Category: Tatsuniyoyi

  • Tatsuniyar Kaza Da Muzuru

    Tatsuniyar Kaza Da Muzuru

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Kaza ce dai ta ce ba ta son kowa a cikin duk ‘yan uwanta zakaru masu nemanta. Ta dage ita sai muzuru kawai ta ke so da aure. Iyayenta ma suka ce ba za su ba ta shi ba. Ita kuma ta ce shi take so.

    ‎Da suka ga ta dage, sai suka ce, ‘To, mu dai babu ruwammu. Kada ki je ki jawo mana abin da zai hallaka mu baki ɗaya. Kaza kuwa ta ce ita dai shi ta ke so, ba za ta sake ba.

    ‎Sai aka kirawo ƙawayenta suka rarraba goron biki. ‎Shi ke nan, aka yi biki. ‎Sai ‘yammatan amarya suka je suna waka suna cewa:

    ‎Ke kaza kar ki jawo mana tserereninya da muzuru.’ Sai kaza ta ce: ‘Shi ba ya cin kaji, mhn. Shi ba zai ci kaji ba, mhn. In ji dai ni na kai kaina, mhn.’

    ‎Shi ke nan, sai suka ce da makaɗin ya sauya musu kiɗa. Shi kuwa makaɗin zakara ne, saboda a dangin amarya ya ke. Sannan ga kuma angwaye muzurai sun jeru, suna jin waƙa.

    ‎Shi ke nan, sai ‘yar ƙaramar kaza ta shiga fage ta ce:

    ‘Ni auta, autar kaza,

    In waiwaya haka,

    In muskuta haka,

    Sai na kan ji kiɗan da daɗi.’

    ‎Sai ta fita. Wata kuma ta shiga ta ce:

    ‘Ni wake-waken kaza,

    Kazar da ba a duka,

    Kazar da ba a zagi,

    In waiwaya haka,

    In muskuta haka,

    Sai na kan ji kiɗan da daɗi.’

    ‎Shi kuma makaɗin zakara, yana cewa:

    ‎’Daga baya-baya nake tsaya, In na ji kaya-kaya in naƙe.’

    ‎Sai kuma kaza ta uku ta shiga ta ce:

    ‘Ni ja-ja ja-jar kaza,

    Kazar da ba a duka,

    Kazar da ba a zagi,

    In waiwaya haka,

    In muskuta haka,

    Sai na kan ga idon muzuru!’

    ‎Daga nan fa sai angwaye muzurai suka yiwo kan ‘yan biki kaji radadada. Muzurai suka fara ciran su kai, su fafa, su fukafiki na kaji. Ita kuwa amarya sai cewa ta ke yi, ‘Kar ka cire mini fukafiki. Kar ka cire mini kai.’ Suka isa gida da ƙyar, suna cewa: Ga shi ta jawo mana tsiya. Wanda bai ji bari ba, zai ji hoho. An ce ta bari ta  ƙi.

    ‎Kurunkus kan ɗan kusu.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin Tatsuniyoyi Da Wasanni wanda Ibrahim Yaro Yahaya Ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kura Da Zomanya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kura Da Zomanya

    Tatsuniyar Kura Da Zomanya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can cikin wani ƙungurmin daji akwai wata Zomanya mai ciki, wadda gidanta yake kusa da na wata Kura, ita ma mai juna biyu. Suna zaman lafiya da junansu irin na maƙwabta. Wata rana sai Zomanyar nan ta je wurin Kura ta ce mata: “Kin ga ni da ke mun kusa haihuwa, ya kamata mu nemi wurin da za mu rinƙa  ɓoye ‘ya’yanmu.

    “Sai Kura tace: “E, gaskiya ne, to amma bari mu tona rami babba domin mu saka ‘ya’yanmu a ciki.” Da suka tona rami sai suka zauna tare, har lokacin haihuwarsu ya yi. Da suka haihu, sai suka tara ‘ya’yansu a rami ɗaya, kuma suka yi alƙawari cewa Kura za ta rinƙa samo musu abinci, ita kuma Zomanya za ta rinƙa renon ‘ya’yansu.

    Suka zauna, in Kura ta tafi neman abinci ta dawo, sai ta miƙa wa Zomanya ta ci, kuma ta raba wa ‘ya’yansu. Kullum haka. Amma ita kuwa Zomanya, in an kawo mata abinci sai ta ba ‘ya’yanta su ci, in sun ƙoshi sai ta cinye sauran, ta hana ‘ya’yan Kura. Kullum haka, kuma in Kura ta zo ta ce za ta duba lafiyar ‘ya’yanta sai Zomanya ta ce ai sun ci abinci sun ƙoshi, suna barci.

    Haka suka yi ta yi, har dai wata rana Kura ta ce sai ta ga ‘ya’yanta. Da ta leƙa ramin ta jawo ‘ya’yanta sai ta ga duk sun rame. Sai ta tambayi ‘ya’yanta abin da ya same su, suka rame haka. Sai ‘ya’yan suka ce ai ba a ba su abinci, in an kawo abinci sai Zomanya ta hana su, ta bai wa ‘ya’yanta, su kuwa sai ta sa su yi barcin dole kullum.

    Da jin haka sai ran Kura ya ɓaci, ta yi kuka, ta yi gumani da ƙaraji mai tsanani, ta ce tun da Zomanya ta ci amanarta, to ita da ‘ya’yanta za su cinye Zomanya da ‘ya’yanta gaba ɗaya. Ko da Zomanya ta ji abin da Kura ta faɗa, sai ta rasa abin da za ta yi, idanunta suka raina fata.

