Category: Tatsuniyoyi

  • Tatsuniyar Gizo Da Ɓaure

    Tatsuniyar Gizo Da Ɓaure

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Wata rana ne dai wani sarki yana zance a zuci, yana cewa, ‘Gonata ta ɓaure ta yi kyau. Ɓauren yanzu duk ya nuna. Gara in sami wani ya je ya tsinke mini duk ɓauren, kar in bar shi ya ruɓe a banza. Amma fa wanda zai tsinke ɓauren ba zai sha ba, ko da ɗaya ma.

    Idan ya gama bai sha ba, zan ba shi ‘yata tare da gararta baki ɗaya’. ‎Shi ke nan. Kashegari sai sarki ya sa duk a yi shela a gaya wa mutanen gari sarki yana kiran su a ƙofar fada.

    ‎Mutane suka taru a ƙofar gidan sarki. Sai sarki ya ce, ‘Da ma ba wani abu ya sa na yi kiran ku ba. Gonar ɓaurena ce na ke so a tsinke min, amma ba za a sha ko ɓaure ɗaya ba. Sai dai zan ba wanda ya tsinke ɗin ladan tsinkewar. Watau zan ba shi ‘yata da gararta baki ɗaya.’

    ‎Sai kowa ya ce ba zai iya ba, domin bauren ya cika kyau, ga kuma ƙanshi da zaƙi. Ba wanda zai iya ba tare da ya sha ba. Can, sai Gizo ya zo; ya ce wa sarki, ‘Zan iya. ‎Shi ke nan, sai sarki ya ce, ‘To. Gobe ka yi shiri ka tafi’.

    ‎Da gari ya waye, sai Gizo ya dura ruwa a jallo, ya ɗauki madubi da kuma tsinkensa na sakace. Ya je gonar sarki ya kama tsinkar ɓaure. In yana cikin yi mutane suka zo suka ce, ‘Gizo barka da aiki’; sai ya tsiri tofar da yau, yana cewa, ‘Tuf! Kai wannan ɓaure! Ko warinsa ba na so’.

    ‎Idan sun wuce, sai ya ci gaba da tsinkar ɓauren, yana sha yana zubo wani a ƙasa. Shi ke nan, ashe bai sani ba, wata ‘yar tsuntsuwa tana kallon sa. Da ya gama tsinkar ɓauren tas. Ya sauko zai tafi gida, sai ya ɗauko jallon ruwansa ya kurkure bakinsa, ya ɗauko madubin nan da tsinken sakace, duk ya ciccire ɓauren da ya maƙe masa a haƙorinsa.

    Bakinsa ya yi tas, kamar bai ci kome ba. Sai sarki ya aiko mutane don su debe ɓauren da Gizo ya tsinke. Suka zo suka sami Gizo suka ce, ‘Sannu da aiki, Gizo’. ‎Ya ce, ‘Yauwa’. ‎Suka ce, ‘Har ka gama? Sai ya ce, ‘I. Amma da ƙyar’.

    ‎na gama. Kamar na yi amai, saboda warin ɓauren nan. Warin duk ya cika mini ciki’. ‎Sai suka zuzzuba ɓauren a buhunhuna suka tafi su kai wa sarki. Da suka je gida, sai sarki ya tambaye su labarin Gizo da tsinkar ɓaure. Suka ce, ‘Ai, yallaɓai, Gizo bai sha ɓauren nan ba, domin mun ga muna zubawa a buhu yana tofad da yau..

    Kuma da muka ce da shi, ‘Me ya sa ka ke zubad da yau?’ Sai ya ce warin ɓauren ne ya cika masa ciki. Sun gama faɗin haka ke nan, sai ga Gizo ya zo gidan sarki. Sarki ya ce da shi, ‘To, Gizo. Ka yi aiki mai kyau. Sai kuma ka je gida ka gyaggyara, za a kawo amarya da gararta.’

