Shi dai Malam Bahaushe a bisa tarihin da ya shuɗe, mutum ne baƙi sosai, mara tsawo, mai shafaffen hanci da faffaɗan baki. Amma dai wannan siffantawar ta Bahaushe a kan iya cewa tana daf da a kira ta tarihi, bisa ga yadda aka samun auratayya sosai tsakanin ƙabilar Hausawa da sauran ƙabilu daban-daban.
Al’ummar Hausawa mutane ne da suka shahara a kan riko ga ɗabi’u da al’adunsu na gargajiya. Sai dai canji da suka samu na addini wanda a fari suka wanzu cikin addinin gargajiya da aka fi sani da Maguzanci, sannan daga bisani suka rungumi addininin Islama. Ga Malam Bahaushe, babu wani abu da ya ɗara addininsa martaba da kima.
Hausawa sun bambanta da sauran ƙabilun Najeriya, ta hanyar tsananin ruƙonsu ga al’adun tufafin sa wa da abinci da gine-gine da sauransu. Ɗaukacin Hausawa za ka same su rungume da al’adunsu. Ba ma iya Bahaushen ƙasarmu Najeriya ba, har da sauran Hausawan wasu ƙasashen daban.
A JIYA, Malam Bahaushe ba ya iya cin abincinsa na dare shi kaɗai a gida. Sai dai ya ci abincin tare da sauran maƙwabtansa. Kowa zai fiddo da abincinsa, yawanci tuwo da miyar kuka su zauna cikin da’ira, suna ci kwano bayan kwano cikin annashuwa, har kowa ya koshi.
Idan kuma an samu saura bayan sun ƙoshi sukan tattara su bai wa almajirai waɗanda akasari suke rabewa a wajen domin ko sa ɗan samu saura, su ma su kashe yunwar cikinsu. Wannan al’adar ita ake yi wa laƙabi da ‘Ciyayya’ ma’ana dai cin abinci tare da abokan arziƙi. Idan kuma cikin rashin sa’a akwai wani da ranar Allah bai yassare masa ƙarfin iya fiddo da tuwon ba, hakan ba zai hana shi zuwa a ci tare da shi ba.
Wannan ma shi zai sanya abokan nasa su fuskanci yanayin rashi ko matsi da ke fuskantarsa. Idan ma ya jima cikin halin matsin rayuwa, to sauran mutanen da suke taren za su tallafa masa da ‘yan kayayyakin abinci da na masarufi. Kuma idan wani ne daga cikinsu ya ɗauki ‘yan kwanaki biyu bai samu halartar ciyayyar ta su ba, to sauran fa ba za su yi ƙasa-a-gwuiwa ba wajen tuntuɓa a game da shi ba.
Wasu har ma ba za su samu nutsuwa ba sai sun aika gidansa ko wajen mai-ɗakinsa. Idan ba shi da lafiya ne ko kuma wata matsala ta rayuwa ce ke damunsa, to za su yi yunƙurin ba shi tallafi da addu’o’i ɗaya bayan ɗaya ko kuma a ƙungiyance.
A JIYA, budurci na ‘yan mata yana da matuƙar martaba. Kusan duka ‘yan matan Hausawa suna riƙe ɗiyancinsu har a yi musu aure. Rasa ɗiyancin ‘ya mace budurwa tamkar rasa rai ne. Wannan ita ce babbar fitina ga rayuwar yarinya kafin a yi mata aure. Ana gudanar da wani bincike na al’ada domin tabbatar da budurcin ‘ya mace kafin a kai ta ɗakin aure.
Idan kuma aka samu yarinyar ba ta kai budurcinta ba, to za ta rasa rayuwarta nan take. Idan kuma wasu dalilai suka sanya ba a yi binciken ba har amaryar ta kwana a ɗakin mijinta, kuma daga bisani angon ya gano cewar ba ta tsira da budurcinta ba, to wannan sabon auren dai za a warwareshi. Kafin warwarewar auren, ‘yan uwan angon mata sukan ziyarci ɗakin amarcin washegarin tarewar amarya, domin tabbatar da shin surukarsu ta tsira da budurcinta kafin auren?
Sukan nutsu su saka ido domin nazarin wata alama duk ƙanƙantarta da ka iya tabbatar musu da amaryar nan kamammiya ce. Misali a ce sun ga wani fasasshen faranti, ko wata ƙwarya, wadda angon ya fasa domin ya tabbatar da budurcin amaryarsa ga duk wani baƙo da ka iya zuwa domin nazarin amaryar sa.