    Tsoro ya kama ta. Sai ta dubi Kura ta ce: “To shi ke nan, tunda kin ce ni da ‘ya’yana mun zama nama, to ki yi haƙuri mu fito daga rami tukunna.” Zomanya ta shiga rami ta gaya wa ‘ya’yanta idan ta fita Kura ta bi ta, to su fita da gudu su yi nasu wuri. Da Kura ta sake magana, sai Zomanya ta haɗa manyan kunnuwanta biyu, ta ɗan miƙo su waje ta ce da Kura: “Don Allah ki riƙe mini takalmana kafin in fito.

    “Jin haka sai ya sa ran Kura ya ɓaci, ita a tsummaninta yaya za a yi kamar Zomanya ta ce ta riƙe mata takalmanta, bayan ta zama nama a wurinta. Sai ta kama kunnuwan Zomanya da ƙarfi ta finciko su ta jefar, wai ita a nufinta takalma ne. Sai kunnuwa suka sulluɓe, Zomanya da ‘ya’yanta suka ranta a na kare.

    Kamar wasa, Kura ta kasa kama ko ɗaya daga cikinsu. Da ba domin Gizo ba da na shara muku ƙarya. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    •  Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka.
    • Ƙarshen maci amana jin kunya.
    • Kowa ya ci zomo, ya ci gudu

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Mace Mai Ciki

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Mace Mai Ciki

    Tatsuniyar Mace Mai Ciki

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana wata mata mai juna biyu ta je ɗibar ruwa a bakin rafi. Bayan ta cika tulunta da ruwa, sai ta kasa ɗauka saboda cikinta ya girma sai nishi take yi, abin tausayi. Kuma ga shi ita kaɗai ce ƙwal a wurin.

    Haka ta haƙura ta zauna. Can sai ga wani mutum ya taho, sai ta dube shi ta ce: “Malam don girman Allah ka ɗora ni mana.” Sai yace shi ba zai ɗora ta ba sai dai idan za ta yi masa wani alkawari. Mai ciki ta dube shi ta ce: “Na mene ne?” Shi ko ya kaɗa baki yace: “Idan kin haihu, in namiji ne to abokina ne, idan kuma mace ce, to matar ɗana ce.

    ” Da jin wannan sharaɗi sai ta yarda. Ya ɗauki tulu ya ɗora mata ta kama hanya ta tafi gida. Da ta je gida sai ta yi wa mijinta bayanin yadda suka yi da mutumin. Da yake mijinta mai sauƙin kai ne, sai ya ce: “To shi ke nan, Allah ya sauke ki lafiya.

    ”Bayan ’yan kwanaki sai mutumin ya zagayo gidan matar, suka gaisa. Ya nuna mata ɗansa suka yi sallama ya koma gida. Bayan wata ɗaya sai matar ta haifi ’ya mace, amma jikinta na jaki ne. Da mutumin ya ga haka sai ya yi halin dattaku ya ce: “To shi kenan tun da an yi alƙawari ai sai an cika.

    ”Sai ya kira ɗansa aka ɗaura musu aure da yarinyar ya kai ta gidansu. Yaro ya zauna da mace mai jikin jaki, ya ɗaure ta a gida. Amma duk sanda ya tafi gona idan ya dawo gida sai ya tarar an yi masa shara, an dafa masa abinci an kuma kai masa ruwan wanka bayan ɗaki.

    Kullum haka, sai abin ya fara ba shi tsoro tun da ba kowa a gidan. Rannan sai ya je ya sami babansa ya gaya masa, amma sai baban ya ƙi kula shi sai ya kore shi. To da ma yaron yana mutunci da wata tsohuwa maƙwabciyarsa dangarsu ɗaya. Sai wata rana ya zauna a gindin bishiya, yana tunanin abin mamakin da ke samunsa.

    Da tsohuwar ta gan shi a zaune haka, sai ta kira shi ta ce: “Ɗanyaro me ke damunka ne?” Shi ko sai ya kwashe labari ya bai wa wannan tsohuwa. To da ma ashe tsohuwa tana ganin duk abin da yarinya take yi idan ya tafi gona. Watau rikiɗa take yi ta koma kyakkyawar budurwa, ta shiga yi masa waƙa, ta yi shara, ta yi wanke-wanke, ta dafa abinci, ta ɗebo ruwa a rijiya ta kai masa banɗaki.

    Duk bayanta gama kafin ya dawo sai ta mayar da jikinta na jaka, ta ɗaure kanta a turke.
    Da tsohuwa ta gama bai wa yaron labarin abin da take gani sai ta shawarce shi da cewa gobe ya kwashi kayan aiki kamar zai tafi gona, idan ya kama hanya sai ya ratse a hanya, ya zagayo gidanta.

    Bayan sun gama shirya zancensu, sai ya koma gida yana mamaki, ya shiga ɗaki ya kwanta. Da gari ya waye sai ya saka kayan aiki ya ɗauki fartanyarsa ya kama hanyar gona. Bayan ya tafi ya yi nisa sai ya ratse cikin ciyawa, ya zagayo ta gidan tsohuwa, ya same ta a ɗaki.

