Yadda Ake Ci-ka-Ƙara

0
1266

Ci-ka-ƙara abin maƙwalashe ne da ya samo asali daga dankalin Turawa. kuma abubuwan da ake amfani da su,ba masu wahalar nema ba ne, kamar yadda Za mu koyar da shi a sauƙaƙe.

Kayan haɗi:

Dankali 10
Kifi tarwaɗa 1
Albasa1
Butter kc 1
Kori
Maggi
Gishiri
Citta
Busasshen biredi
Kwai

Yadda ake haɗawa:

Da farko ki dafa dankali da gishiri, sai ki daka shi, sannan ki cire kan kifi da ƙayar da fata ki dan turara shi da gishiri da kori kamar minti biyar, sannan ki dagargaza shi, ki zuba a kan dakakken dankalin, ki sa buttar da yankakkun albasa da attaruhu, sai maggi da kori da citta, sannan ki juya, sai ki bar shi ya huce, sannan ki dunƙula shi yanda kike so, sai ki tsoma shi a cikin kaɗaɗɗen ƙwanki, sannan ki sa a cikin garin busasshen burodi, ki nannaɗo, sai ki bar shi ya kama kamar minti goma, sannan ki soya a mai. Sai ci.
labarin da ya wuceAsalin Sunan Ƙabilar Ƙuraish
Labarin na GabaYadda Ake Soyayyiyar Taliya