Cinikin Bayi a Afrika ya ɗauki salo daban-daban kamar yadda na yi bayani a baya babu abin da ya kassara Afrika kamar wannan, ta hanyoyi daban-daban har da canja wa mutane da kuma canja yanayin zamantakewa. To kowanne sashe na Afrika akwai irin nau’in bautar da ake yi ta inda mutane tsakaninsu ma ko kuma su da maƙotansu wasu su je su sato wasu.
Duk wannan abu yana faruwa, kafin masu waɗannan su zo su waɗannan mutanen Portugal, da bayan ma sun zo waɗanda su suka kawo cinikayyar Bayi gadan-gadan da kuma su mutanen Ingila Dens da Dutch su ma suka zo suka shiga cikin wannan ciniki.
A ɓangaren abinda ya kama daga Senegal har zuwa Port Sudan da kuma Yammacin Tsakiyar Sudan (Western Central Sudan) wanda yawancin su duk musulmai ne nan ma an yi cinikin Bayi kuma an bautar da mutane, an yi yaƙe -yaƙe a tsakanin juna, an sayar da mutane, kafin ma zuwan Turawan Portugal da bayan zuwan su.
Saboda su waɗannan da suke wannan sashe na Afrika yawanci idan sun kama Bayin suna amfani da su a tsakanin su wasu kuma su kai su su sayar a tafi da su ta Sahara. Tunda akwai ƙasashe manya a wannan nahiya, kama tun daga kan Ghana, Mali, Songhai da Borno idan aka zo Sokoto ƙasashe ne masu ƙarfi kuma suna da dawakai suna amfani da su akan maƙwabtan su, wannan abu ya ɗauki salo iri-iri da hanyoyi daban-daban, kuma bayan zuwan su da kuma kafin jihadi da kuma bayan jihadin Shehu Ɗan Fodio.
Tunda a cikin tarihi ma wasu daga cikin malamai sun ce ɗaya daga dalilin da yasa su Shehu Ɗan Fodio suka yi jihadi saboda ana ɗiban musulmi ana sayar da su Bayi, wannan abu ya tayarwa da malamai da sauran mutane hankali, kuma da aka yi Daular Sokoto an yi ƙoƙari a hana wannan, waɗanda kawai suka yarda a dinga siyarwa su ne waɗanda ba musulmai ba.
Sun mayar da mutanen da suke ƙananan ƙabilu da suke a tsakiya su aka rinƙa farauta a na sayar da su, wannan abin ya jawo musu baƙin jini a wajen sauran mutane bayan zuwan Mishan, wanda Mishan sun yi amfani da wannan don su ƙarfafi ko su dasa ƙiyayya tsakanin musulmin Arewa da waɗanda ba musulmi ba, cewa dama can iyayen su, idan mutum ya karanta littattafan su zai ga duk irin waɗannan abubuwa da irin abin da suka nuna sai suka mayar da abin cewa, gaba ɗaya a wannan nahiya ba abin da aka yi sai dai kashe su da mayar da su Bayi.
Wannan abu ya shiga zukatan waɗanda ba musulmi ba, wanda daga baya suka zo suka karɓi addinin kirista. Mun san irin waɗannan cewar wancan zamanin da yanzu ba ɗaya ba ne, to amma wannan abin ya yi tasiri gare su da mutanen su ya kuma cunkusa ƙiyayya daban-daban.
A irin wannan yanayi na yadda ake kama Bayi a wannan nahiya ta Sudan, an yi rubuce rubuce daban-daban musamman Turawan da suka zo a da can kafin su yi mulkin mallaka, har da wanda ya ba da labarin irin abubuwan da suka faru a Borno, tunda babbar ƙasa ce kuma suna da ƙarfi a lokacin da suke kai hari wurin irin waɗannan ƙananan ƙabilu, kuma in ba su bayar da kai ba za a ɗebo su da matan su da yaran su, manya-manyan mazan duk a karkashe su. Yara da mata a ɗebo su a sayar da su, waɗanda suke sha’awarsu su mayar da su ƙwarƙwarori ko su bayar da su duk wannann ya faru.
