Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa,
wand muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na
ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.
A yau, za mu koyar da yadda ake yin EGG FRENCH TOAST ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.
Abubuwan buƙata
- Biredin alkama yanka 4
- Fulawa ½ kofi
- Ƙwai
- mai cokali 3 (domin shafa abun suya)
- Sinadarin Ɗanɗano
- yaji
Yadda ake haɗawa
- A cikin buɗaɗɗen kwano, a zuba, fulawa, sinadarin ɗandano da ɗan barkono, a juya a ajiye gefe, a wani kwano mai ɗan zurfi sai a kaɗa ƙwai shi ma, a jiye gefe guda.
- A ɗauko wannan bread, sai a tsoma a cikin ruwan ƙwai, sai a saka shi cikin flour, sannan a mayar cikin ruwan ƙwai, a fito da shi.
- A ɗora abun suya mara zurfi, sai a shafa mai a kai, sannan a saka bread ya gasu, na minti 1-2 ko in launinsa ya koma golden brown.
Domin koyar Yadda ake caramelized onion grilled cheese sandwich dan wannan koren rubutun