mana ya yi. Duk wanda ya kashe wani, ya sani ba zai tabbata a duniya ba shi ma wata rana sai ya mutu, ya bar duniyar.

A hadisin Manzon Allah SAW a fili ya faɗi cewa duk wanda ya ɗau makami ya yi kisan kai, to ba ya tare da Mu (wato ba ya tare da Manzon Allah SAW da kuma sauran muminai). Shin idan mutum ya mutu amma ba ya tare da Manzon Allah SAW, ina ne makomar sa?

A aya ta biyu Allah ya ja kunnen mu da nuna mana sakamakon wanda ya aikata aika aikan kisan kai, makomar sa wutar jahannama kuma zai tabbata a cikin ta har abada. Shin wannan abin da Allah ya faɗa shin akwai wanda ya ke ganin ba haka ba ne? Ko kawai tatsuniya ce da labarin ƙanzon kurege?

Duk musulmin da ya yi imanin akwai ƙiyama, akwai hisabi sannan akwai sakamako, to ya tabbata abinda Allah ya faɗi gaskiya ne to ba zai yarda ya kusanci wannan mummunan aikin ba, ba zai yarda ya ɗau ran wani mutum ba.

Dukkan musulmi da yake rayuwa a wannan duniyar, na farko dai ya san zai mutu, toh buƙatar sa in ya mutu ya sami rayuwa mai daɗi da take cike da ni`ima wadda tafi ta nan duniyar. Rayuwar lahira ta aljannah ba a samun ta da saba wa Allah, musamman da mummunan aika aika na kashe ran ɗan Adam.

Allah muna roƙonka ka shiryar da mu, Ka ganar da mu hanya mai kyau, Ka tabbatar da mu a kan ta, sannan Ka ba mu rayuwa mai kyau a nan duniya da rayuwa mafi kyau a lahira. Amin.

Karanta Ayyukan Ta’addancin Matasa A Kano: Aure, Yawan Haihuwa Da Tarbiyya A Wata Mahanga

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Atini Yake (Dysentery)
Labarin na GabaTsokaci A Kan Littafin Salmanu Da Salma
Rabiu Musa Adam
Sunana Rabiu Musa Adam, ni malami ne a sashen koyar da manya na cibiyar Al-Furqan, Kano.