Falalar Salla A Masallacin Haramin Makka Da Madina

0
9

An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu anhu) ya ce: Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) yace; “Salla a masallaci na ta fi salla a wani masallaci sau dubu ban da masallaci mai alfarma”(Bukhari 1190 Muslim 1394).

An karɓo daga Abdullahi Ibn Zubair (Radiyallahu anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) yace: “Salla a masallaci na tafi salla dubu a sauran masallatai ban da masallacin harami, kuma salla a masallacin harami tafi salla dubu ɗari a wannan masallacin” (Ahmad, Ibn Khuzaimaha, Suhihul Jami’I 3841).

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Zama A Madina Ya Ke danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Sallar Idi danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceLallai Ne Shugaba Ya Nemi Yardar Allah Shi Kaɗai
Labarin na GabaHadisi Na Ɗaya A ƙan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu