Fassarar huɗubar Juma’a kai daga Masallaci mai alfarma, ta yau Juma’a 9 Jumadal Ula, 1447 H / 31 October, 2025 M
Mai Huɗuba: Sheikh Dr. Mahir bin Hamad Almu’aiƙili
Mai Fassara: Usman Muhammad Ahmad
Huɗuba ta farko:
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Wanda Yake afuwa da yafiya kuma Yake gafarta zunubai, kuma Yake saka wa ma’abota kyautatawa, kuma Yake tunkuɗe musu tsanani da damuwowi, kuma Shi ne wanda Yake talala kuma Yake jinkirtawa don mai laifi ya tuba.
Kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, Tsarkakakke daga tawaya da aibuka Wanda Ya ce: ((Haƙiƙa kuma Mun halicci sammai da ƙasa da abin da yake tsakaninsu cikin kwana shida, kuma wata gajiya ba ta shafe Mu ba)).
Kuma ina shaidawa lallai Annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa, ma’abocin tafkin nan da za a tuzga masa, da matsayin nan da za a masa baiwarsa, duk wanda ya masa biyayya ya tsira, kuma duk wanda ya saɓa masa za a jefa shi a wuta, Allah Ya yi salati a gare shi, da alayensa, da sahabbansa, da matansa, da waɗanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar da halittu za su koma zuwa ga Ubangijinsu a cikinta, kuma Ya yi masa sallama mai yawa.
Bayan haka:
Ya ku taron muminai! Ina muku wasici da ni kaina da tsoron Allah, ku ji tsoron Allah Maɗaukakin Sarki kuma ku masa biyayya, kuma ku sani cewa a gaba gare ku akwai mutuwa da ƙabari, da tashi daga ƙabari da taron filin alƙiyama da sakamako, wasu za su kasance cikin ni’ima da farin ciki, wasu kuma za su kasance cikin azaba da halaka – Allah Ya tsare mu – ((Lallai masu taƙawa suna cikin gidajen aljanna da ƙoramu () A mazauni na gaskiya a wurin Mai mulki, Mai iko)).
Ya ku al’ummar musulmi!
Lallai zuciya ita ce abin da Ubangiji Yake la’akari da shi daga bawa, don haka, duk wanda ya haɗu da Allah da zuciya kuɓutacciya, to haƙiƙa ya rabauta kuma ya tsira, kuma duk wanda ya haɗu da Shi da zuciya mara lafiya, to haƙiƙa ya taɓe kuma ya yi asara, kuma cututtukan zukata suna da yawa, kuma daga cikin mafi hatsarinsu akwai cutar ƙeƙashewa, saboda ma’abocin ƙeƙasasshiyar zuciya, yana kawar da kai daga tuba da komawa zuwa ga Allah, har ma a lokacin saukar bala’i da masifa, sai zuciyarsa ta zama makiyaya ce ta Sheɗan, kuma ba ta karɓar wa’azozin Alƙur’ani.
Allah Maɗaukaki Yana cewa: ((Kuma lallai Mun aika da (manzanni) zuwa ga al’ummomin da suka gabace ka, sai Muka ɗora musu tsananin talauci da cutuka ko sa ƙasƙantar da kai To me ya hana lokacin da musibarmu ta zo musu, su ƙasƙantar da kai? Sai dai kuma zukatansu ne suka ƙeƙashe, Shaiɗan kuma ya ƙawata musu abin da suka kasance suna aikatawa)), kuma Allah Mai girma da ɗaukaka Ya ce: ((To tsananin azaba ya tabbata ga masu ƙeƙasassun zukata da ba sa ambaton Allah. Waɗannan suna cikin ɓata mabayyani)).
Kuma daga cikin sabuban tausasan zuciya da khushu’inta akwai dawwama a kan ambaton Allah, da tuntuntuni cikin ayoyinsa, da tuna mutuwa da magaginta, da ƙabari da matsansa da duhunsa, da ziyartar maƙabartu, da nazari game da lamuran ranar alƙiyama, ya zo a cikin littafin Ɗabaƙatul Hanabila cewa, wani mutum ya ce wa Imamu Ahmad: “Ta yaya zuciyata za ta yi taushi?”, sai ya ce: “Ka shiga maƙabarta, kuma ka shafa kan maraya”.
Ya ku ‘yan’uwa masu imani!
Ita rayuwa gajera ce duk yadda ta yi tsawo, kuma kwanakinta ‘yan kaɗan ne ko yaya suka yawaita, mai dace shi ne wanda ya rayu a cikinta a kan biyayya ga Ubangijinsa, kuma ya yi guzuri a cikinta don ranar haɗuwa da Mahaliccinsa, asararre kuwa, shi ne wanda ya bi son zuciyarsa, kuma ya yi burace-buracen samun kyakkyawar sakamako a wajen Allah, har mutuwa ta afka masa alhali yana cikin gafalarsa.
Kuma bai mata shiri da aiki nagartacce da zai zama sababin kuɓutarsa ba, kuma masu barin wannan duniya iri biyu ne: Mamaci da zai huta daga wahalar wannan gida ta duniya, ya isa zuwa ga hutu a gidan matabbata, da kuma mamaci da bayi da ƙasa za su huta daga sharrinsa, kuma zai tafi ne zuwa ga mammunan makoma, kuma tur da makwanci.
Hadisi ya zo a Sahihu Muslim, daga Abu Ƙatada Allah Ya ƙara masa yarda cewa: Lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bi ta wajen wata gawa, sai ya ce: (Wanda zai huta, da wanda za a huta daga gare shi), sai suka ce: Me kake nufi da wanda ya huta da wanda aka huta daga gare shi? Sai ya ce: (Bawa mumini zai huta daga cutarwar duniya da wahalarta zuwa rahamar Allah, shi kuma fajirin bawa bayi da ƙasa, da bishiyoyi, da dabbobi za su huta daga gare shi).
Ya ku ‘yan uwa masu imani!
Idan mutum ya mutu, to haƙiƙa alƙiyamarsa ta tsaya, domin ƙabari shi ne farkon matakan lahira, Allah Ya sanya shi ya zama wa’azi da izina, wacce zuciya za ta tausasa da ita, kuma ta tunkuɗe gafala, ta kuma taimaka wurin ƙoƙarin aikata ɗa’a, don haka, babu abin da zai amfanar da mutum a ƙabarinsa face aikinsa, hadisi ya zo a Bukhari da Muslim cewa: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Abubuwa uku ne suke bin mamaci, sai biyu su dawo, ɗaya kuma ya wanzu tare da shi: Iyalansa da dukiyarsa da aikinsa za su bi shi, sai iyalansa da dukiyarsa su dawo, sai aikinsa ya tsaya tare da shi)).
Don haka ne Usman Allah Ya ƙara masa yarda ya kasance idan ya tsaya a kan ƙabari, sai ya yi kuka, har sai ya jiƙa gemunsa, sai aka ce da shi: Kana tuna aljanna da wuta ba ka kuka, amma kana kuka saboda wannan? Sai ya ce: Lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Ƙabari shi ne farkon matakan lahira, idan ya tsira a cikinsa, to abin da yake bayansa ya fi shi sauƙi, idan kuwa bai tsira ba, to abin da yake bayansa ya fi shi muni). Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Ban taɓa ganin wani abu mai firgitarwa ba face ƙabari ya fi shi firgitarwa). Tirmizi ne ya rawaito a Sunan ɗinshi.
Ƙabari ya fi shi firgitarwa; saboda mutum yana kasancewa a cikinsa shi ɗaya tilo, ba tare da aboki, ko masoyi, ko mai ɗebe kewa, ko abokin zama ba, kuma akwai matsa a cikinsa, da akwai wani da zai kuɓuta daga wannan matsar, da Sa’adu ɗan Mu’azu ya kuɓuta daga gare ta.
Ƙabari ya fi shi firgitarwa; saboda akwai fitina a cikinsa, kamar fitinar Dujal koma wacce ta fi ta tsanani, ƙabari ya fi shi firgitarwa; saboda shi ko dai ya zama dausayi ne daga cikin dausayoyin aljanna, ko kuma rami ne daga cikin ramukan wuta – Allah Ya tsare mu – saboda haka, duk wanda ya kasance mai kyautatawa, to ƙabarinsa zai zama yalwa da farin ciki a gare shi, duk kuwa wanda ya kasance mai mummunan aiki, to zai zama kewa da baƙin cikin da damuwa a gare shi.
Hadisi ya zo a Bukhari da Muslim, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Shi bawa idan aka sanya shi a ƙabarinsa, kuma abokansa suka juya suka tafi suka bar shi, har ma zai na jin ƙaran takun takalmansu, sai mala’iku biyu su zo masa, sai su zaunar da shi, sai su ce da shi: Me ka kasance kana cewa game da wannan mutumin, wato Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi?
Sai ya ce: Na shaida cewa shi bawan Allah ne kuma Manzonsa, sai a ce da shi: Ka duba mazauninka a wuta, Allah Ya musanya maka shi da wani mazauni a aljanna), Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare ya ce: (Sai ya gan su gaba ɗaya, amma kuma kafiri ko kuma munafiki sai ya ce: Ban sani ba, na dai kasance ina faɗin abin da mutane suke faɗi ne, sai a ce da shi: Ba ka sani ba, kuma ba ka karanta ba, sannan sai a dake shi da guduma ta ƙarfe da ƙarfi a tsakanin kunnuwansa biyu, sai ya yi ihu da ƙarfi ihun da duk wanda yake kusa da shi zai ji ban da mutane da aljanu).
Don haka ne ya zama daga cikin shiriyar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi akwai neman tsari daga azabar ƙabari a kowace salla, kamar yadda ya zo a Sahihu Muslim, daga hadisin Abu Huraira Allah Ya ƙara masa yarda cewa: Lallai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Idan ɗayanku ya yi tahiya, ya nemi tsarin Allah daga abubuwa guda huɗu, ya ce: Ya Allah ina neman tsarinka daga azabar wutar jahannama, da azabar ƙabari, da fitinar rayuwa da mutawa, da sharrin fitinar Dujal).
A’uzu billahi minsh-shaiɗanir-rajim: ((Har sai idan da mutuwa ta zo wa ɗayansu zai ce: “Ubangijina, Ku mai da ni (duniya) mana “Don in yi aiki na gari game da abin da na bari (a rayuwata).” Ina! Lalle wannan kalma ce da yake faɗin ta (da bakinsa). A gabansu kuwa akwai shamaki har zuwa ranar tashinsu Sannan idan aka busa ƙaho to fa babu wata dangantaka (mai amfani) a tsakaninsu a wannan ranar, kuma ba za su tambayi juna ba
To waɗanda ma’aunansu suka yi nauyi waɗannan su ne masu babban rabo. Waɗanda kuwa ma’aunansu suka yi sakayau waɗannan su ne waɗanda suka yi asarar kawunansu, suna masu dawwama a cikin (wutar) Jahannama)). Allah Ya albarkace mu da Alƙur’ani da sunna, kuma Ya amfanar da mu abin da ke cikinsu na ayoyi da hikima, ina faɗin abin da kuke sauraro, kuma ina nema mana gafarar Allah daga kowane zunubi da laifi, don haka ku nemi gafararsa, lallai Shi Ya kasance Mai gafara ne Mai jin ƙan.
Huɗuba ta biyu:
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, dukkan yabo ya tabbata ga Allah Mai tabbatar da zukata, Mai gafarta zunubai, ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah Shi, kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, Mai yaye damuwa, kuma ina shaidawa lallai Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa da Sahabbansa, da aminci mai yawa.
Bayan haka, ya ku taron muminai!
Lallai a cikin ziyartar maƙabartu akwai wa’aztuwa da ɗaukan izina da suke zaburar da mutum a kan tsoro da fargaba, da kuma gaggawa wurin ɗa’a da aiki, kuma duk wanda ya ji tsoro zai yi gaggawa, kuma duk wanda ya yi gaggawa zai kai ga matsayin da yake fata, saboda haka ne Annabi tsira da amincin Allah su tabbbata a gare shi ya kwaɗaitar game da ziyartar maƙabartu don wa’aztuwa da ɗaukar izina, ya zo a cikin Musnad na Imamu Ahmad cewa: Annabi tsira da amincin Allah su tabbbata a gare shi ya ce: (Na kasance ina hana ku ziyartar ƙaburbura.
to ku ziyarce su domin za su tunatar da ku lahira), kuma ziyartar maƙabartu yana da hukunce-hukunce da ladubba, daga cikinsu akwai yin addu’a ga mamata, domin ƙaburbura cike suke da duhu, amma Allah yana haskaka su sakamakon addu’ar salihai daga cikin bayinsa, ya zo a cikin Sahihu Muslim daga hadisin Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda cewa: “Wata mata baƙa ta kasance tana hidima a masallacin Annabi, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbbata a gare shi ya daina ganinta, sai ya tambayi inda take, sai suka ce: ta rasu, sai ya ce: (Me ya sa ba ku sanar da ni ba?)
