Mai Huɗuba:
Sheikh Dr Saleh Bin Abdullahi Bin Humaid
Mai Fassara:
Dr Abdullahi Yunusa Machina
Shugaban Sashi
Dr Abdurrahman Muhammad Sani Yakubu
Huɗubar Masallaci Mai Alfarma
Mai Girma Sheikh Salih Bin Humaid 26/06/1446H
Yekuwar jahiliyya ce, ku bar ta, domin ita abar ƙyama ce
HUƊUBA TA FARKO
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Wanda Ya kaɗaita da halitta da jujjuya al’amura, (Yanzu wanda ya yi halitta ba zai san ta ba, Alhali Shi ne mai tausasawa Masani?) (Suratul Mulk: 14).
Ina gode masa, tsarki ya tabbata a gare Shi, Ya bayar da yawa, Ya nemi kaɗan.
Kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, shaidawar da ke tseratarwa daga azabar wuta.
Kuma ina shaidawa lallai shugabammu kuma Annabin mu Muhammadu bawan Allah ne kuma manzonsa, mai bushara da kuma gargaɗi, kuma fitila mai haskakawa, tsira da aminci da albarkar Allah su tabbata a gare shi, da Alayensa da Sahabbansa waɗanda suka kasance mataimaka kuma mashawarta na ƙwarai ga Annabinsu, da tabi’ai da waɗanda suka biyo su da kyautatawa, kuma Ya yi daɗin sallama mai yawa a gare su.
Bayan haka, Ya ku mutane! Ina mana wasiyya da jin tsoron Allah, saboda haka, ku ji tsoron Allah, Allah Ya muku rahama, kuma ku sai sani cewa lallai mu’amalantar masoyi da tausasawa tana dawwamar da ƙauna, ga baƙo kuma tana haifar da soyayya, ga maƙiya kuma tana tunkuɗe sharri, ga mai fushi kuma, tana kashe wutar fushi.
Mafiya daraja cikin mutane su ne mafiya saurin nuna ƙauna, mafiya jinkiri wajen nuna ƙyama. Amma marasa daraja cikin mutane, su ne mafiya jinkiri wajen nuna ƙauna mafiya gaggawa wajen bayyana adawa. Kuma ana rigegeniyar samun kusanci da Allah ne da zuciya da kuma ayyuka, ba da ababen hawa ko ƙafafu ba. (Ranar da dukiya ko ƴaƴa ba sa amfani, sai wanda ya zo wa Allah da lafiyayyar zuciya (Suratush-Shu’ara: 88-89).
Ya ku Musulmi!
Akwai wata cuta mai hatsari cikin zamantakewa, wacce ke gadar da ƙiyayya, take haifar da gaba, take tarwatsa alaƙoƙi, take dasa ƙiyayya a zukata, take rarraba kawuman jama’a, take barazana ga zaman lafiya, take yaɗa yanke zumunta. Cuta ce abar ƙyama, wacce ke gina katangar ƙarfe tsakanin wanda aka jarabe shi da ita da sauran mutane, take hana fahimtar juna, take rufe ƙofar tattaunawa, take sa mutum yin hukunci na gama-gari, take sanya shi ya raina masu saɓawa ra’ayinsa, wannan cuta ita ce cutar ta’assubanci da ƙabilanci.
Ya ku bayin Allah!
Ta’assubanci cuta ne mai fatattakawa, shi ne sababin duk wani bala’i, kuma daƙushewar ƙwaƙwalwa ne da toshewar basira, yana makantarwa daga ganin gaskiya, kuma yana katangewa daga bin shiriya, yana ingiza faɗace-faɗace, kuma yana jawo yaƙe-yaƙe, yana rura wutar jayayya, kuma yana tsawaita saɓani.
Ta’assubanci tsauri ne, kuma nisantarwa ne, Ta’assubanci yana jawo ɓoye gaskiya da lulluɓe ta, saboda ma’abocinsa yana ganin cewa gaskiyar, hujja ce ga abokin saɓaninsa. Ta’assubanci yana rage damar isa zuwa ga ingantacciyar mafita, kuma yana yaɗa zalunci da danne haƙƙoƙi, yana raunata al’umma kuma yana yaɗa fitintinu da yaƙe-yaƙen cikin gida.
