Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya daga Masallaci mai Alfarma 7th Nuwamba 2025

0
74

Fassarar huɗubar Juma’a kai daga Masallaci mai alfarma, ta yau Juma’a 16 Jumadal Ula, 1447 H / 07 November, 2025 M

Mai Huɗuba:  Sheikh Dr. Abdallah bin Awwad Aljuhani

 Mai Fassara: Dr Abdullahi Yunusa Machina

Transcribe: Aminu Bashir

Huɗuba ta farko:

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, muna yaba masa, muna neman taimakonsa, kuma muna neman gafararsa. Kuma muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi, to babu mai ɓatar shi, kuma duk wanda ya batar, to babu mai shiryar da shi.

Kuma ina shaidawa lallai babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa. ((Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku ji tsoron Allah matuƙar tsoronsa, kuma kada ku mutu face kuna musulmi)).

((Ya ku mutane! Ku ji tsoron Ubangijinku wanda Ya halicce ku daga rai guda ɗaya, kuma Ya halicci matarsa daga gare shi, kuma Ya yaɗa maza da mata masu yawa daga gare su, kuma ku ji tsoron Allah wanda kuke yi wa juna magiya da shi, kuma ku kiyaye yanke zumunta, lallai Allah Ya kasance Mai kula da ku ne)).

((Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku ji tsoron Allah kuma ku faɗi magana wacce take daidai, Zai gyara muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubanku, kuma duk wanda ya yi ɗa’a ga Allah da Manzonsa to haƙiƙa ya rabauta rabauta mai girma)).

Bayan haka: Ina yi muku wasiyya da ni kaina da duk wanda ya ji maganata da jin tsoron Allah Mai girma da ɗaukaka, wanda Ya halicci bayi, kuma zuwa gare shi makoma take, kuma gare shi ake neman dacewa da shiriya, domin jin tsoronsa riba ce, kuma kariya ce daga azabarsa, kuma hanya ce ta samun kusanci zuwa gare Shi.

Kuma ku kiyayi sauyawar ni’imar Allah gare ku, kuma ku lizimci jama’arku, kuma kada ku kasance ƙungiya ƙungiya, kuma lallai mafi wayo cikin mutane shi ne wanda ya yi wa kansa hisabi, kuma ya yi aiki don abin da ke bayan mutuwa, kuma ya nemi hasken da zai haskaka duhun kabarinsa da shi daga hasken Allah.

Kuma lallai bawa ya ji tsoron Allah Ya tashe shi makaho ranar ƙiyama alhali ya kasance yana gani a duniya. Kuma ku sani cewa lallai duk wanda Allah yake tare da shi, to ba zai ji tsoron komai ba; kuma duk wanda Allah baya tare da shi, to wa zai yi fatan samun kariya daga gare shi koma bayansa.

Ya ku taron muminai maza da mata: Lallai daga cikin manyan ni’imomin Allah ga halittunsa akwai cewa Ya shiryar da su kuma ya nusar da su zuwa ga yin imani da Shi, kuma Ya bayyana musu falalar da Ya yi musu, Allah Maɗaukaki ya ce: ((Gori suke maka don sun musulunta?; to ka ce: “Kada ku yi min gorin musuluntarku; a’a, Allah ne ma zai yi muku gori don Ya shiryar da ku zuwa ga imani, idan kun kasance masu gaskiya”)).

Kuma imani da Allah Maɗaukaki shi ne tabbataccen gaskatawa da ƙudurta cewa lallai Allah shi ne Ubangijin dukkan komai kuma Mamallakinsu, kuma Mahaliccinsu, kuma Mai gudanar da su; da kuma cewa lallai Shi kaɗai ne wanda ya cancanci bauta, kamar Salla da Azumi da addu’a da fata da tsoro da ƙasƙantar da kai da rusunawa, da kuma cewa lallai Shi ne wanda ya siffantu da dukkan siffofin kamala, Wanda Ya tsarkaka daga kowane aibu da tawaya.