Kamar dai sun raina lamarinta, sai ya ce: (Ku nuna min ƙabarinta), sai suka nuna masa, sai ya yi mata salla, sannan ya ce: (Waɗannan ƙaburbura a cike suke da duhu ga ma’abotansu, kuma lallai Allah Maɗaukaki yana haskaka musu sakamakon addu’ata gare su), kuma ya kasance daga cikin shiriyarsa tsira da amincin Allah su tabbbata a gare shi, idan ya zo maƙabarta, yana cewa: (Assalamu ala ahlid diyari minal muminina wal musulmin, wa yarhamullahul mustaƙdimina minna wal musta’akhirin, wa inna insha Allahu bikum lalahiƙun), Muslim ne rawaito shi.
Ya ku taron ‘yan-uwa!
Lallai ƙaburbura suna da alfarma, don haka ba ya halatta ga mutum ya taka su, ko ya zauna a kansu, ya zo a cikin Sahihu Muslim cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbbata a gare shi ya ce: (Mutum ya zauna a kan wuta ta ƙone tufafinsa har ta kai ga fatarsa, shi ya fi alheri gare shi sama da ya zauna a kan ƙabari).
Haka kuma, Annabi tsira da amincin Allah su tabbbata a gare shi ya hana fuskantar ƙaburbura yayin salla, da riƙar maƙabartu a matsayin wurin salla, ya zo cikin Bukhari da Muslim daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda cewa: “lallai Ummu Habiba da Ummu Salama Allah ya ƙara musu yarda sun ambaci wani coci da suka gani a Habasha mai ɗauke da hotuna a cikinsa, sai suka ba da labarinsa wa Annabi tsira da amincin Allah su tabbbata a gare shi, sai ya ce: (Lallai su waɗannan mutanen idan wani mutumin kirki ya mutu a cikinsu sai su gina masallaci a kan ƙabarinsa, sannan su zana waɗancan hotunan, kuma waɗannan su ne mafiya sharrin halitta a wurin Allah a ranar alkiyama).
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbbata a gare shi ya ce: (Ku saurara! lallai waɗanda suka gabace ku sun kasance suna riƙar ƙaburburan annabawansu da salihansu a matsayin masallatai, lallai na hane ku daga yin hakan). Muslim ne ya rawaito shi.
Ya ku bayin Allah! Kuma hakan ya kasance ne saboda lallai shi wuce iyaka game da ƙaburburan salihai yana kai mutum ga yin shirka da Allah, ga babban malamin tafsirin nan, Abdullah ɗan Abbas Allah ya ƙara musu yarda, yana faɗi a ƙarƙashin fassarar faɗin Ubangiji Maɗaukaki: ((Kuma suka ce: kada ku bar ababen bautarku, kuma kada ku bar Wadda da Suwa’a da Yagusa da Ya’uƙa da Nasra)), ya ce:
“Waɗannan sunaye ne na wasu mutane salihai daga cikin mutanen Annabi Nuhu, yayin da suka mutu, sai Shaiɗan ya yi wahayi ga mutanensu cewa su kafa hotunansu a wuraren da suke zama, kuma su sa musu sunayensu, sai suka yi haka, ba tare da suna bauta musu ba, har sai da waɗannan suka mutu, kuma ilimi ya bace, sai aka fara bauta musu”. Bukhari ne ya rawaito shi.
Saboda haka, ya kai bawan Allah! ba ya halatta a girmama ƙaburburan salihai, ko a yi gini a kansu, bare kuma a riƙa kewaye su da ɗawafi, ko yanka ko bakance dominsu, ko kiran ma’abotansu, ko neman agaji a wajensu, a neman biyan buƙatu ko yaye damuwa, don haka mu ji tsoron Allah ya ku Musulmi, kuma mu taƙaita da abin da aka shar’anta ziyartar ƙaburbura saboda su, na wa’aztuwa da ɗaukan izina, da sallama ga mamata, da yi musu addu’a, kuma kada mu ƙirƙiro wani abu da zai fusata Ubangiji a wurin.
