Breast Cancer

0
156

Matan da kan shayar nada ƙarancin yiwuwar haɗuwa da cutar sankarar nono wato ‘breast cancer’ da ƙarancin haɗuwa da Kansar kwanson ƙwayayen halitta wato ‘ovarian cancer’ ƙarancin haɗuwa da ciwon zuciya,cutar shanyewar ɓarin jiki,haɗuwa da ciwon sugar tare da samun kariya daga cutar damuwa dakan shafi wasu matan bayan haihuwa.

Gwargwadon tsayin lokacin da kika ɗauka kina shayarwa gwargwadon kariyar da za ki samu daga waɗancan cuttukan, wacce ta shayar da yaro iya wata 12 kacal ba za ta sami kariya kamar na wacce ta shayar tsawon watanni 18, shekara 2 ko 3 ba.

Haka gwargwadon tsayin lokacin da kika ɗauka kina shayarwa gwargwadon lafiyar yaro ko yarinyar ki, duk me son lafiyayyar zuri’a toh ya shayar na ɗan lokaci me tsawo. 

An yi abin ne don a shayar ba domin ai ado kurum ba.

Domin karanta amsar wannan tambayar Wani Lokacin Ina G.O.P.D Danna nan

labarin da ya wuceWani Lokacin Ina G.O.P.D
Labarin na GabaHIV/AIDS