Ta’assubanci wuce iyaka ne game da mutane, da gidaje, da mazhabobi, da al’umma, da ƙabila, da gari, da ra’ayi, da al’ada, da kafafen yaɗa labarai, da wasanni, da dukkan wani lamari na zamantakewa.
Ya ku Musulmi!
Ku yi duba cikin wannan miƙaƙƙiyar matsaya ta Annabi, haƙiƙa Imamu Muslim ya rawaito a Sahihinsa, daga Hadisin Jabir ɗan Abdullahi Allah Ya ƙara musu yarda, ya ce: Mun kasance tare da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai wani mutum cikin Muhajirai ya bigi wani mutum cikin Ansarawa, sai Ba’ansaren nan ya ce: Ya ku Ansarawa ku taimake ni. Sai shi ma Almahajirin ya ce: Ya ku Muhajirai ku taimake ni, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Me ya sa ake irin wannan yekuwar jahiliyya?” Sannan sai ya ce: “Ku bar ta saboda ita abar kyama ce”. Allahu Akbar!
Ya ku bayin Allah!
Hijira da taimako sifofi ne biyu masu daraja, Muhajirai da Ansarawa kuma su ne mutanen farko ‘yan gaba-gaba, Allah Ya ƙara musu yarda. Amma lokacin da waɗannan mutane biyu suka nufi amfani da waɗannan laƙubba masu daraja kuma siffofi masu girma wajen ƙabilanci, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya zabura ya yi gaggawan shawo kan wannan matsaya da faɗinsa: “Yanzu yekuwa irin ta jahiliyya kuke yi?”.
Wato lallai matsayin Hijira da darajar taimako sun koma siffofin zargi saboda ƙabilanci, bari dai, sun ma zama hanya abar ƙyama abar ƙi, kuma sun zama yekuwa irin ta jahiliyya: (Ku bar ta saboda ita abar ƙyama ce), babu inkari da ya kai wannan siffa tsanani, kuma babu zargi da ya kai wannan siffa girma.
Ya zo a Hadisi ingantacce daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa: “Duk wanda ya yaƙi mutane a ƙarƙashin makauniyar tuta, yana fushi don ƙabilanci, ko yana kira zuwa ga ƙabilanci, ko yana taimakon ƙabilanci, sai aka kashe shi, to, ya mutu irin mutuwar jahiliyya”. A wani lafazi, “Ba ya cikin al’umma ta”. Muslim ne ya rawaito.
Ku saurari wannan kalma mai hikima daga ma’abocin hikima Amru ɗan Aas Allah Ya ƙara masa yarda, an tambaye shi: Me ya sa ka yi jinkirin shiga Musulunci alhali kai mutum ne mai kaifin hankali? Sai ya ce: Lallai mu mun kasance muna tare da wasu mutane da suka fi mu shekaru, hankulansu sun kai duwatsu tabbatuwa, ba su taɓa bin wata hanya ba, da muka bi bayansu a cikinta, face mun same ta mai sauƙi.
Amma yayin da suka ƙaryata Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai muka ƙaryata shi tare da su, kuma ba mu yi tunani cikin lamarinmu ba, sai muka girmama su, amma yayin da suka shuɗe, lamari ya dawo gare mu, sai muka yi duba cikin lamarin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, muka yi tunani game da shi, sai ga shi lamari ne bayyananne, sai Musulunci ya ɗarsu a zuciya ta”. Allah Ya kiyaye ku!
Tabbas babu abin da zai katange gaskiya sai ta’assubanci, da makauniyar biyayya ga iyaye da kakanni, (Yayin da waɗanda suka kafirta suka sanya kishi irin kishin jahiliyya a cikin zukatansu) Alfath: 26, (Lallai mu mun sami iyayenmu a kan wani addini, kuma lallai mu hanyarsu muke kwaikwayo (23) Ya ce da su: Yanzu ko da na zo muku da abin da ya fi zama shiriya a kan abin da kuka sami iyayenku a kansa?” Suka ce: Lallai mu masu kafircewa abin da aka aiko ku da shi ne). Azzukhruf: 23-24.