    ‎Shi ke nan. Gizo ya je gida ya gyaggyara sarai. Aka ɗauko amarya da gara aka zo da ita gidan Gizo. Kafin ‘yan ɗaukar amarya su tafi gida, sai suka ji tsuntsuwa tana waƙa tana cewa: ‘Kai Gizo, kai Gizo, A can ka ci ɓaurenka, Har ka kurkure bakinka, Har ka manto jallonka…’

    ‎Tana ta faɗar haka har sai mutanen suka ce, ‘Kai, ku tsaya mu ji abin da tsuntsuwar can take faɗa. ‎Sai Gizo ya ce da su, ‘Kai, ku rabu da ita don Allah, shirmenta ta ke yi’. ‎Sai mutanen suka ce, ‘Wane irin a rabu da ita? Kai! Mu tsaya mu ji’.

    ‎Shi ke nan, sai ‘yan kawo gara da amarya suka ji tana cewa: ‘Kai Gizo kai Gizo, A can ka ci ɓaurenka, Har ka kurkure bakinka, Har ka manto jallonka…’‎Sai suka ce, ‘La’ila! Ashe da ma ka ci ɓauren ka ce ba ka ci ba?’

    ‎Sai suka yi ta surutu da hayaniya. Shi ke nan. Sai suka mayad da amarya da gararta gida su ka gaya wa sarki abin da ya faru.

    ‎Shi ke nan. Ƙurunƙus

    ‎Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Danna nan don karanta ‎Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum

    Edita@rumasau-kallamu

  • ‎Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum

    ‎Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum

    ‎‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Wata barewa ce, sai ta rikiɗa, ta zama mace kyakkyawa. Sai ta ɗauki ɗan kwatashinta ta ɗora a ka ta tafi tsakiyar karofi ta ajiye. Da ta ajiye, sai ta ce duk wanda ya jefa ’yar tsakuwa ta buɗe kwatashin nan, shi ne mijinta.

    ‎Sai wannan ya ɗauki tsakuwa ya jefa bai buɗe ba, wancan ya jefa tsakuwa bai buɗe ba. Sai aka sami wani ya jefa ’yar tsakuwa, sai ya buɗe. Sai ta ce ta sami miji, shi za ta aura. Sai suka tafi garin ita yarinyar, wurin iyayenta za a ɗauro mata aure da wannan mutumin.

    ‎Sai aka ɗaura musu aure ta zo ta tare gidan mijin. Kullum ranar girkinta sai a ce ta je ta ciro kuɓewa a gonar mijin ta yi miya. Da ta je gonar, sai ta yar da zanenta ta yi birgima a ƙasa ta zama barewa ta yi kiran ’yanuwanta, ta yi waƙa ta ce:

    ‎Cinkalkal, cinkalkal kalaya,

    Turmin ’yan kale ya yi fure, ceɗiya.

    Tudu na korar Tudu, Marina.

    Tudu na korar tudu da ƙaho.

    Ban da kwatsa-kwatsan.

    Ban da ƙanƙan.

    Sai ’yan uwanta su zo su taru su ciccinye kuɓewa. Sa’an nan in sun gama sai su tafi gida. ‎Ita kuma sai ta yi birgima ta komo mutum ta ɗauki zanenta ta ɗaura. Sai ta koma gida ta dinga cewa, ‘Ni da gangan aka tura ni. Ga shi nan ban samo kome ba.’

    ‎To, ran nan sai mijinta ya bi ta gonar. Sai ya gan ta tana birgima. Da ta gama birgimar, sai ya ga ta rikiɗe ta zama barewa. Sai ya ga ta yi kiran ‘yan’ uwanta bareyi da waƙa. Bareyi suka taru a gonar jingim. Duk suka cinye kuɓewa.

