Asalin Samuwar Goni

0
44

Asalin kalmar Gwani/Goni kalmar Barbarci ce “Luhranni Gonni” ma’ana wanda ba ya kuskure in yana karanta Alƙur’ani.

Kalmar Gwani dai-dai ta ke da Al’mahir da kalmar Al-Mukri, ma’ana ƙwararren makarancin Alƙur’ani. Kamar yadda mai irin wannan matsayi ake kiransa Fakih a Masar ko kuma Karmako a Senegal.

Yaɗuwar amfani da matsayin Gwani tsakanin makaranta ya samo asali ne tsakanin ƙarni na goma sha zuwa ƙarni na goma sha tara a Maiduguri bisa sharaɗin makaranci ya sanya allo a gaban malaman Marte ko Gawala ko Konduga. To a nan ne za su ga can-cantar a naɗa makaranci a matsayin Gwani.

A baya-bayan nan makaranci ba ya zama Gwani har sai ya sa allo gaban Goni Dala a Monguno ko kuma marigayi Goni Ƙashim cikin Maiduguri.

Ga misalin ɗaya daga sarƙa ko silsilar naɗa Gwani tun kimanin sama da shekara ɗari huɗu da goma sha shida a Barno, wadda ta ke tuƙewa kan Goni Musa Dongol, farkon wanda aka fara kira Goni a tsohon birnin Ngazargamu. Wannan silsila ita ce “Daga Imam Mahir Sheikh Goni Isa ɗan Sayyid Adam wanda aka fi sani da Walda Am jileji daga Mahir Alwali Salih Goni Hamid Kidik daga Goni Bukar Konduga daga Mahaifinsa Goni Mustafa Yabe daga 120 Musa Afgalbiyama daga mahaifinsa Goni Nukabi Bardi daga mahaifinsa Goni Kadai daga Goni Mele daga Goni lbrahim Al’aysar daga Mahaifinsa Goni Umar Jundi daga Mahaifinsa Goni Musa Dongol”

Tsokaci:

Akwai saɓani a wasu lokutan wurin wasu malamai game da matsayin Gangaran. Shin wane ne gaba tsakaninsa da Gwani? Wannan ya biyo bayan wani shahararren makarin zance “gangaran ka fi gwani”. Ala ayyi halin Gwani shi ne mafi karɓuwar ajin ƙoli a azuzuwan makaranta, kamar yadda ya gabata. Amma fa a yanzu ba a ɗabbaƙa sharuɗan da a da sai makaranci ya cika su sannan ya samu matsayin Gwani.

Shi kuwa Gangaran har yau sai wanda karatunsa ya bushe raƙayau sannan za a kira shi da wannan laƙabi. Ma’ana dai a yanzu in har ka ga wanda makaranta ke kira Gangaran to kusan za a iya cewa ya fi gwanin da aka naɗa ba tare da ya cika sharuɗan ba.

Domin karanta cikakken bayani akan Ɗabi’un Makaranta da Halayensu Cikin Zamantakewar Tsangaya danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Kasance A Cikin Zikiri Kowane Lokaci danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceƘalubale Ga Makarantun Tsangaya
Labarin na GabaHutun Alhamis Da Juma’a A Tsangayu