Falalar Biyawa Wani Hajji Ko Umra

0
12

Haƙiƙa duk wanda ya kasancce sanadin aikata alhairi, za a ba shi lada dai-dai da ladan wanda ya aikata wannan aikin ba tare da an rage komai daga ladansa ba..

A kan haka, wanda ya biyawa wani kuɗin aikin hajji ko Umra; za a ba shi lada da za a baiwa wanda ya yi aikata aikin hajji ko umra. Saboda haka, magabata suka kasance suna ɗaukar nayin waɗanda ba su taɓa yin aikin hajji ko umra ba.

Misalin Waɗannan magabata akwai Muslim Ibn Yasar da Abdullahi Ibnul Mubarak; waɗanda suka kasance suna aikin hajji duk shekara, kuma suna tafiya da mutane da suke ɗaukar nauyinsu!.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Karatun Al-Ƙur’ani Ya Ke danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceWaƙoƙin Fada Da Wasu Waƙoƙi Game-Gari
Labarin na GabaFalalar Ayoyi Goma Na Farko Ko Ƙarshen Suratul Kahfi