Aibukan Damakwaraɗiyya Guda Ashirin Da Ɗaya (21) A Mahangar Musulunci

0
24

Mu sani cewa, aibukan da suke cikin damakwaraɗiyya suna da yawa a mahangar Musulunci, fiye da amfanin da ake ruɗarmu da su. Ga muhimmai daga cikin aibukan nata kamar haka: 

  1. Tana ba wa ɗan Adam haƙƙin kafa doka. (Sovereignty belongs to the People) A musulunci Allah kaɗai Shi ne mai kafa dokoki. Allah Shi ne mai bayar da umarni da hani, da halattawa da haramtawa a dukkanin tsarin rayuwa. Ga wasu ayoyi daga Alƙur’ani da suke tabbatar da haka:

Haƙiƙa ubangijinku shi ne Allah, Wanda ya halicci sammai da ƙasa, a cikin kwana shida. sannan ya daidaita a Al’arshi: yana rufe yini da dare (shi daren) yana nemansa (shi yinin) ciki hanzari. Da rana da wata da taurari ababen horewa ne da umarminsa. Ku sani cewa, Shi ne mai halitta (don haka) umarmi nasa ne (halacci ko haramci Allah ya ɗaukaka, ubangijin halittu (Suratul A araf, aya ta: 54). 

Wannan aya tana nuna mana cewa, kasancewar Allah shi ya halicci dukkanin halittu na cikin duniyar nan tamu, kuma shi yake sarrafa su, ya zamo wajıbi mu gane, kuma mu yarda, cewa shi kaɗai ya cancanci ya bayar da umarni da hani, da kafa dokoki. 

Na tabbata cewa lafiyayyen tunani zai yarda cewa, akwai zalunci a ce, ga wanda ya yi halitta kuma yake sarrafa ta, amma wani can ko wasu, su zama su ne masu kafa wa wannan halittar dokoki da ba su umarni da hani. Allah ya sa mu gane. 

Domin karanta bayani akan Ma’anar Damokuraɗiyya Danna nan

Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

Kuma ba ya yin tarayya da wani a cikin hukuncinsa da wani a cikin hukuncinsa (Suratul Kahaf, aya ta: 26) 

Malam ibnul jarir yace: “Allah (SubahanahuWata’ala) ba ya sanya wani, in ba shi ba cikin kaddarawarsa da hukuncinsa a Kan halittarsa. Shi kaɗai yake, a cikin hukuncinsa da ƙaddarawarsa a cikin lamarinsu. Haka nan a cikin tsara al ‘amuransu da sarrafa su, yadda ya ga dama, kuma yadda ya so. 

Shi kuma malam Muhammadul Amin Ash Shanƙiiɗi cewa ya yi: “Ma’anar Wannan aya shi ne: Allah, ya girma ya ɗaukaka, ba ya tarayya da wani, a cikin hukuncinsa. Bar wannan Hukunci, nasa ne, shi kaɗai, ya girma ya ɗaukaka. Babu hukunci ga waninsa ko ƙanƙani. Halal shi ne abin da ya halatta. Haram, shi ne abin da ya haramta, maɗaukakin sarki. Abin daya tsara shi ne Addini (watau hanyar rayuwa). Abin da ya yanke shi ne hukunci”

Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

Shin akwai wani hukunci banda na Allah? Yayi umarni kada ku bauta wa kowa sai Shi. Wannan shi ne addini (watau tsarin rayuwa) miƙaƙƙe. Amma mafi yawan mutane ba su sani ba'” (Suratu Yusufa, aya ta: 40). 

Wannan yana nuna cewa yin biyayya ga dokar wanin Allah, wadda ta saɓa wa ta Allah, bauta ne ga shi wanda ya kafa wannan dokar. Ko waɗanda suka kafa ta Malam Muhammad Mutawalli ash Sha’araawi a tafsirinsa, ya fassara: da cewa: 

“Kada ku bi wani umarni ko hani, sai abinda Allah ya saukar a tsarinsa na shiryarwa zuwa ga abinda yake daidai, kuma alhairi (ga bayinsa). 

Domin karanta tarihin damokuraɗiyya a Najeriya danna nan

Ya fassara 

Haƙiƙa wannan shi ne tsari miƙaƙƙe, ba waninsa ba. Amma mafi yawan mutane ba su sani ba, cewa manzanni Sun isar musu da wannan tsarin. Saidai cewa su ba su aiwatar da wannan ilimin ba a ayyukansu. 

Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

Kuma kada ku dinga cewa: wannan halal ne, wannan haram ne, ga abin da harasanku suke suffatawa na ƙarya kuna ƙagar ƙarya ga Allah. Haƙiƙa waɗanda suke ƙagar ƙarya ga Allah ba za su rabauta ba. ɗan jin daɗin ne kaɗan kuma azaba mai raɗaɗi ta tabbata a kansu. (Suratun Nahli, aya ta: l16-117). 