Idan kuma baƙon ya gaza ganin wata alama, yakan yi wa amaryar wata ‘yar hikima ta hanyar sanya ta ta kawo masa ruwa. Wanda a galibi a ƙwarya suke kawo ruwan. Idan suka amshi ruwan sannan suka yi nasarar ganin tsaga ko ‘yar ƙaramar ƙofa a jikin ƙwaryar, to kuma duk wani kokwanto ya kau. Amaryar ta tsira da budurcinta.
Domin karanta zuwan ilimi ƙasar Hausa danna nan
A JIYA, yawancin Hausawa ba su san soyayya kafin aure ba. Amma galibi auraren da ake dacen samun wanzuwar soyayya kafin su, to tattaunawa tsakanin saurayin da budurwar tana wakana da dare. Saurayin wanda yake samun rakiyar babban abokinsa sukan tura yaro ƙarami gidan su budurwar domin ya kira musu ita su yi hira.
Wannan wata al’ada ce da ake gudanarwa da dare. Kuma Hausawa suna yi mata laƙabi da ‘zance’. ‘Ta na zuwa’ yawanci ɗan aiken yake sanar da su bayan ya sanar da ita zuwansu. Shi kuma gogan nata yakan bai wa yaron tukwuicin ‘yan kwabbai, domin nuna yabawa da kan-gadon ɗan aikensa. Cikin farin ciki yaron zai amsa daga bisani ya ruga gida baki har kunne.
Zancensu kacokan suna aiwatar da shi cikin tsananin kunya da kamun kai. Suna zama can nesa da juna, sannan yarinyar takan gaza iya furta komai ga saurayinta, domin tsananin kunya. Sai dai ta riƙa gyaɗa kai, ko girgiza kai, a yayin da fuskarta ke fuskantar ƙasa tana kallon ƙasan.
Bahaushiyar da sam ba ta iya amsar kuɗin zance ba. Ma’ana ’yar kyautar kuɗin da saurayin zai ba ta lokacin da ya zo zance. Zai yi iya yinsa domin ta amsa, amma sam ba ta iya karba. Wannan ba komai ba ne face tsananin kamun kai da kunya da ke cikin al’adun Hausawa. Ƙarshe dai ba yadda zai yi sai dai ya aje ’yan kuɗin a gefenta. Ita ko ba za ta iya ɗauka ba sai bayan saurayin da abokinsa sun shuri takalmansu sun tafi.
Auren haɗi ko na ɗan dangi yawanci shi ne auren da Hausawan suka fi yi. Cikin ikon Allah kuma suna zamowa aure mai inganci cike da zaman lafiya. Ana ɗaukar lokaci mai tsawo ba ka ji wata husuma ta ɓullo a tsakanin ma’auratan ba.
Halayyar auratayyar Hausawa da riƙon aure a zamanin da, da kuma ƙauna da son juna da sauran su, za a iya kamanta ta da karin maganar Hausawa da take cewa ‘Naka naka ne ko ya ci namanka ba zai tauna ƙashin ba’
Hausawa kenan a wancan zamanin. Amma a wannan zamanin, mukan iya cewa labarin ya sauya salo mutuƙa gaya. Kamannin da aka san su da Malam Bahaushe su ma mukan iya cewa sun sauya. Kamar siffa da kyawunsu, duk da dai an ce shi kyau yana daga cikin idon mai hangensa.
Wannan sauyin kuma ba komai ba ne ya kawo shi face auratayya da ta shiga tsakanin Hausawa da sauran ƙabilu, kamar Fulani da Nufawa da Barebari da sauransu. Amma auratayyarsu da Fulani ta fi kowacce tasiri da ƙarfi da har ta kai yanzu ‘yan jarida suke kiransu da sunan ‘Hausa-Fulani.’
A yanzu muna iya cewa al’adar ciyayya ta yi ɓatan-dabo a cikin al’dun Hausawa. Wasu daga cikin ‘yan-matan Hausawa marasa aure sun fara sakin turbar da aka san su da bi. Abin takaici, wasu ana yaudararsu da kuɗi ko ƙyale-ƙyalen duniya domin a kawar da budurcinsu kafin aurensu.