Haƙiƙa ya zo cikin Musnad na Imām Ahmad cewa, Annabi tsira da amincin Allah su tabbbata a gare shi ya ce: (Na hana ku ziyartar ƙaburbura, to ku ziyarce su, amma kada ku faɗi abin da zai fusata Ubangiji), a wata ruwayar kuma: (Amma kada ku faɗi magana marar kyau), wato: maganar banza, kuma bai dace ga wanda ya je maƙabarta ya shiga cikin zancen duniya ba, ko yin dariya da barkwanci, bari dai, abin da ya dace shi ne ya yi tunani game da halin ma’abota ƙaburburan, haka kuma, ana so ya yi tunani a kan halinsa da makomarsa, da kuma cewa shi ma mai tafiya ne zuwa wurin da suka tafi.
Sannan ku sani, ya ku taron muminai cewa, lallai Allah Ya umarce ku da wani umarni mai daraja wanda Ya fara da kansa, sai Ya ce: ((Lallai Allah da mala’ikunsa suna yin salati wa Annabi. Ya ku waɗanda kuka yi imani, ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa)).
Ya Allah Ka yi salati ga Annabi Muhammad da matansa da zuriyarsa kamar yadda Ka yi salati ga iyalin Annabi Ibrahim, kuma Ka yi albarka ga Annabi Muhammad da matansa da zuriyarsa kamar yadda Ka yi albarka ga iyalan Annabi Ibrahim, lallai Kai ne Sha-yabo Mai girma.
Ya Allah, Ka ƙara yarda da halifofi shiryayyu, Abubakar da Umar da Usman da Ali, da sauran sahabbai da tabi’ai, da waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar alkiyama, kuma Ka haɗa mu tare da su cikin afuwarka da karamcinka da kyautarka, ya Mafi tausayin masu tausayi.
Ya Allah, Ka ɗaukaka Musulunci da Musulmai, Ka sanya wannan ƙasa ta zama mai aminci da kwanciyar hankali da wadatar arziki da yalwa, da sauran ƙasashen Musulmai.
Ya Allah, Ka amintar da mu a ƙasashenmu, Ka shiryar da shugabanninmu da majiɓinta al’amuranmu, kuma Ka ƙarfafi shugabanmu kuma jagoranmu da gaskiya.
Ya Allah Ka datar da shugabanmu hadimin masallatai biyu masu alfarma da gaskiya, tare da magajinsa amintacce zuwa ga abin da ɗaukaka ne ga Musulunci da gyaruwar Musulmai, da kuma abin da alheri ne ga ƙasa da mutane, tare da dukkan shugabannin musulmai.
Ya Allah, Ka kiyaye mana addininmu, da shugabancinmu da tsaronmu, ya Allah Ka datar da jami’an tsaronmu da sojojinmu masu tsaro a kan iyakoki da fagage.
Ya Allah, Ka tabbatar da aminci da zaman lafiya da kwanciyar hankali da nutsuwa ga ‘yan-uwanmu a Falasɗinu.
Ya Allah Ka kiyaye Masallacin Ƙudus, kuma Ka sanya shi ya kasance mai ɗaukaka har zuwa ranar alkiyama.
Ya Allah, Ka yaye damuwar masu damuwa daga cikin musulmai, Ka kwaranye baƙin cikin masu bakin ciki, Ka biya bashin waɗanda ake bi bashi, kuma Ka warkar da marasa lafiya daga cikinmu da na sauran musulmai.
Ya Allah, Ka sanya ƙaburburanmu su zama mafi alherin masauƙanmu bayan mutuwa, Ka sanya su su zamto dausayi daga cikin dausayoyin aljanna, saboda rahamarka, ya Mai ni’imtarwa, ya Ma’abocin ɗaukaka da girma.
Ya Allah, Ka gafarta wa Musulmi maza da mata, da muminai maza da mata, rayayyunsu da matattu.
((Ya Ubangijinmu! Ka ba mu mai kyau a duniya da mai kyau a Lahira, kuma Ka tsare mu daga azabar wuta!).
((Ya Ubangijnmu! Ka karɓa daga gare mu, lallai Kai Mai ji ne kuma Masani. Kuma Ka karɓi tubanmu lallai Kai ne Mai yawan karɓar tuba kuma Mai jin ƙai)).
((Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka Ubangijin buwaya game da abin suke siffanta Shi da shi () Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni () Kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai)).
Karanta Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya Daga Masallaci Mai Alfarma 15th August 2025
Edita @rumasau-kallamu










