Kowane mutum na da ciki, wanda a kusan kowane lokaci mutum kan samu ciwon ciki da ke da nau’i daban-daban. Akwai wasu nau’in ciwon ciki da idan mutum yana jin su to lallai ya hanzarta ganin likita, domin kuwa wannan suna nuni da cewar akwai matsala da kan iya haifar da matsalololi.
Masana sun gudanar da wani bincike a kan jerin alamu na ciwon ciki da ke da matuƙar hatsari ga rayuwar ɗan Adam. Suka ce idan mutum yana yawan jin ƙunar zuciya, kamar zuciyar mutum daga tsakiya tana zafi, musamman idan mutum ya gama cin abinci, to lallai wannan idan ya ɗauki lokaci mutum na samun haka to ya garzaya asibiti mafi kusa da shi.
Idan kuma cibiyar mutum na yawan ciwo, ko da kuwa mutum ya ci abinci ko kuwa, haka idan mutum yana samun ƙunar ciki idan yaci abinci mai zafi ko mai yaji to hakan kan iya zama wata cuta da shan wasu maguguna ba zai magance ba, akwai buƙatar mutum ya ga likita don ya duba ya ga abun da ke damun mutum.
Haka ma idan mutum kan samu ciwon gefen ciki a kai-a kai to shi ma yana da buƙatar ganin likita, domin kuwa ana iya dace da hanjin mutum sun sauka daga kan layin da ya kamata, shi yasa mutum ke samun ciwon. Sai kuma wasu lokuta mutane kan zauna da cutar nan da ke kira dattin ciki, idan kuma ba a gaggauta aiki don cire ta ba, to tana iya haifar da wasu matsaloli da dama a cikin cikin mutum.
Domin karanta Larurar Sanyin Gaba (Genital Infaction) shiga nan
Menene Ƙurajan Al’aura Da Yadda Za A Magance Su
Ƙurajen al’aura wani irin cuta ko matsala da ke addabar fatar al’aurar ɗan Adam mace ko namiji. Kamar yadda kuka sani ne kalar ƙuraje ja ne, sannan wata sa’a ya kan haɗa da yi wa mutum zafi ko ka ƙaiƙayi tare da ɗan kumbura a daidai inda ya fitowa mutum. Idan mutum ya kamu da duk wani cutar ƙuraje wanda bai san da irinsa ba, ya yi ƙoƙari ya garzaya zuwa wurin likita domin ya duba lafiyarsa.
Abubuwa Da Ke Janyo Kurajen Azzakari Ko Al’aura
Abubuwa da dama kan janyowa mutum ƙurajen al’aura/azzakari daga cututtuka da ake kamuwa da su musamman a banɗaki, waɗannan cututtukan a kan kamu da su ta hanyar jima’i ko kuma ta matsalar rashin isasshen ƙarfin sinadarin kariya a jikin bil-adama wato autoimmune disorders. Ga kaɗan daga cikin Abubuwa Da Ke Janyo Kurajen Al’aura:
Cutar Kaiƙayin Al’aurar mace (VAGINAL Yeast Infection):
Irin wannan ƙurajen yakan addabi mata ne a al’aurar su musamman idan suna da wata matsalar infection, yana sa ƙaiƙayi, a kan fata ya yi ja, yakan sa fatar gaba ya kwaye sannan yakan sa mace ta rinƙa fitar da wani irin farin ruwa a gabanta.
Cutar Molluscum Contagiosum:
Wannan cutar yakan addabi fatar mutum, ƙurajen kan fito ƙananun zagayayyun kuraje a al’uarar ɗan Adam. Wani lokacin sukan yi ƙaiƙayi sannan kuma ta yi wa mutum zafi.
Cutar Balantis:
Wannan yakan fito a fatar al’aurar ɗan Adam ko a bisa kan alƙalamin azzakirin, Abun da yakan kawo irin wannan cutar shi ne rashin tsabta. Yana kawo ƙaiƙayi, yakan sa fatar wurin ya yi ja tare da saka al’aura ta fidda wani irin farin ruwa.
Domin karanta Larurar Gaggautowar Saurin Balaga (Precocious Puberty) Danna nan