    ‎Suna cikin ci sai ya fasa su. Sai ya ga matarsa, ta gan shi. Ya komo gida. Sai ta ɗauko kuɓewar ta biyo shi. Ta tarad da shi a gida. Ya ce, ‘Wace ce?’ Ta ce, ‘Ni ce.’ Ya ce, ‘Ina za ki?’ Ta ce, ‘Ɗaki za ni.’ Ya ce, ‘A a, koma daji.’ Sai ta ce ta ƙi. Sai ya biyo ta a guje ya kora ta daji.

    ‎Daga nan ba ta sake dawowa  ba. Shi ke nan. Kurunkus.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin tatsuniyoyi da wasanni wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Gizo Da Namun Daji

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar ‎Gizo Da Namun Daji

    Tatsuniyar ‎Gizo Da Namun Daji

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Gizo ne dai yana son ya ci nama, amma ba shi da shi. Ya rasa yadda zai yi. Sai ya ce a ransa, ‘Bari dai in yi wata dabara. Sai ya sayo goro ya rarraba wa namun daji da tsuntsayen gida.

    ‎Sai ya fara kai wa kaza, ya ce, ‘Ga shi. Goron wasa ne wanda za a yi a cikin daji. Naki ne wannan. ‎Sai kaza ta ce, ‘To. Amma fa kada ka kai wa muzuru. Sai ya ce, ‘Haba, me zai sa in kai masa?’

    ‎Da gizo ya fita, sai ya shiga gidan muzuru, ya kai masa goro. Sai shi ma muzurun ya ce, ‘To, amma kada ka kai wa kare. ‎Sai gizo ya ce, ‘Haba me zai sa in kai masa? ‎Da dai gizo ya fita, sai ya shiga gidan kare ya ba shi nasa goron. Kare ya ce, ‘To, amma fa kada ka kai wa kura.’ Gizo ya ce, ‘Haba me zai sa in kai mata?’

    ‎Da ya fita, sai ya kai wa kura nata goron. Kura ta ce, ‘To, amma fa‎ kada ka kai wa Zaki.’ Ya ce, ‘Haba kura, me zai sa in kai wa Zaki? ‎Shi ke nan, sai ya kai wa Zaki nasa goron, ya ce, ‘Ranka ya daɗe. Wani ɗan wasa za a yi na kawo maka goro.’

    ‎Da Zaki ya karɓa, sai ya ce, ‘To Allah ya kai mu. ‎Shi ke nan. Da ya fita, sai ya shiga ya kai wa damisa. Damisa ta ce, ‘In ce ko dai ba ka kai wa Sarki Zaki ba? Sai Gizo ya ce, ‘Haba, haba. Wane ni da gayyatar Sarki? Sai damisa ta ce, ‘To, Allah ya kai mu.’

    ‎Da ya fito sai kuma ya shiga gidan giwa ya kai mata nata goron. Sai giwa ta ce, ‘To, in ce ko ba ka kai wa manyan dawa ba? ‎Ya ce, ‘Mhm. Yaya zan kai? Ko kai masa ne ma ai ke zan bai wa ki kai masa.’

    ‎Shi ke nan. Ana nan ana nan, sai ranar wasa ta zo. Gizo ya bayyana musu wurin da za su haɗu a yi wasan. Ya ce musu, ‘To, ku tafi zan same ku. Ni daga baya zan taho tare da makaɗa. Shi ke nan. Sai kaza ta fara tafiya. Ashe ba su sani ba, gizo ya riga su isa can. Sai kaza ta isa can. Gizo ya yi mata maraba. Ya ce, ‘To shiga wannan bukkar kafin su zo.’

    ‎Shi ke nan. Kaza ta shiga, ta zauna. Daga can sai ga muzuru ya taho. Sai Gizo ya gaya wa muzuru cikin raɗa, ‘Maraba. Shiga tana nan a ciki. Shi ke nan sai muzuru ya shiga ya tasar wa kaza zai cinye ta. Ya cinye ta.