    Daga nan sai suka ɓuya suka shiga leƙen yarinyar. Jim kaɗan sai suka ga ta rikiɗa ta koma kyakkyawar mace, ta fara waƙa ta kama shara da sauran ayyukan gida, ta shirya miya, ta dafa abinci, ta zuba nasa, ta kai masa ruwan wanka banɗaki. A daidai lokacin da ta fito daga bayan gida sai mijinta ya tsallaka danga ya dira a gabanta.

    Sai kawai ta razana za ta rikiɗa sai ya kama hannunta ya fara yi mata waƙa yana roƙon ta. Da ta ji waƙarsa sai ta fara kuka tana roƙon ya yafe mata. Shi kenan suka yi zamansu cikin daɗi suka ci gaba da more rayuwarsu cikin ƙauna da farin ciki. Dan kan ɓarya, ba domin Gizo ba da na sheƙa muku ƙarya. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Alkawari kaya ne, in an sauke sai a huta.
    • Tsintar dami a kala.
    • Rabon kwaɗo ba ya hawa sama.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Cilakowa Da Kodokodo

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Cilakowa Da Kodokodo

    Tatsuniyar Cilakowa Da Kodokodo

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wasu tsuntsaye biyu a wani baƙin daji da ke ƙasashen Gabas. Ɗaya sunanta Cilakowa, ɗayar kuma Kodokodo. Ita Cilakowa tana da dogon baki, ita kuma ’yar Sarkin tsuntsaye ce.

    To tana so ta yi aure, amma saboda dogon bakin nan nata, ba wanda ya fito domin ya aure ta. Ana nan, sai rannan ta yi tunanin cewa bari ta je wurin Kodokodo ta yi mata dabara, ta ce za ta biki ta ba ta aron bakinta, idan ta gama harkar bikin za ta dawo mata da shi.

    Sai ta yanke shawarar haka, ta je ta yi bayani sai Kodokodo ta ba ta. To ashe daga bikin nan aure za ta yi. Sai ta gama biki, ita ma ta yi aure. Ana nan, ana nan sai Kodokodo ta ji shiru, ko labarin Cilakowa babu. Ga shi kuma bakin Cilakowa da ta karɓa ta ba ta aron nata, ya yi mata tsawo, ta yadda ma ba ta iya magana ko cin abinci da shi.

    Sai ta fara ramewa saboda ƙishirwa da yunwa, abin ya dame ta. Da ta ga ba dama, watau ba za ta iya ci gaba da jurewa ba, sai wata rana ta yanke shawarar cewa gara ta je ko ina ne neman Cilakowa.

    Duk inda ta je sai a riƙa cewa ai sunan Cilakowa Sheba. Kodokodo dai ta mai da hankalinta wajen neman bakinta. Tana cikin tafiya sai ta tarar da wasu mutane suna daka. Da ta ƙarasa kusa da su, sai ta durƙusa ta gaishe su, da waƙa kamar haka: –

    “Masu dakan nan, masu dakan nan;
    Ba ku gane min Sheba ba?
    ’Yar gidan su Dalailu.
    ’Yar Sarkin tsuntsaye. Ta karɓi aron bakina. Daga biki sai aure. Wutsiyata ta shinge. Bakina na talaka talak.”

    Suka ce: “A a, ba mu gan ta ba, ki yi gaba.” Da ta yi gaba sai ta ga wasu mutanen, su ma ta sake yi musu irin wannan waƙar. Sai suka ce da ita ta je ta shiga wani gidan, sai
    ta shiga.

    Tana shiga sai suka yi arba da Sheba, ta dube ta tace: “Na biyo bakina, daga aro sai aure?” Kafin ma Cilakowa ta yi wata magana sai fut, ta cire bakinta, ta ba ta nata, ta tafi. Da mijin Cilakowa ya dawo sai ya ga Sheba da dogon baki.

    Ganinta haka ya ba shi mamaki, sai ya dube ta yace, “Sheba ɗauke karan nan.” A cikin murya tattausa ta mayar masa da jawabi cewa: “Ba kara ba ne, bakina ne.” Sai ya dube ta ya ce: “To in haka ne ba zan iya zama da ke ba, bakinki ya yi tsawo da yawa.” Shi ke nan ya kore ta, ta koma gida. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • In ba ki da gashin wance kada ki ce za ki yi kitson wance.
    • Kayan aro ba ya rufe ƙwauri.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Daskin Dariɗi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Daskin Dariɗi

    Tatsuniyar Daskin Dariɗi

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    Da gero da dawa da maiwa da duk dai kayan abinci haka, su shinkafa, acca, iburu, alkama da burtuntuna, sai suka shirya za su tafi gun wani saurayi wanda ya ce duk wata wadda ta faɗi sunansa, ita zai aura.

    ‎Shi ke nan. Ko wacce ta ci kwalliya. Ita kuwa burtuntuna ba ta yi kwalliya ba don ba ta da kayan ado. Suka kama hanya suna tafiya. A kan hanyar da su ke wucewa sai suka ga wata ‘yar tsohuwa a tsugunne da ruwan wankanta.

    ‎Sai tsohuwa ta ce da dawa, ‘Don Allah yarinya, zo ki cuɗa ni mana? ‎Sai dawa ta ce, ‘A, don Allah ku ji ‎tsohuwa? In yi kwalliyar tawa haka sannan ki ce in zo in cuɗa ki? Sai ta wuce ta ki cuɗa ta.