Daga cikin irin waɗannan mutanen da suka ga abin da ya faru akwai Harith Barth, ya faɗi abin da ya gani da Borno ta kai hari Mandara wurin mil 300 daga ƙasar Borno (Kukawa) da irin abubuwan da suka faru aka dinga ɗebo mutanen. Duk wannan sun rubuta su kuma sun bayar da bayanai a kansu a irin wannan yanayi, mun ga shi ma kansa Luggard da sauran su abin da suke ta cewa su Turawan Ingila cewa su sun zo ne don su kawar da cinikin Bayi.
Bayan an yi jihadin Shehu Ɗan Fodio an ci nasara waɗanda aka kama aka mayar da su Bayi, wasu a faɗace-faɗace inda wasu har ma an sayar da su an tafi da su wata ƙasa kamar irin su Nicolas wanda aka sayar da shi har ya kai Rasha, wanda Sir Nicolas ya yi Baptising ɗin sa daga nan ya tafi Spain bayan ya ‘yantar da shi, inda daga nan ya tafi America aka yi yaƙi da shi.
Duk irin wannan ya sa a zagi Shehu Dan Fodio da cewa jihadi ne da irin wannan bautar ta sa aka kama shi ya tafi, duk mun san irin wannan idan ma ƙasashen an samu waɗanda suke son Shehun kuma suka yi amfani da wannan abin da aka yi na jihadi su ma suka tayar da rigima kamar Ab-bahiya a ƙasar Brazil. Wannan duk ya nuna mana irin yadda wannan ƙasa ta Afrika take da yanayin zamantakewa na rigingimu da faɗace-faɗace da abubuwan da suka jawo.
A wannan nahiyar ƙasashen musulmi kenan wanda yawancin Bayin su suna sayar da su ne a Sahara wasu suna shiga Europe ɗin wasu suna shiga nan iyakar Magrib da Misra, yawancin irin waɗannan Bayin nan ake kai su, mun san cewa a irin bauta ta ƙasashen musulmi daban take da ta sauran ƙasashe tun da akwai ƙa’idoji na shari’a waɗanda aka gindaya ba za ka iya yi wa Bawanka ba da sauran su, kuma a can ƙasashen musulmi su na da tsarin cewa, mutum zai iya nemo ‘yancin sa.
Duk da dai a nan nahiyar Sudan abin bai fiye tabbata ba, kuma da su kan su Bayi a nan waɗanda aka haife su a cikin bauta ba a sayar da su saboda sun musulunta sun zama Bayi na gida, wanda a hankali suna shiga gida har ma ya zama su mata a mayar da su ƙwarƙwarori, ko wasu da suke fara mulki suna samun ‘yanci su ma su zama wasu abu kamar yadda muke ganin Bayi a Fada. Wannan yana daga cikin abubuwan da suke faruwa a irin bautar ƙasashen musulmi da kuma nan ƙasar Sudan daban suke da sauran wurare.
Ana ɗiban su su ma ana kai su can ƙasashen Larabawa, wasu su mutu a hanya, wasu kuma su tsira da wahala dai iri-iri. A irin ƙasashensu su ma ana samun bauta da kuma yaƙe-yaƙe a wurare irin su Upper Volta ɗin nan wanda aka ce ita ce ta zama Burkina Faso, wanda waɗannan ƙasashen ma yawanci ba ɓarin musulmi ba ne, har ma aka ga cewa a ƙididdigar da aka yi kashi 17 bisa ɗari na ƙasar gaba ɗaya an bautar da su, kafin Turawa su zo lokacin da aka hana waɗannan abubuwan.
Kowacce nahiya da irin nata, saboda idan ka tafi can ɓangaren su Ethopia nan ma da take babbar ƙasa ce ta kirista su ma sun bautar da mutane wasu an kama su wasu kuma an sayar da su wasu an mayar da su Bayi. Akwai ƙasashen da suke na musulmi su ma suna ɗiban Bayi. Kiristocin Ethopia bayan da suke ɗiba ma suna bautar da su wasu, sun kashe wasu kuma su sayar da su tunda su ba tsarin su ɗaya da musulmi ba.
Su ma musulmin da suke wannan nahiya ta Gabashin Afrika, Bayi ana tafiya da su can Gulf da kuma sauran ƙasashen Asia ma duk ana ɗiban ‘yan Afrika. Waɗannan abubuwa ne da suke dama kafin zuwan Portugees ɗin su fara wannan cinikayya tasu kuma har su canja yanayin yadda ma bautar da ɗiban zai kasance a wannan nahiya ta Afrika.
Kamar yadda na faɗa su ma ƙasashen kurmi yadda suke ɗiban nasu Bayin ya sha bamban da irin namu na Savannah, saboda su ƙasashen kurmin nan yawancin su ba su da dauloli masu ƙarfi in banda irin su Benin da Oyo da France. Waɗannan manyan dauloli kuma da sauran waɗanda suke kusa da su da ‘yan Uyo su idan sun ɗiba sayar wa da Turawa suke, kuma a irin wannan wurare irin su Oyo Bayin ana yayyanka su a ba wa ababen bautar su, tunda duk sun yarda da sadaukarwa saɓanin irin ƙasashen musulmi ko na kirista na gabashin Afrika inda ba a yanka mutum a sadaukar da shi da irin shirka da suka saba.
Wannan yana daga cikin abubuwan da suka sha bamban da bautar musulmi da waɗanda ba musulmi ba, ta inda su musulmi idan sun ɗiba Sahara suke kaiwa su kuma waɗannan suna ɗiba ne su kai Atlantic. Duk wannan kafin zuwan Turawan Potugal waɗanda lokacin da suka zo kurmi suka yi da kuma inda yake suna da ruwa suka dinga ɗiba su da ƙabilun da suke a waɗannan wurare da mutane masu ƙarfi, amma duk kusan abin da ya faru shi ne, su waɗannan ƙasashe da na Arewacin Sudan da na Kudu na can bakin teku suna shigowa tsakiya ne suna ɗiban ƙananan ƙabilu su suke sayarwa.
Saboda haka suka ragargaji wurin da ake cewa Middle Belt ba ma kaɗai a Nijeriya ba, inda ita kanta Middle Belt ɗin an canja mata suna kuma mun san cewa ita Nijeriya ita ta fi kowacce ƙasa yawa da yadda su waɗannan mutanen aka dinga ɗiba, waɗanda suke a bakin teku cikin ƙasa suka dinga shigowa shi yasa za ka ga yawanci su ƙabilar Igbo su aka fi yi wa wannan farmaki tunda su ne suke kusa da Ijo kuma ba su da ƙarfi ba su da tsarin gwamnati irin na waɗannan ƙasashe.
Yawancin waɗanda aka fi kai wa farmaki ana ce musu Stateless ko kuma non-State, waɗanda ba su da tsarin hukuma irin na waɗannan ƙasashe su aka dinga ɗiba ana sayarwa a ko ina a Afrika, su suka shiga wannan tsari na ɗiban Bayi da rashin albarka na cutar da su tun ma dai kafin su Turawan Portugal ɗin su zo, tunda dama mutane suna faɗa a tsakanin su, wannan ya ɗebi wannan wancan ya ɗebi wannan, zuwan Turawa sai ya zama ya canja wannan abin gaba ɗaya yanda za mu gani su kuma wane irin tasiri abin su ya yi wa al’ummar Afrika.
Danna nan don karanta cinkin bayi a tarihin Afrika kashi na huɗu
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu