Dalilan Da Ke Haddasa Tsawaitar Kwanakin Al’ada

0
8

A likitance, matsakaicin jinin al’ada yana yin tsakanin kwana 3 zuwa 7 ne yake ɗaukewa. Amma akan samu matan da suke yin har kwana 8, kuma duk ana ɗaukarsa normal ne. Idan kuwa ya wuce kwanaki 8 ɗin, to, ya zamo na ciwo wanda ake kira “menorrhagia”.

Abubuwan da suke haddasa menorrhagia su ne:

  • Rashin daidaiton zubar ruwan sinadarai (hormonal imbalance),
  • Ƙarin mahaifa (uterine fibroids),
  • Cututtukan sanyin mara na mata (pelvic inflammatory diseases),
  • Zazzagowar farji (polyps),
  • Kumburin bangon mahaifa (endometriosis),
  • Hujewar bangon mahaifa (adenomyosis),
  • Laulayin magunguna (medication side effects),
  • Yin amfani da magungunan tazarar haihuwa (hormonal contraceptives).

Haka nan a cikin fiƙihun addinin musulunci, jinin al’ada yakan yi kwanaki 3 ne zuwa 7, kamar dai mahangar likitancin zamani. Idan ya wuce haka, to, mace za ta ƙara kwanaki 3 a kai. Kenan zai zamo kwanaki 10. Idan har yanzu bai ɗauke ba, sai ta yi wanka ta cigaba da yin ibadah, kuma mijinta zai iya saduwar aure da ita. Wannan shi ne jinin istihadah, kuma mahangar yawancin malaman Hanafiyya, Hambaliyya, da Shafi’iyya kenan.

Su kuma malaman Malikiyya abinda suka ce shi ne mace za ta yi la’akari ne da kwanakin da ta saba yin al’adarta. Idan suka wuce, kuma jinin bai tsaya ba, to, sai ta ƙara kwanaki 3 kawai a kai. Idan har yanzu bai tsaya ba, to, sai ta yi wankan tsarki ta cigaba da yin ibadah kuma mijinta zai iya saduwar aure da ita. Wannan shi ne bayani a taiƙaice.

Danna nan don karanta Kwanakin Da Mahaifa Ke Yi Ta Rufe Bayan Gama Al’ada

Edita; Rumasa’u M. Kallamu 

   

labarin da ya wuceAbubuwan Da Ke Sa Mace Ta Riƙa Jin Alamun  Juna Biyu
Labarin na GabaHaramcin Zalunci Da Tasirin Addu’ar Wanda Aka Zalunta