    ‎Can kuma sai ga kare ya taho. Shi ma dai Gizo ya gaya masa kamar yadda ya gaya wa muzuru. Sai shi ma karen ya cinye muzuru. Daga nan kuma sai ga kura. Ita ma ya gaya mata kamar yadda ya‎ gaya wa kare da muzuru. Sai kura ta shiga ta cinye kare.

    ‎Kura kuma tana zaune a cikin rumfa. Sai ga Zaki ya taho. Shi ma Gizo ya gaya masa haka. Ya shiga ya cinye kura. ‎Daga nan sai ga giwa da damisa sun jero sun taho. Sai Gizo ya ce, ‘To. Ku shiga nan bukkar mana.’

    ‎Daga shigarsu, sai suka kaure da faɗa. Suka yi ta faɗa tun daga cikin rumfa har suka yiwo waje. Idonsu duk ya rufe, suna ta faɗa. Sai Gizo ya samo ganga, ya soma kiɗa yana waƙa:

    ‎Zaki bari, damisa bari.

    ‎Giwa bari.

    ‎Faɗanku na manya,

    ‎Wa yake shiga?

    ‎Sai wawa, sai mahaukaci.

    ‎Sai ko ni da ba ni da hankali.

    ‎Suna ta faɗa, can da giwa ta ga abin ba dama, sai ta fito ta yi‎ tafiyarta gida, ta bar zaki da damisa suna karawa. Sai Gizo ya ci gaba da yi musu waƙa. Ya yi ta yi, su kuma suna ta faɗa. Ashe Gizo da ma ya zo da yaji a ƙunshe. Sai ya ɗauko yajin nan ya barbada musu a idanunsu. Sai fa faɗa ya rincabe, idanunsu suka rufe ruf.

    ‎Daga can sai Gizo ya ɗauko wuƙa ya ce, ” ‘Yan banza. Ana so a ci nama an rasa yadda za a yi.” Sai ya kama yankan naman jikinsu yana tarawa, har ya kashe su duka. Sai ya jide naman ya kai gida aka soya masa, ya ci ya  ƙoshi, ya ajiye sauran, yana ci lokaci-lokaci.

    ‎Shi ke nan. Ƙurunƙus.

    ‎Wannan rubutu an ciro shi ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Danna nan don karanta Ga Tsoro Ga Ban Tsoro

    Edita@rumasau-kallamu

  • ‎Tatsuniyar Yarinya Da Dodanni

    ‎Tatsuniyar Yarinya Da Dodanni

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Wata yarinya ce dai mai tsananin kyau, duk garinsu babu mai kyanta, ta ce ba ta son kowa sai maras tabo. Sai dodanni suka ji labari. Sai suka yi wanka a gidan tururuwa. Sai suka zama samari kyawawa da su.

    ‎Da ta gan su, sai ta ce ta sami mazan aure. Sai duk ta dube jikinsu, sai ta ga jikin wannan da ɗan tabo ɗan mitsitsi, sai ta ce ba ta son sa. Da ta duba jikin ɗayan ta gan shi‎ sumul ba ko ɗigon tabo a jikinsa, sai ta ce shi ta ke so.

    ‎Shi kenan, sai aka shirya aka yi biki. Sai suka ce za su tafi da ita garinsu, su ba mazauna ba ne, Sai aka ce to za a ba ta ƙanwarta ta taya ta zaman ɗaki. Sai ta ce ita ba ta so, ta zauna ita kaɗai. Shi kenan, aka yi aka yi su tafi da ƙanwarta ta ƙi. Sai ƙanwar ta zama ƙuda ta maƙale mata.

    ‎Shi ke nan, da suka je gidan dodanni, sai dare ya yi suka shiga ɗaka suka rufe ƙofa. Sai ta ga ƙanwarta, sai ta rufe ta da faɗa, ta ce, ‘Ke wa ya kawo ki nan? ‎Ita kuwa ƙanwar sai ta yi shiru. ‎Shi ke nan sai yar ta ƙyale ta.