    ‎Sai kuma shinkafa ta zo, tsohuwa ta ce da ita, ‘Don Allah yarinya zo ki cuɗa ni mana? Sai shinkafa ta ce, ‘Duk wannan kwalliyar tawa in tsaya in cuɗa ki?’ Sai ta ki cuɗa tsohuwa, ta shige abinta.

    ‎Sai su maiwa, su gero, su alkama suka zo da dai dai, kowacce tsohuwa ta tambaya ta cuɗa ta sai ta ki, ta yi wucewarta. Daga nan sai ga burtuntuna ta zo. Sai tsohuwa ta ce da ita, ‘Yarinya don Allah zo ki cuɗa ni mana?’

    ‎Sai burtuntuna ta ce da ita, ‘To.’ Ta shiga cuɗa ta. Tana cikin cuɗa ta, sai bayan ‘yar tsohuwa ya burme Yarinya ta ce, ‘Yau na shiga uku, na lalace. Sai ‘yar tsohuwa ta ce, ‘Mene ne?’ Burtuntuna ta ce, ‘Bayanki ne ya ɓurme.’

    ‎Sai ‘yar tsohuwa ta ce, ‘Me kika gani a ciki?’ Ta ce, ‘Na ga kwatashi guda biyu, babba da ƙarami. ‎Ta ce, ‘To, ɗauko ƙaramin.’ Burtuntuna ta ɗauko ƙaramin kwatashi. ‎Sai tsohuwa ta ce, ‘To, ajiye nan.’ Burtuntuna ta ajiye.

    ‎Can sai tsohuwa ta haɗiye burtuntuna. Ta mai da ita fara, ta fito da ita waje, ta duba ta ta ce, ‘Kai, ba haka na ke son ki ba. Sai ta sake haɗiye ta, ta mai da ita ja zur kamar tsada, ta fito da ita waje ta duba ta ta ce, ‘Yauwa, haka na ke son ki.’

    ‎Sai ta buɗe ɗan kwatashin nan, ta ba burtuntuna kayan ado irin na mata kamar su zannuwa, su fatala, su yari, su awarwaro. Burtuntuna ta ci ado da su. Da ta gama adon, sai tsohuwar ta ce, ‘To, ga shi na shirya ki. Kin san sunan yaron da za ku wurin sa?’ Ta ce, ‘A a, ban sani ba.’

    ‎Sai tsohuwa ta ce, ‘Sunansa Daskin-da-riɗi.’ Sai ta ce, ‘To. ‎Sai ta yi godiya, suka yi sallama. Shi ke nan. Sai burtuntuna ta tafi ta sami sauran ‘yan’uwanta a hanya. Da suka gan ta sai suka dinga cewa, ‘Kun ga waccan shegiyar.

    Wa ya ba ta aron kaya ta ɗaura?’ Sai kuma su ce, ‘Wa ya sani ne? Mu yi maza mu je kada ta riga mu. Ko da ya ke ma ko ta je me zai yi da ita? ‎Shi ke nan. Da suka je, sai suka jajjeru. Dawa ta fara zuwa kofar gidan saurayin. Ta ce:

    ‘Assalam alam ɗan yaro.

    Assalam alam.’

    ‎Sai ya ce:

    Wane ne nan ya ke mana,

    Assalam alam?

    Sai ta ce:

    ‎Dawarku ce ta ke maka Assalam alam.

    Mai tuwo da daɗi, ni dawa Mai tuwo da daɗi

    ‎Sai ya ce:

    Na ji naki suna yarinya, Ba ni nawa suna.

    ‎Sai ta ce:

    Ban san ka ba, ɗan yaro. Ban san ka ba.

    ‎Sai ya ce:

    Da ba ki san ni ba, yarinya, Koma da baya ki sha kuka.

    ‎Dawa sai ta koma da baya ta yi ta kuka saboda ba ta san sunan saurayin ba, kuma babu damar ta aure shi ke nan.

    ‎Sai kuma ga su maiwa, da gero, da iburu, duk dai suka zozzo. Kowacce ya ce ta faɗi sunansa, sai ta ce ba ta san shi ba. Suka yi ta kuka. Shi kuma ya ce sai wadda ta san sunansa zai aura.”

    ‎Shi ke nan, nan sai ga burtuntuna ta zo: Sai suka ce da ita; ‘Ke don Allah, mu ma ba mu san sunansa ba, balle ke! ‎Sai ta rabu da su. Sannan sai ta je kofar gidan saurayin ta ce:

    Assalam alam, dan yaro.

    Assalam alam.

    ‎Sai ya ce:

    Wace ce nan ta ke mini Assalam alam?

    ‎Sai ta ce:

    Burtuntunarku ce ta ke maka Assalam alam.

    Burtuntuna, ai ni ce, Mai ɓata kaya.

    ‎Sai ya ce:

    Na ji naki suna, yarinya. Ba ni nawa suna.

    ‎Sai ta ce:

    Daskin-da-riɗi dan yaro Daskin-da-riɗi.”

    ‎Sai ya ce:

    “Buɗe ki shigo, yarinya, Buɗe ki shigo.”

    ‎Shi ke nan sai ta buɗe ta shiga. Sai kuma sauran su dawa, su gero, su iburu su ke cewa, ‘Ni zan yi miki wanka.’

    ‘Ni zan yi miki wanke-wanke.’

    ‘Ni zan yi miki alwala.’

    ‘Ni zan yi miki shara.’

    Da sauran abubuwa dai na barance. Sai  burtuntuna ta yarda suka zama barorinta. Shi ke nan. Ƙurunƙus.

    Wannan tatsuniyar an ciro ta ne daga littafin Tatsuniyoyi da Wasanni wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    ‎Danna nan don karanta Tatsuniyar Budurwa Marar Tabo

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniya Mai Taken Marainiya

    Tatsuniya Mai Taken Marainiya

    TASKAR TATSUNIYOYI”. Babi Na Daya: Marainiya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata yarinya marainiya, watau wadda take ba uwa ba uba; kuma ita kaɗai ce a wurin mahaifiyarta, lokacin da mahaifanta suka rasu suka bar ta. Ta sha wulaƙanci a wurin kishiyar uwarta, wadda take da ‘ya’ya maza da mata, waɗanda duka suka taru a kanta suka rika yi mata wulaƙanci.

    A cikin wannan yanayin kullum da sassafe takan je gindin wata bishiyar kurna ta zauna, ta yi ta kuka. Wannan kurna tana yin ‘ya’ya masu yawa, ga kuma zaƙi zaƙwai. Abincinta ke nan daga safe har yamma, kuma idan za ta koma gida sai ta ɗebo waɗanda za ta ci da dare.

    To akwai wani dan sarki kyakkyawa, mai suna Aminu, wanda ‘yar kishiyar uwarta take so, to amma shi kuma ba ya son ta. Shi ma kuma yakan je shan iska, ya hau kan wannan bishiyar kurna da marainiyar take zama a gindinta, ta sha ‘ya’yanta, yana kallon kowa, amma babu wanda zai gan shi don ganyen bishiyar ya ɓoye shi.

    Shi ke nan, wata rana marainiya tana zaune sai ɗan sarki ya sauko daga bishiya sai ya ce: “Sannunki ‘yan mata.” Sai ta ce: “Yauwa samari.” Aminu ya ce: “Me ke damun ki ne? Kullum sai in zo in gan ki a gindin wannan bishiya, har ma domin tunanin da kike yi ba ki sanin zuwana, kuma ga shi kikan riga ni zuwa don ni sai da la’asar nake zuwa, har in hau bishiya ba ki gan ni ba.”

    “To yaya kake zama a kan bishiyar kurna mai ƙaya?” Ta tambaye shi. Sai ya ce: “Ni na san dabarar da nake yi.” Haka dai suka ci gaba da hirarsu har ya kawo ga maganar aure, sai ta ce: “Ni dai marainiya ce, ba ni da uwa, ba ni da uba.” Sai ɗan sarki Aminu ya ce: “Yau na zama uwa da uba a wurinki.” Suna nan yana kiran ta, har ya fara zuwa gidansu marainiya.

    Da ‘yar kishiyar ta gane dan sarki ne yake zuwa wurinta, sai ta ce ta san makircin da za ta yi. Sai ta sayo allurai da yawa ta je ta sossoka a inda Aminu yake zama idan ya zo wurin marainiya. Da zuwansa sai ya zauna a kan alluran nan, kuma gaba ɗaya alluran suka shiga jikinsa.

    Nan da nan ya fara jin zazzaɓi, ya tashi ya tafi gida. Ciwonɗan sarki dai ya gagara warkewa, babu irin maganin da ba a yi ba. Wata rana marainiya ta tafi ɗiban ruwa a rafi, sai ta ji aljanu suna maganar ɗan sarki ba shi da lafiya, amma da an samo kashin tsutsotsi masu cin mutane a bayan wani gari mai nisa, aka jiƙa masa ya sha to zai warke.

    Da marainiya ta ji sai ta yi maza ta ɗauki goranta, ta je gida, ta aske kanta ta shafe jikinta da baƙin tukunya, ta sa kayan maza, ta ɗauki kwano, kamar almajiri zai je bara. Ta kama hanyar wancan gari mai nisa, inda za ta samo kashin tsutsa mai cin mutum, har sai da ta yi tafiyar shekara biyu kafin ta isa wurin tsutsotsin.

    Sai ta je wurinsu a hankali, ta kwanta don in sun ji motsin tafiyarta za su cinye ta. A hankali ta yi ta lulubawa dai -dai. Bayan ta sami abin da ta je nema, sai ta kama hanyar garinsu, ta isa lafiya. Bayan ta ɗan huta, sai ta kama hanyar gidan Sarki, ta tarar
    mutane maƙil sun cika fada suna jiran mutuwar Aminu.

    Da zuwa fada sai ta fara bara, mutane sun ɗauka namiji ne, suka ce: “Kai kana ganin ɗan sarki babu lafiya amma sai ka zo ka yi mana bara don ba ka da kunya?” Sai ta ce: “Ku bar ni in duba shi ko zai warke. Akwai wani magani da nake tafe da shi.” Sai suka daka wa ɗan almajiri tsawa, suka ce: “Duk duniyar nan babu wanda zai warkar da shi sai kai?”

    Sai ta ce: “Abar ni mana in ɗan gwada.” Da ƙyar aka bar shi ya shiga. Da shiga sai ta ciro wannan kashin tsutsa, ta jiƙa, ta ba ɗan sarki, ya sha. Cikin ikon Allah nan take sai ya fara amai, duk ya amayar da ciwon da ke damunsa, ya warke sarai. Kowa yana mamakin ɗan almajiri. A cikin farin ciki Sarki ya ce: “Zan ba ka gida da dawakai da dukiya mai yawa.” Shi ma Sarki bai san da mace yake magana ba.