A YAU Hausawa sun ɗauki ɗabi’ar sakin matansu a kan ‘yan matsalolin cikin aure da za a iya kawar da kai gare su, ko kuma a samo masalaha cikin ruwan sanyi. Daga bisani kuma ya bar ‘ya’yan ita wadda ya saka ɗin a hannun kishiyoyi. Yin hakan kuma ba komai ya ke haifarwa ba face jefa rayuwar yaran a matsanancin ƙunci, domin gallazawar da yaran suke sha a hannun matan mahaifinsu yawancin lokuta.
Wasu kuma matasan abin mamaki sai ka ga sun share shekaru da dama cikin tsananin soyayya, amma sai su gaza kamanta irin shekarun nan da suka yi na soyayya a cikin rayuwar aurensu. Cikin lokaci ƙalilan sai ka ji igiyar auren ta katse.
A YAU, shagulgula kamar liyafa, yanka kek da bidiri iri-iri domin gudanar da bikin aure su ne abin da Hausawa suka fi lale da shi. Ba da jimawa ba muka samu labarin wani ango da ya mula ya maƙawa amaryar tasa saki a ranar ɗaurin aurensu.
‘Yan mintuna kaɗan da a kai masa amaryar ɗakin amarcinsu. Ba kuma komai ya jawo sakin ba face labarin da ya same shi na gudanar da wata liyafa da amaryar take yi, wanda wani tsohon saurayinta ya ɗauki nauyin haɗa mata. Kuma tun fil-azal angon ya nuna ƙin amincewa da hakan.
A YAU, matasan Hausawa sun ari al’adar saɓule wando (ass down), ko saka tsukakken wando (pensil), ko askin iskanci irin na shahararren ɗan ƙwallon nan mai laƙabin Balatoli da dai sauran ƙyale-ƙyalen zamani. Wani yayi ma da bai jima sosai da shuɗewa ba, shi ne wata sabuwar rawa da ake yi mata laƙabi da ‘Dab,’ wadda wani mawaƙi ya shigo da ita ƙasar nan mai suna Olamide.
Ita dai rawar Dab an soma ta kusan shekara shida baya ko kuma kwatankwacin hakan. Kamar dai yadda mawaƙin gambaran nan na ƙasar Amurka wato Bow Bow ya faɗi, ita rawar Dab ta samo asali ne daga al’ummar Kannabis. Wannan shi ne sabon salon yayi ga matasan Hausawa.
A YAU, wasu Hausawan sun ɗauki halayyar nuna raini ga ‘yan-uwansu da ke karantar harshen Hausa a jami’o’i da sauran makarantun gaba da sakandare. Idan kuma ka ce su rubuta sakin-layi guda ɗaya da harshen Hausa, da yawansu ba za su iya rubutawa daidai ba. Turawa da Larabawa da dai sauransu, duk suna karantar harsunansu cikin alfahari da tunƙaho!
Shahararrun mutane kamar Malami-uban-malamai, Farfesa Ɗandatti Abdulkadir da Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya da Farfesa M.K. Galadanci da Farfesa Abdulkadir Ɗangambo, Farfesa Abdalla Uba Adamu da sauransu za a iya rubuta su a jikin zinare a matsayin shahararrun masana, kuma jigogi a fannin ilmi da nazarin harshen Hausa a ƙasarmu Najeriya da sauran sassan duniya.
Ƙarshe dai an san cewa taɓarɓarewa da wancakali da al’adu masu kyau na gargajiya ba a iya ƙabilar Hausawa ya tsaya ba. Sauran ƙabilun ƙasar nan su ma suna fama da irin wannan matsalolin, ko ma fiye da hakan. A taƙaice dai za mu iya cewa wannan matsala ce da ta shafi duk wani sashi na duniya, sakomakon sauyin zamani.
Hausawa ma ba su fiye wancakali da al’amuran al’adu masu kyau ba kamar wasu ƙabilun. Za mu iya cewa ƙabilar Hausa tana ɗaya daga cikin mafi kyawun ƙabilu a Najeriya da ma Afirka gaba ɗaya! Idan ka dubi Hausawan zamani, za ka amince da karin maganar Hausawan da ta ke cewa ‘Bahaushe mai ban Haushi.’ Amma dai Bahausahe ya yi gaskiya da ya ce: KOWA YA BAR GIDA: GIDA YA BAR SHI
Danna nan don karanta rabe-raben auren Hausawa
Edita; Rumasa’u M. Kallamu