Kuma ku sani – Allah Ya ya muku rahama – cewa lallai imani ba wata magana ce mai daɗi da ake furtawa da baki kawai ba, ko wasu burace-burace ba tare da aiki ba, bari dai, shi ne abin da ya tabbata a cikin zuciya kuma ayyuka suka gaskata shi, kuma shi furuci ne da harshe, da gaskatawa da zuciya, da kuma aiki da gaɓɓai da sassan jiki, yana ƙaruwa da ayyukan ɗa’a kuma yana raguwa da ayyukan saɓo.

Kuma imani da Allah Maɗaukakin sarki shi ne tushen dukkan rabauta, domin ba a saukar da littattafai ba, kuma ba a aika manzanni ba, face don tabbatar da shi, da kuma dasa shi a cikin zukata, domin shi ne tushe mafi girma kuma rukuni na farko daga cikin rukunan imani guda shida.

Kuma shi imani kyauta ce daga Allah, kuma ni’ima ce mai girma a rayuwar musulmi, ni’ima ce wacce take tsarkake shekaru, kuma ta sanya albarka a cikin rayuwa, kuma ta bada lamunin samun rabauta a lahira, kuma ta ɗaga darajar ma’abocinta a duniya da lahira, domin a cikinta ne rayuwa ta gaskiya da farin cikin lahira suke.

Kuma wannan ni’ima babu wanda ya san ta sai wanda ya ɗanɗana ta, kuma babu wanda zai ji daɗinta sai wanda ya rayu a cikinta, kuma shi imani haske ne mai shiryarwa mai haskakawa, Allah yana ba da shi ga wanda Yake so daga cikin bayinsa, kuma Yana hana ta ga wanda Ya ga dama.

Allah Maɗaukaki Ya ce: ((Ka ce: “Lallai Allah Yana ɓatar da wanda Ya ga dama, Yana kuma shiryar da wanda ya koma gare Shi)), kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa ya ce: (Duk wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, kuma ya yarda da Musulunci a matsayin addini, kuma ya yarda da Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa a matsayin Annabi, to lallai ya ɗanɗani daɗin imani). Muslim ne ya rawaito shi.

Kuma imani na gaskiya wanda Allah yake so, shi ne tushen kowane alheri, kuma maɓuɓɓugar ɗaukaka, kuma asalin karama da daraja da jagoranci, ma’abocinsa yana rayuwa cikin ɗaukaka da farin ciki da ƙarfi da tabbata a kan hanyar gaskiya.

Kuma haƙiƙa Allah Maɗaukaki ya yi wa masu imani da kuma ɗa’a alkawarin samun nasara da kafuwa a doron ƙasa a cikin bayani mai daraja inda Ya ce: ((Wannan bayani ne don mutane, kuma shiriya ce da kuma wa’azi ga masu taƙawa. Kuma kada ku yi rauni, kada kuma ku yi baƙin ciki, kuma ku ne mafiya ɗaukaka in dai har kun kasance muminai Idan ma wani miki ne ya same ku a jiki, to haƙiƙa miki irinsa ya samu mutanen Makka.

Kuma waɗannan kwanaki ne da muke jujjuya su tsakanin mutane domin Allah Ya bayyanar da waɗanda suka yi imani, kuma Ya riƙi shahidai a cikinku. Allah kuwa ba Ya son azzalumai Kuma don Allah Ya tace waɗanda suka yi imani, kuma don Ya halakar da kafirai.))

Kuma masu imani suna farin ciki da jiɓantar Allah Maɗaukaki a gare su, kuma suna ni’imtuwa da daddaɗar rayuwa, kuma Allah yana son su, kuma muminai ma suna son su, kuma Allah Maɗaukakin sarki yana basu kariya, kuma suna da albishir a rayuwar duniya da lahira, kuma imani na daga cikin mafi girman abababen da ke sanyaya musu zuciya yayin masifu, Allah Maɗaukaki ya ce: ((Ba wata musiba da za ta samu sai da izinin Allah. Duk kuwa wanda ya yi imani da Allah zai shiryi zuciyarsa. Allah kuma Masanin komai ne)).

Kuma su ne ma’abota tsaro da kwanciyar hankali, kuma suna gaggawar zuwa ga imaninsu, kuma suna samun ƙarfi da shi cikin duk abin da ya same su na alheri ko na sharri, na ɗa’a ko na saɓo, na sauƙi ko na wahala. Kuma suna amfana da wa’azi da tunatarwa, kuma suna cikin kulawar Allah Maɗaukaki.

Kuma imaninsu yana kare su daga faɗawa cikin alfasha, kuma da hasken imaninsu suke bambance tsakanin gaskiya da ƙarya, da shiriya da ɓata, da kuma bidi’a da sunna.
Kuma haƙiƙa Allah Maɗaukaki ya yi musu alkawarin samun nasara da kafuwa, kuma su ne ma’abota buwaya da ɗaukaka, Allah Maɗaukaki Ya ce: ((kuma taimakon muminai ya zama haƙƙi ne a kanmu)).

Kuma Mala’ikun da suke ɗauke da Al’arshin Allah Mai rahama suna nema musu gafara, kuma Allah Maɗaukaki yana shiryar da su da imaninsu zuwa hanya madaidaiciya.
Kuma Allah Maɗaukaki yana musu albishir da samun aminci da farin ciki a duniya da lahira, da kuma dawwamammiyar ni’ima a lahira.

Allah Maɗaukaki Ya ce: ((Lalle waɗanda suka ce: “Allah ne Ubangijinmu”, sannan suka tabbata, to mala’iku za su sauko musu lokacin mutuwa suna cewa: “Kada ku tsorata, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi farin ciki da Aljanna wadda kuka kasance ana yi muku alƙawarinta “Mu masoyanku ne a rayuwar duniya da kuma ta lahira; kuma a cikinta za ku samu duk abin da rayukanku suke marmari, za kuma ku samu duk abin da kuke nema a cikinta“Liyafa ce daga Allah Mai gafara, Mai jin ƙai”)).

Bayan haka, ya ku muminai: Haƙiƙa hikimar Allah Maɗaukaki ta hukunta cewa Ya sanya wannan al’umma ta zamo mafi alherin ul’umma wacce aka fitar ga mutane, tana umarni da kyakkyawan aiki, kuma tana hana mummuna, kuma tana imani da Allah.
Kuma Allah tsarki ya tabbata a gare Shi Ya umurce su da yin ayyuka nagari inda Ya ce: ((Kuma ku aikata ayyuka nagari, lallai Ni Masanina abin da kuke aikatawa ne)).

ma’abocinsa dukkan alheri a duniya da lahira, kuma shi garkuwa ne da bawa yake kare kanshi daga sha’awace-sha’awace da shubuhohi da manyan fitintinu da shi, kuma shi waraka ne ga zukata.

Wanda duk lokacin da mutum ya gafala daga barin shi saboda kwaɗayin wani abin duniya mai ƙarewa, sai rayuwarshi ta ƙuntata, kuma zuciyarshi ta kamu da jinya, kuma lallai idan ka dubi dayawa daga cikin koke-koke da damuwowi da baƙin ciki da tsoro da taɓarɓarewar al’amura a rayuwar mutane, za ka ga alamomin nisantar imani da Allah Mai girma da ɗaukaka da bijire wa addininsa da shari’arsa a cikinsu.

A’uzu billahi minash-shaiɗanir-rajim, Bismillahir Rahmanir Rahim: ((Waɗanda suka yi aiki nagari, na miji ne ko mace, alhalin suna muminai, to tabbas za mu raya su rayuwa mai daɗi, kuma tabbas za mu saka musu ladansu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa)).

Allah Ya amfanar da mu da Alƙur’ani mai girma, da shiriyar shugaban Manzanni, ina faɗi abin da kuka saurara, kuma ina nema mana gafar Allah, da sauran musulmi daga kowane zunubi, don haka ku nemi gafarsa, lallai shi Mai yawan gafara ne Mai jin ƙai.

Huɗuba ta biyu:

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah bisa kyautarsa da kyautatawarsa, kuma godiya ta tabbata gare shi bisa falalarsa da ni’imominsa, kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa, ya Allah Ka yi daɗin tsira da aminci ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka:

Ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah, kuma ku tabbatar da imaninku da Ubangijinku, kuma ku sani cewa lallai Imani da Allah Mai girma da ɗaukaka yana sanya yarda da Allah Mai grima da ɗaukaka a zuciyar mumini a kowane hali, kuma yardar bawa ga Mahaliccinsa shi ne farkon sababi daga cikin sabuban natsuwar zuciya, wacce ita ce asalin rabauta, domin da yardar mutum da kansa da abin da Allah Ya ƙaddara masa ne zai samu natsuwa a kan hali da yake ciki yanzu, da kuma yaƙininsa da lahira da sakamako na adalci ne zai samu natsuwa game da gobenshi.

Ma’anar haka, shi ne cewa lallai mumini ba ya cizon yatsa a kan abin da ya shuɗe ta hanyar kuka ko baƙin ciki, kuma ba ya rayuwa cikin baƙin ciki a kan yanayi da yake ciki, kuma ba ya fuskantar gobe da tsoro, saboda a cikin addininsa akwai makamai da zai yi dogaro da su wurin dogewa a kan gwagwarmayar rayuwa, kuma ya fuskanci masifunta da raɗaɗinta da bala’o’inta da su.

Saboda haka, ahir ɗinka kuma ahir ɗinka da rabuwa da yarda da Ubangijinka ko da daidai da ƙiftawar ido ne, sai darajarka ta faɗi a wurinsa, saboda akwai ƙarfin rai da yarda da shi, da natsuwar zuciya a cikin ƙulla alaƙa da Allah, Allah Maɗaukaki Yana faɗi a cikin littafinsa mai girma: ((Ya ku waɗanda kuka yi imani ku nemi taimako ta hanyar haƙuri da salla. Lallai Allah Yana tare da masu haƙuri)).

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan wani abu ya tsananta a gare shi, sai ya garzaya zuwa ga salla, kuma sallarsa ba ta kasance wani abu na al’ada ne kawai da yake yi ba, bari dai, ta kasance kaiwa maƙura ne wurin ganawa da Allah, har ma ya kasance idan lokacinta ya yi sai ya ce wa sahabinsa Bilal Allah Ya ƙara masa yarda: (Ka hutar da mu da salla), wato ita wannan salla ya ku muminai tana ɗauke da makullan rayuwa da wani sashi na hanyoyin rayuwa cikin nutsuwa, don haka, ku dogara da ita saboda ku rabauta.

Ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah, kuma ku kiyaye shi, kuma ku ɗau izina daga waɗanda suka shuɗe gabaninku, kuma ku sani cewa lallai babu makawa sai kun haɗu da Ubangijinku kuma zai muku sakamako a kan ayyukanku ƙananansu da manyansu sai dai abin da Allah Ya gafarta shi, lallai Shi Mai gafara ne Mai jin ƙai, saboda haka, ku kula da kawunanku, ku kula da kawunanku, kuma ku nemi taimakon Allah, kuma ba mu da wata dabara ko ƙarfi face da Allah.

((Lallai Allah da Mala’ikunsa suna salati ga Annabi. Ya ku waɗanda kuka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa)). Ya Allah Ka yi salati ga Annabi Muhammadu da alayen Annabi Muhammadu, kamar yadda Ka yi salati ga Annabi Ibarahim da alayen Annabi Ibrahim, Lallai Kai Sha yabo ne Mai girma, kuma Ka yi albarka ga Annabi Muhammadu da alayen Annabi Muhammadu, kamar yadda Ka yi albarka ga Annabi Ibrahim da alayen Annabi Ibrahim, lallai Kai Sha yabo ne Mai girma.

Ya ku bayin Allah, ku Yawaita salati da sallama ga mafakar halittu a matsaya mai girma ranar alƙiyama, Annabinmu kuma mai cetonmu Annabi Muhammadu tsira da maincin Allah su tabbata a gare shi, kuma Ka masa sallama mai yawa.

Kuma ya Allah Ka ƙara yarda da halifofi huɗu shiryayyu da sauran sahabbai gaba ɗaya, da tabi’ai, da waɗanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako, ya Allah Ka amfanar da mu da son da muke musu, kuma ya Allah Ka tashe mu a cikin tawagarsu, kuma kada Ka kautar da mu daga bin sunnarsu da tafarkinsu, ya Mafi karamcin masu karamci.

Ya Allah Ka ƙarfafi Musulunci da musulmai, kuma Ka ɗaukaka kalmar gaskiya da addini da falalarka, ya Allah Ka taimaki shugabanmu kuma majiɓincin lamuranmu hadimin Masallatai biyu masu alfarma da gaskiya da dace da daidai, kuma Ka datar da shi ga abin da Kake so kuma Ka yarda da shi, kuma Ka yi riƙo da hannunsa zuwa ga ayyukan nagarta da taƙawa.

Ka azurta shi da mashawarta nagartattu, Ka ɗaukaka addininka da kalmarka da shi, kuma ka sanya shi ya taimaki musulunci da musulmai, kuma ka haɗa kan musulmai bisa gaskiya da shiriya ta dalilinsa ya Ubangijin talikai, ya Allah Ka datar da shi da magajinshi da ‘yan’uwansa da mataimakansa zuwa ga gaskiya da shiriya, da dukkan abin da gyara ne ga bayi da ƙasa.

Ya Allah Ka datar da shugabannin musulmai zuwa ga aiki da littafinka da sunnar Annabinka Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Ka sanya su su zama rahama ga bayinka muminai, kuma ya Allah Ka haɗa kawunansu a kan gaskiya ya Ubangijin talikai.

Ya Allah Ka ƙarfafa kariyarka ga ƙasarmu da dukkan ƙasashen musulmi, kuma ya Allah Ka datar da jami’an tsaronmu da masu dako a kan fagage da iyakoki, kuma Ka zama Mai taimako da kawo ɗauki da agazawa da ba da nasarar a gare su.

Ya Allah lallai muna tawassuli da yardarka, Ka tsare mu daga fushinka, kuma muna tawassuli da amincinka, Ka tsare mu daga azabarka, kuma muna neman tsarinka daga damƙarka, ba za mu iya ƙididdige yabo a gare Ka ba, Kana nan kamar yadda Ka yabi kanka.

Ya Allah kada Ka mana uƙuba da munanan ayyukanmu, kuma kada Ka kama mu da abin da wawayen cikinmu suka aikata, kuma Ka isar mana a kan dukkan wani lamari da yake damun mu, kuma Ka zama mai taimako da ba da nasarar gare mu. Ya Allah Ka taimaki addininka, da littafinka, da sunnar Annabinka tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a kowane waje, ya Ubangijin talikai.

Ya Allah lallai muna neman gafararka, lallai Kai Ka kasance Mai yawan gafara ne, Ka sauko mana da ruwan sama mai yawa, ya Allah Ka saukar mana da ruwa, ya Allah Ka saukar mana da ruwa, ya Allah Ka saukar mana da ruwa, ya Allah lallai mu halittu ne daga cikin halittunka, kada Ka hana mana falalarka saboda zunubanmu.

Ya Allah Ka gafarta mana, da iyayenmu, da dukkan musulmai maza da mata, da muminai maza da mata, rayayyu daga cikinsu da mamata. Ya Allah Ka karɓa daga gare mu, lallai Kai Mai ji ne kuma Masani, kuma Ka karɓi tubanmu, lallai Kai Mai yawan karɓar tuba ne Mai jin ƙai.

Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin buwaya daga abin da suke siffanta shi da shi, kuma aminci ya tabbata ga Manzanni, kuma dukkan yabo ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

Karanta Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya Daga Masallaci Mai Alfarma 31st Octoba 2025

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceKira A Kan Haɗin Kai
Labarin na GabaMijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Huɗu