    Sai ta ce: “A a ba na son wannan.” Sai Sarki ya ce: “To me kake so?” Ba tare da ɓata lokaci ba, marainiyar da ake zato namiji ce tace: “Ni dai babu abin da nake so kamar zoben hannunsa.”Ɗan sarki Aminu bai taɓa zaton zai rabu da wannan zobe ba, amma sai ya cire ya ba ta.

    Ta karɓa ta tafi. Bayan kwana biyu sai ya je gidan su marainiya a cikin fushi, yace da ita: “A duk garin nan babu wanda bai san da rashin lafiyata ba, amma ke ba ki taɓa zuwa gani na ba.” A cikin tattausar murya ta kalle shi ta ce: “Zauna ka ji labari.” Ya zauna ta fara gaya masa yadda ta yi.

    Da ta gama sai ya ce: “Ƙarya ne, idan maganarki gaskiya ce, to me aka bai wa ɗan almajirin?” Ya ce: “Zobe.” Sai ta ce: “To idan ke ce, nuna min zoben. Ya duba zobe, ya tabbatar zobensa ne. Daga nan ya fara mamaki. Ya ɗauke ta suka je gaban babansa, suka gaya masa labarin kome.

    Ya sa aka ɗaura musu aure, aka yi gagaruimin biki, kuma aka basu kyautar gari guda da dukiya mai tarin yawa, suka ci gaba da cin duniyarsu da tsinke. Kurunkus.

    > Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Rabon kwaɗo ba ya hawa sama
    • Mai nema yana tare da samu
    • Mai rabon ganin baɗi ko ana ha-maza ha-mata sai ya gani.
    • Hassada ga mai rabo taki ce.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar ‎Gizo Da Giwa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar ‎Gizo Da Giwa

    Tatsuniyar ‎Gizo Da Giwa

    ‎‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    Wani mutum ne dai ya ba wani malami kuɗi don a yi masa asiri. Sai malamin ya ce sai an samo hauren giwa domin ya haɗa maganin da shi. Sai mutumin ya je cikin jama’a ya ce, ‘Wa zai iya samo min hauren giwa in ba shi kuɗi? ’Aka rasa wanda zai iya. Sai Gizo ya ce shi zai iya.

    Sai mutumin ya ce, ‘To shi ke nan sai ka samo ka kawo.’ Shi ke nan, sai Gizo ya je gida ya daka nakiya mai zaƙin gaske. Sai ya je gidan giwa da ɗan ƙunshin nakiyar a hannunsa, ya ce, ‘Gafaya dai.’ Sai giwa ta ce, ‘Maraba da Gizo.’

    ‎Ya ce, ‘Yauwa. Wata nakiya ce na kawo miki da na samo a pa.’ Shi ke nan sai giwa ta ce, ‘To’. Ta gutsiri nakiya ta kai bakinta. Da ta ji zaƙin nakiyar, sai ta ce, ‘Don Allah Gizo, ni ma ka raka ni in je in samo?’

    ‎Sai ya ce, ‘Haba yaya! Me zai hana? Ki zo gobe in kai ki.’ Shi ke nan, sai ta zo washegari suka je wajen kan pa. Sai ya ce da ita, ‘Idan kika doka bakinki sau ɗaya, kika doka sau biyu, a na ukun sai ki ga nakiya rubus a bakinki.’ Shi ke nan, sai giwa ta doka bakinta sau ɗaya fas a kan pa. Ta kuma dokawa.

    Da ta doka na ukun sai haƙorinta ya balle ya faɗo ƙasa. Sai jini shar. Sai Gizo ya ce, ‘Assha, assha. Yaya aka yi haka kuma?’ Ya yi maza ya ɗauki haƙorin giwar ya sa a aljihunsa. Ita ba ta gani ba. Tana ta kanta.

    ‎Shi ke nan sai gizo ya bar giwa a nan. Ya yi sauri ya kai wa mutumin nan haƙorin. Mutumin ya ba shi ladansa. Sai gizo ya je daji ya tattara namun daji suka je gidan da giwa ta ke a kwance. Suka tarar kanta ya kumbura, suntum.

    Sai gizo ya gaya wa namun dajin, ‘In na ce, “Babbanmu da giɓi,” ku ce, “Ɓurum ɓaɓurka.”’ Sai ya fara waƙar: Babbanmu da giɓi. Sai suka amsa: Ɓurum ɓaɓurka. Shi ke nan sai suka gama, suka koma. Gizo ya bar giwa a wahala. Shi kuwa ya karɓe kuɗinsa.

    Shi ke nan. Kurunk us.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Budurwa Marar Tabo

    Tatsuniyar Budurwa Marar Tabo

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata yarinya kyakkyawa, wadda ko tabo ɗaya babu a jikinta. Shi ke nan, sai ta ce ita fa ba za ta auri wanda yake da tabo ko da ɗaya ne tak a jikinsa ba. Manema wannan ya zo, wancan ya zo, amma duk suna da tabo.

    Ana nan, sai ga wani saurayi wai shi Ɗandisheri wanda ba shi da tabo a jikinsa, in ban da wani ƙarami a kan ɗan yatsansa, shi ma ya je saran itace ne ya yi sartse. Da ya je, sai ta ce ba ta son sa. Ya haƙura.