Ya ku taron Musulmi!
Daga cikin siffofin mai tsananin ta’assubanci a ra’ayi da daskarewar tunani, da karkata zuwa ga kausasa wa abokin saɓani akwai cewa: Shi mai ta’assubanci yana raya cewa shi ne a kan gaskiya, da hujja ko babu hujja, kuma duk wanda ya saɓa masa, to, a kan ɓata yake, yana da hujja ko ba shi da ita, mai ƙabilanci ba ya gani sai abin da yake so ya gani.
Mai ta’assubanci yana rarrabe mutane kuma yana ƙimanta su bisa dangance-dangancensu na addini, da na ƙabila, da yanki da mazhaba da ƙungiya da siyasa. Mai ta’assubanci yana jingina kura-kuransa da aibukansa ga wasu, mai ta’assubanci yana gane gaskiya ne ta hanyar mutane, amma ba ya gane mutane ta hanyar gaskiya.
Mai ta’assubanci ba ya so gaskiya ta kasance tare da ɓangaren da ba nasa ba, domin shi ya taƙaita ne da ra’ayoyinsa da kuma ƙuntataccen hangen nesansa, damuwarsa ita ce gardama da kuma ɗaga kai bisa sauran abokanansa.
Ya ku ‘yan uwa!
A cikin yanayin ta’assubanci, murya tana ɗagawa, ana musayar zargi, za ka ga hakan a bayyane a cikin tarurrukan mutane da dandulansu da wajen haɗuwarsu da tattaunawar su a kafafen watsa labarai da hanyoyin sadarwa, ba tare da mutunta tsarin tattaunawa ko lura da dokokin ɗabi’a da bin tafarkin hikima da ladabi ba.
Kuma an tabbatar da cewa wannan ba zai taɓa zama hanyar da ta dace don warware matsaloli ko haɗuwar zukata ko haɗin kai ba, kuma ba za a iya cimma kyawawan manufofi ta wannan hanyar ba.
Ya ku ‘yan uwa a tafarkin Allah!
Mutum ba a haifarsa da ta’assubanci, sai dai yana koyan ta’assubanci ne daga danginsa da abokansa da makarantarsa da kuma yanayin da yake ciki. Daga nan! Za mu gane cewa domin magance matsalar ta’assubanci to, dole ne a tabbatar da daidaito tsakanin mutane tare da yaɗa al’adun tattaunawa da zaman lafiya da karɓar ra’ayi daban-daban da ƙauna da neman uzuri da yin alheri ga wanda ka sani da ma wanda ba ka sani ba.
Da izinin Allah, abubuwan da za su kare mutum daga ta’assubanci sun haɗa da: Ƙudurcewa ta gaskiya da kuma yaƙinin cewa babu abin da ya ke da kariya daga kuskure sai Littafin Allah, kuma babu wani mutum da ke da kariya daga zunubi sai Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Sai kuma kallon malamai da dattawa a matsayin masu nuni zuwa ga gaskiya, masu isar da saƙon Allah gwargwadon ijtihadinsu da iyawarsu, ba su da kariya daga kuskure, kuma ba su tsira daga yin kuskure da yin ba daidai ba.
Allah Ya kare ku!
Daga cikin hanyoyin guje wa ta’assubanci akwai ƙarfin zuciya da niyya ta gaskiya wajen watsi da al’adun da ba su dace ba da kuma ɗabi’un da suke nesa da gaskiya da adalci.
Dukkan wannan, nauyi ne da ke kan ma’abota ilimi da falala da nagarta da alfarma da masu kula da tarbiyya, da kuma waɗanda suke da kishin al’umma da yin ƙoƙari tuƙuru don gina mutum cikakke da yaɗa nagarta da gyara da kuma yaƙar ɓarna da dukkan nau’ikanta, Kuma kafin komai ma, wajibi ne a samu tsarkin niyya da kyawun zuciya da kaucewa son rinjaye, da cin nasara, da tsere wa fitinar neman yabo da muƙamai, da kuma yaɗa soyayya a cikin gida da makaranta da kasuwa da kafofin yaɗa labarai ta dukkan hanyoyinsa.
Da tsarkakar zuciya daga hassada da kuma kuɓuta daga sonkai. Wannan duk yana tattare cikin kalmar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi mai cike da ma’ana: (Imanin ɗayanku baya cika har sai ya so wa ɗan uwansa abin da yake so wa kansa). Auzu billahi minash shaiɗanir rajim.
(Kuma aboki ba ya tambayar aboki []Alhali kuma ana nuna musu junansu, mai laifi ya riƙa buri ina ma zai fanshi kansa daga azabar wannan rana da ƴaƴansa[] Da matarsa da ɗan uwansa[] da danginsa waɗanda suke kare shi[] dama duk wanda yake a bayan ƙasa baki ɗaya, sannan fansar ta tserar da shi) (Suratul Ma’arij: 10-15)
Allah Ya amfanar da mu da shiriyar LittafinSa, da sunnar AnnabinSa Muhammadu -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah gare mu da sauran Musulmi daga kowanne zunubi da kuskure. Saboda haka, ku nemi gafararSa, domin Shi ne Mai gafara, Mai jin ƙai.
Danna nan don karanta rayuwa
HUƊUBA TA BIYU
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya ɗaga sama ba tare da ginshiƙi ba, kuma ya tabbatar da ƙasa da turaku. Ina gode masa tsarki ya tabbata a gare Shi. Ni’imominSa sun fi ƙarfin iyakancewa da kuma ƙidayawa.
Kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, shaidawa ta gaskiya da yaƙini wanda nake adana ta domin ranar lahira, kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma Annabinmu Muhammadu bawan Allah ne kuma ManzonSa wanda ya ɗaga tutar addini kuma ya yi jihadi matuƙa a kan tafarkin Allah.
Allah Ya yi daɗin tsira da aminci da albarka gare shi da Alayensa da Sahabbansa masu nagarta da ɗaukaka, da Tabi’ai da waɗanda suka bi bayansu da kyautatawa har zuwa ranar ƙarshe. Bayan haka,
Ya ku Musulmi!
Ma’abota ilimi suna cewa: Duk wanda ya riƙe wani mutum ko ma wane ne, sai ya ɗauke shi a matsayin ma’aunin soyayyarsa da ƙiyayyarsa cikin furuci da aiki, to, yana daga cikin waɗanda suka rarrabe Addininsu suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kowace ƙungiya suna fahari da abin da ke tare da su.
Suka ƙara da cewa: Kuma wannan hanya ce ta ma’abota bidi’a da son zuciya ababen zargi, duk wanda ya yi ta’assubanci ga wani ayyananne, to, akwai shubuhar cewa shi ma yana cikinsu. Dukkan wani abu da ya kauce wa da’awar musulunci da Alƙur’ani na dangantaka, ko gari, ko jinsi, ko mazhaba, ko wata ɗariƙa, to, shi yana daga dangogin jahiliyya.
“Kuma duk wanda aikinsa ya jinkirta shi, to, dangantakarshi ba za ta gaggauto da shi ba”, kamar yadda ya zo a Hadisi ingantacce, (Sannan idan aka busa ƙaho to fa babu wata dangantaka (mai amfani) a tsakaninsu a wannan ranar, kuma ba za su tambayi juna ba). Almu’minun 101
Allah Ya kiyaye ku!
Tabbas ta’assubanci shamaki ne mai kauri da yake shiga tsakanin ma’abocinsa da gaskiya, da kuma tsakaninsa da soyayya. Ta’assubanci shamaki ne mai kauri da yake katangewa daga ilimi mai amfani, da aiki nagari, kuma katanga ce mai tsauri da take hana amfanuwa da wasu, kuma yana hana fasahar ƙirƙira.
Kuma babu abin da zai ga bayan ta’assubanci sai yalwan zuci, saboda yalwan zuci shi ne girmama bambance-bambance, da karɓar saɓani. Kuma duk wanda damuwarsa ita ce isa zuwa ga gaskiya, ba wai ba da kariya ga kai ko mazhaba ko ƙungiya ba, to, zai kuɓuta daga ta’assubanci.
Ya Allah ka haɗa kan Musulmi a kan gaskiya da shiriya, ya Allah ka yi albarka ga malamansu, da shugabanninsu, Ka haɗa zukatansu, Ka haɗa zukatunsu da ayyukansu a kan abin da zai yardar da Kai.