    ‎Ita yar kamar sokuwa ta ke. In dare ya yi, sai ta yi ta shirga barci. Ita kuwa ƙanwar sai ta zauna tangar har gari ya waye. Sai uwar mijinta ta zo da tsakar dare ta ce:

    ‎Sarma-sarma duf-duf.

    ‎Sai ƙanwar ta ce:

    ‎Wane ne nan ya ke mana Sarma-sarma duf-duf?

    ‎Sai uwar mijin ta ce:

    ‎Uwar miji ce ta ke mu ku Sarma-sarma duf-duf.

    Sai yarinya ta ce:

    Me ki ke so ki ke mu ku Sarma-sarma duf-duf?

    Sai ta ce:

    Wuta na ke so na ke muku Sarma-sarma duf-duf.

    Sai yarinya ta ce: Iya ga wuta nan.

    ‎Ki bar mana Sarma-sarma duf-duf.

    ‎Sai yarinya ta watso mata wutar. Tsohuwa ta je ta kashe wutar ta kuma dawo musu. Nan kuwa ashe ba wuta ta ke so ba. So ta ke yi ta cinye su idan ta tarar sun yi barci. Kullum haka, kullum haka. Duk sa’ad da yarinyar ta gaya wa yarta game da uwar mijin mai zuwa ɗiban wuta da daddare, sai yar ta ce ƙarya ta ke yi.

    ‎Ana nan a haka sak, ran nan yarinya ta ce da yarta, ‘To, yau dai ki zauna kada ki yi barci don ki ji yadda mu ke yi da tsohuwar da kunnenki. Shi ke nan, ya ta zauna. ‎Sai ita uwar mijin ta zo ta yi musu irin yadda ta ke yi kullum. ‎Shi ke nan, sai ya ta ji da kunnenta.

    ‎Shi kuma mijin nata yana wani ɗaki suna kwance tare da abokansa. Idan an yi abinci na aikin gona an kai musu, sai su yi haka su bunne. Sai su yi ta cin kwaɗi. Ita kuwa ƙanwar, wadda ta kai musu abincin, sai ta ce da su:

    ‎Mijin yata, ci kwaɗi.

    Mijin yata, ci kwaɗi.

    Mazan-wazata, ci kwaɗi.

    Sha da kwaɗi, ci kwaɗi.

    Sha da kwaɗi, ci kwaɗi.

    Su kuma idan sun ji wannan waƙar, sai su yi ta rawa suna cin kwaɗi. Shi ke nan. Da sun ga ƙanwar ta dawo daga gida, sai su zama mutane su ce, ‘Ga kwanukanki nan.

    Ki ce muna yi mata sannu da aiki. Shi ke nan. Da sun ga ƙanwar ta dawo daga gida, sai su zama mutane su ce, ‘Ga kwanukanki nan. Ki ce muna yi mata sannu da aiki. Shi ke nan, sai yarinya ta ɗebi kwanuka ta tafi da su gida. Kullum haka, kullum haka.

    ‎Sai rannan yar ta yi shawara da ƙanwarta don su gudu gida. Sai suka yi ta haƙa rami, tun daga nan gidan har ya zuwa hanyar ƙofar garinsu. Suna ta bin rami da ita da ƙanwarta har suka je gida.

    ‎Iyayenta suka ce da ita, ‘Lafiya?’ Sai ta ce wa iyayenta, ‘Ashe dodanni ne? Ni ca na ke mutane ne.’ Shi ke nan. ƘurunƘus kan ɗan ɓera. Ba don ƙarya ƙarya ce ba, wa zai zuba  ruwa a jallo, jallo ya fashe kuma ruwan bai zube ba?

    ‎Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Danna nan don karanta Labarin Kalala Da Kalalatu

    Edita@rumasau-kallamu