    Rannan sai wani maciji ya ji labarin halin wannan budurwa, ya gayawa abokansa, suka rikiɗa suka zama mutane samari kyawawa, waɗanda ba ɗaya daga cikinsu wanda yake da tabo ko ɗaya a jikinsa. Sai suka je wurinta, ta bincike kowannensu sarai, ta ga babu tabo a jikinsa.

    Nan take ta ce ta yarda ɗayansu ya aure ta. Aka taru aka ɗaura aure da ɗayansu. Shi ke nan ta tattara kayan ta suka tafi da amaryarsu. Da suka je jeji sai suka ce: “Yawwa mun iso gida.” Ita ko tace: “Ina gidan a nan?” Sai suka ce da ita: “Ai nan ne gidan. Amarya ta yi zuru-zuru, babu yadda za ta yi domin ta riga ta auri ɗayansu.

    Kuma ga shi sun kai ta dokar daji, inda ba za ta iya komawa gari ba. Daga nan suka saka ta a kogon bishiya, suka rikiɗe macizai suna lasar jikinta har ta zama fara fat, babu kyan gani, kuma abin ƙyama. Ana nan kwanci-tashi har ta sami ciki. Bayan wani lokaci mai tsawo, sai wata rana Ɗandisheri suka yi ƙarancin ciyawar akuyarsu, sai ya tafi can cikin ƙungurmin jeji yana yankan ciyawa.

    Sai matar macizai ta hango shi, ta fara rera masa waƙa tana cewa:

    “Ɗandisheri – Ɗandisherina,

    Ɗandisheri ƙanin Babati.

    Idan ka je gida ka gai da iyata,

    Idan ka je gida ka gai da Babati.

    Ni mai zaɓar maza babu tabo,

    Ga ni yau a kogon kukati,

    Maciji na lasa ta mulai,

    Kunama na harbi na mulai.

    “Sai Ɗandisheri ya ɗau waƙa, ya amsa mata yana cewa:

    Ina ruwan Ɗandisheri,

    Daga fari ke aka bai wa ni,

    Daga gani sai kika raina ni,

    Domin tabon ɗan yatsana.

    Da ya je gida sai ya gaya wa iyayenta halin da take ciki. Da suka ji labari, sai suka yi shiri domin su je su gani. Da suka je sai suka same ta a cikin kogo. Suka rasa yadda za su fito da ita. Dole aka sare bishiyar, aka fitar da ita, iyayen suka tafi da ita gida.

    Daga baya ta haifi ɗa namiji, rabin jikinsa ɗan mutum, rabi ɗan maciji. Da mazanta macizai suka ji ta haifu sai suka ƙara zama mutane, suka zo karɓar ɗansu. Da suka isa gidan, sai danginta suka tona makeken rami, aka shimfiɗa musu tabarma a kai, aka kuma hura wuta a ƙarƙashi, aka yi wa ɗansu wanka aka yi masa kwalliya aka kira su, suka zauna suka karɓi ɗansu.

    Suna cikin hira sai su ji ‘nyas-nyas,’ sai suka ce: “Kai akwai abin cizo a gidanku?” Masu gida suka ce: “E wallahi. Jim kaɗan sai tabarma da yayin suka kama wuta, su da shimfiɗar suka faɗa cikin wutar. Yayin da suke ƙonewa sai suka wurgo yaron sama, aka cafe shi, aka ƙara wurga musu, haka dai suka yi ta yi har suka ƙone rumus da su da ɗansu.

    Da ba domin Gizo ba da na yi muku ƙarya. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Mai ruwan ido gama kasuwa da yawo.
    • Jiki magayi.
    • Ƙarya fure take ba ta ‘ya’ya.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Jarumin Sarki

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Jarumin Sarki

    Tatsuniyar Jarumin Sarki

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani jarumin sarki wanda a fagen yaƙi ba ya ja da baya. Duk inda ya sa gaba sai ya sami nasara. Yana da mata uku: amaryarsa kitse ne, sauran kuma mutane ne. To Sarkin nan ya fi son Takitsen. Duk lokacin da zai je yaƙi sai da ita yake tafiya.

    Ana nan, sai wata rana wani yaƙi mai haɗari da zafi ya taso. Sai ya yanke shawarar cewa wannan yaƙin ba irin wanda zai je da mata ba ne. Amma kuma yana tsoron barin amaryarsa a gida. Da sauran matansa biyu suka ji haka, sai suka ce ya bar ta a gida, babu komai za su kula da ita kamar yana nan.

    Sai ya amince da alƙawarin da suka yi, ya hau shi da barade suka dunguma zuwa filin daga, ya bar amaryarsa a gida. Bayan tafiyar Sarki sai matan nan suka sa amarya girki. Tana nufar murhu sai ta narke saboda zafin wuta. Ganin haka fa sai suka fara kuka, suna cewa: “Takitse ta narke ta zama ruwa.

    “To daman akwai wani tsuntsu a gidan Sarki. Da ya ji abinda matan Sarki suke faɗa a cikin kuka, sai ya tashi ya nufi wajen yaƙin, yana cewa;

    Sarki. Sarki. Sarki ka mai da yaƙi baya,

    domin Takitse ta narke ta zama ruwa.

    Haka ya yi ta yi, har Sarki ya kasa kunnensa, ya ji ana cewa ya bar yaƙi ya koma gida, domin matansa suna can a gida suna yin kuka. Fadawa da baraden Sarki ma suka tsaya, suka ji abin da tsuntsu ke cewa. Sai ya tambaye su abin da suka ji daga bakin tsuntsu, sai suka ce, ai Takitse amaryarsa ce ta narke.