Ku yi salati da sallama ga Annabin rahama da aka ba ku, da ni’imar da aka kwaranyo muku, Annabinku Muhammadu Manzon Allah. Haƙiƙa Ubangijinku Ya umurce ku da hakan, kamar yadda ya ce: (Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi, ya ku waɗanda kuka yi imani, ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa) Al’ahzab: 56.
Ya Allah Ka yi daɗin salati da sallama da albarka ga BawanKa kuma ManzonKa Annabinmu Muhammadu, da Alayensa da Matansa da Zuriyarsa. Ka ƙara yarda da halifofi shiryayyu guda huɗu: Abubakar da Umar da Usmanu da Ali, da sauran Sahabbai gabaɗaya, da Tabi’ai da waɗanda suka bi su da kyatatawa har zuwa ranar sakamako, Ka haɗa mu tare da su cikin afuwarKa da baiwarKa da kyautatawarKa ya mafi karamcin masu karamci.
Ya Allah Ka amintar da mu a ƙasashenmu, Ka shiryar da shugabanninmu da majiɓinta lamuranmu, ya Allah Ka ƙarfafi shugabanmu majiɓincin lamuranmu hadimin Masallatai biyu masu alfarma da gaskiya da dace, kuma Ka datar da shi ga abin da Kake so kuma Ka yarda da shi, Ka azurta shi da mashawarta nagari, Ka ƙarfafi AddininKa da shi, kuma Ka ɗaukaka kalmarKa da shi, Ka sanya shi ya zama taimako ne ga Musulunci da Musulmi, kuma Ka haɗa kan Musulmi da shi a kan Gaskiya da shiriya.
Ya Allah Ka datar da shi da yarimansa da ‘yan’uwansa da mataimakansa ga abin da Kake so kuma Ka yarda da shi, Ka yi riƙo da hannunsa zuwa ga ayyukan nagarta da taƙawa, kuma Ka taimake shi ga abin da yake gyara ne ga bayi da ƙasa. Ya Allah! Ka datar da Shugabannin Musulmi bisa aiki da LattafinKa, da Sunnar AnnabinKa tsira da amincin Allah su tabata a gare shi, kuma Ka sanya su masu tausayi ga bayinKa Muminai, Ka haɗe kawunansu a kan shiya, ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka kiyaye ‘yan’uwanmu a Falasɗinu, ya Allah! Ka kare su da kariyarKa, kuma Ka kewaye su da kulawarKa, Ka ɗora karayarsu, Ka kwance ɗaurinsu, Ka yafe laifinsu, Ka warkar da marasa lafiyarsu, Ka jiƙan mamatansu, Ka karɓe su a matsayin shahidai a wurinKa.
Ya Allah! Ka ‘yanta Masallacin Ƙudus daga ‘yan mamaya da ƙwace, ya Allah! Ka ɗaukaka al’amarinsa, kuma Ka ɗaga matsayinsa, Ka ƙarfafa gininsa, Ka tabbatar da sasanninsa, ya Maji roƙo. Ya Allah! Ka taimaki sojojinmu masu dako a kan iyakoki, ya Allah! Ka daidaita ra’ayinsu, Ka ƙarfafa musu gwiwa, Ka ƙarfafi niyyarsu, Ka tabbatar da digadiginsu, Ka ƙarfafa zukatansu, Ka taimake su a kan wanda ya zalunce su, ya Allah! Ka jiƙan shahidansu, Ka warkar da maraunata daga cikinsu, Ka kare iyalansu da zuriyarsu, lallai Kai Maji roƙo ne.
Ya Allah! Ka kare mu daga sharrin masu sharri, da makircin fajirai, da sharrin masu aukowa cikin dare da rana. Ya Ubangijinmu! Ka ba mu mai kyau da duniya da Lahira, Ka kiyashe mu azabar wuta. Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka Ubangijin buwaya daga abin da suke siffantawa, aminci ya tabbata ga Mazanni, dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai.
Domin karanta kakannin manzon Allah SAW danna nan
Edita; Rumasa’u M. Kallamu