    Nanda nan Sarki ya karya linzami, aka koma garinsa. Da ya isa fadar, sai ya shiga cikin turakarsa, ya sa Jakadiya ta kira matan, ya dube su ya ce: “Wace ce ta sa Takitse girki?” Sai matar Sarki tatsakiyarta yi farat ta ce: “Uwar gida ce. A fusace, Sarki ya umarci dogarawa su sare mata kai. Nantakesuka fille mata kai. Ba a wasa da umarnin Sarki. Kurunkus.

    Abubuwvan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Karya al kawari cin amana ne.
    • Soyayya amanar zuciya

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Ɗankaɗafi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Ɗankaɗafi

    Tatsuniyar Ɗankaɗafi

    Ga ta nan ga ta nan ku.

    Wata mata ce dai ba ta taɓa haihuwa ba, tun da take. Sai ta ce, ‘Allah, Allah, ba ka ba ni ɗa ba, ko da Dankadafi ne? Allah sai ya karɓi roƙonta, sai ta haifi ɗanta namiji. Shi ke nan, yaro yana nan yana girma. Sai ran nan ta goya shi. Da ta gaji da goyo, sai ta ce da shi, ‘To, sauko ka kwanta Ɗan inna.’

    ‎Sai ya ce, ‘Mhm, a baya.’ Ta kuma cewa, ‘Sauko a wanke maka ido.’ Ya ce, ‘Mhm, mn, a baya.’ Kome dai ta ce, sai ya ce, ‘Mhm, Mn, a baya.’ Sai ran nan ta ce, ‘Kai ni dai na gaji.’

    ‎Gun malami za ni ko yana da abin da zai yi mini in rabu da ɗan nan na gaji. Sai ta je wajen malami. Malami ya ce, ‘Duk abin da aka gaya miki kya iya?’ Sai ta ce, ‘I, zan iya.’

    ‎Sai ya ce, ‘To sayo sa guda ki kawo mini.’ Sai ta sayo sa ta kai wa malami. Sai ya ce, ‘To, biyu za a raba, ki ɗauki rabi, in ɗauki rabi.’ Ta ce, ‘To.’ Aka raba naman sa kashi biyu, malami ya ɗauki rabi, ta ɗauki rabi.

    ‎Sai ya ce, ‘Ki soya wannan ki tafi da shi daji ki haɗa da majanyi da zane. In kin sauko yaron yana cin naman sai ki gudo ki baro shi can.’ Sai ta ce, ‘To.’ Ta je gida ta soya nama. Ta tafi daji da shi. Ta ce, ‘Dan Inna, Dan Inna, sauko ka ci nama.’

    ‎Sai ya ce, ‘Mn, a baya.’ Sai ta ce, ‘Ga naman naka nan sauko ka ci.’ Sai ya sauko. Da ya sauko yana cin naman, sai uwar ta waiga, ta waiga ba ta ga kowa ba, sai ta gudu ta bar shi da majanyi da zane. Fatar bayanta har ta kwaye saboda goyo.

    ‎Shi ke nan sai ga kura, ita da ’yan uwanta suna wasa. Sai ta ce, ‘Dan kanena, dan kanena, sam min dan naman in ci in goya ka.’ Shi ke nan, ya ba ta. Sai ta ɗauke shi ta goya shi suna wasa. Sai ta ce, ‘Sauko in huta.’ Sai ya ce, ‘Mn, a baya.’ Kome dai ta ce, sai ya ce, ‘Mn, a baya.’

    ‎Da ta yi ta yi ta cire shi daga bayanta ya ƙi, sai ta kira ’yan uwanta su cire mata shi. Da suka zo garin cire shi sai fatar bayan kura ta ciro, ta ce, ‘Na gamu da jaraba.’ Sai suka gudu suka bar shi nan.

    ‎Can sai ga dodo ya zo ya ɗauke shi ya ɗora a bayan dokinsa, shi kuma yana gaba yana cewa:

    Za ni za ni za ni,

    Za ni za ni,

    Za ni da namana,

    Za ni da namana,

    Za ni da kai sharɓa,

    ‎Dankaɗafi za ni da namana. Suna cikin tafiya a daji, sai Gizo ya ga dodo da yaro, sai ya sauke yaron, ya ajiye a ƙasa. Shi kuma ya hau kan dokin dodo. Dodo bai sani ba yana ta waƙa.

    ‎Shi ke nan sai ana ta tafiya da Gizo, sai kurciya ta ga Gizon a kan dokin dodo sun kusa da kogi, sai ta ce da Gizo, ‘Ku ne a yi muku rana, ku yi wa mutum dare.’ Gizo ya ce, ‘A’a, ba zan yi miki ba.’ Shi ke nan, sai kurciya ta ɗauke Gizo a fiffikenta.

    ‎Da dodo ya je bakin kogi, sai ya waiga don ya ɗauko yaro ya cinye ya sha ruwa, sai ya ga ba kome. Baƙin ciki sai ya sa shi ya faɗa cikin ruwan nan, ya zama gawayi. Shi kuwa Dankaɗafi kura ta cinye shi a can dajin da aka ajiye shi.

    ‎ Shi ke nan.

    Kurunkus.

    ‎Wannan rubutu an ciro shi ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Gizo Da Ɓaure

    Edita@rumasau-kallamu