Wannan ayar tana nuna cewa, waɗanda suke kafa dokoki na halattawa da haramtawa ƙarya suke yi wa Allah. 

A nan sai mu duba girman zunubin wanda ya yi wa wani ƙarya. To ina ga wanda ya yi wa Allah ƙarya! 

Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce

“Ya kai wannan Annabi, don me za ka dinga haramta wa kanka abin da Allah ya halatta maka, kana neman yardar matanka. (Suratut Tahrimi, aya ta: 1).

Wannan aya tana nuna cewa, ba ma maganar wani ko wasu su kafa wa wasu doka ta haramta musu wani abu ake yi ba, shi kansa mutum ya haramta wa kansa cin wani nau’i na abinci haramun ne. Domin ai ba shi ya yi kansa ba. Wanda ya yi shi shi ne mai wannan haƙƙin. 

Kuma sai ayar ta yi mana wani abu mai kama da abin da Bahaushe yake cewa, a tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro. Watau sai aka hana Annabi yin haka. Watau idan wani dalili ya sa mutum ba zai ci wani nau’i na abinci ba, ko ya ji ba ya sha’awarsa sai kawai ya ce ba ya ci. Domin ba shi da ikon kafa wa kansa doka, ta haramta wa kansa wannan abincin. 

Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

“Idan kuka yi jayayya a kan wani abu, to ku mayar da shi ga Allah da Manzo. Idan kun kasance kun yi imani da Allah da ranar lahira. Wannan shi ya fi alhairi, kuma shi ne abinda ƙarshensa ya fi zama alheri (Suratun Nisa’i, aya ta : 59). 

Wannan ayar tana koyar da mu Musulmi cewa, yayın da wata matsala ta faru a tsakanin al’umma, muke son mu yi maganinta, ba haɗuwa za mu yi mu kafa wa mutane doka ba. A’a, da farko dubawa za mu yi a Al’Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), mu samo mata mafita. 

Idan ba mu samu amsa, bayyananniya ba, to sai mu duba mu ga ko ra’ayin magabata na ƙwarai ya haɗu a kan amsa guda ɗaya; Idan ba mu samu ba, to a sannan sai mu yi amfani da tunaninmu, mu aiwatar da abin da muke ganin ya fi kusa da abin da Allah yake so. Ba wai abin da mu muke so, ko abin da mutanen ƙasa suke so ba. 

Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce

“Na rantse da ubangijinka! Ba za su yi imani ba, sai sun hukunta ka a saɓanin da ya faru a tsakaninsu. Sannan ya zamo ba su sami wani ƙunci ba a zukatansu, game da hukuncin da ka yi. Ya zama sun yi cikakkiyar miƙa wuya. (Suratun Nisa i, aya ta: 65).

Ita kuma wannan ayar nuna mana take yi cewa, babu imani ga duk wanda bai hukunta tsarin da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya zo da shi ba, ya zama shi ne hukuncin da ya zaɓa ba Kuma idan aka yi masa hukunci da shi, ya ji babu wata damuwa game da shi. Sai Hadisi “Daga Adiyyu bin Hatim (Radiyallahu Anhu) ya ce: 

“Naje wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), alhali akwai “cross na zinariya a wuyana. Sai ya ce “Ya ‘Adiyyu! Cire wannan gunkin daga wuyanka Sai na ji shi yana karanta Suratu Bara ‘ah (kamar haka): 

“Sun riƙi malamansu da masu bautarsu iyayen giji. maimakon Allah Sai na ce: Ya Ma ‘aikin Allah! Ba su kasance suna bauta musu ba. Sai ya ce: “Haka ne, amma ai suna halatta musu abin da Allah ya haramta, sai su karɓi halatta warsu. 

Suna kuma haramta musu abin da Allah ya halatta, sai su karɓi haramcin su. Wannan ita ce bautar da suke yi musu (Tirmizi da Baihaƙi suka ruwaito). 

Ya zo a cikin al Mu’ jamul Kabir cewa Hatimu ya ce: Sai na ce: Ba mu kasance muna bauta musu ba. Sai ya ce: “Shin ba sa haramta muku abin da Allah ya halatta, sai ku haramta shi. Kuma halatta muku abin da Allah ya haramta sai ku halatta? Sai na ce: Eh, (muna yi) Sai ya ce: “To ai wannan ita ce bautar da kuke yi musu. 

Wannan Hadisin yana nuna mana cewa duk sanda wasu za su dinga kafa wa mutane dokokin da suka saɓa da na Allah, su kuma mutanen suna bin su, to bauta musu suke yi. Sun zama su ne allolinsu, maimakon Allah. Kokuma sun haɗa su da Allah a matsayin su ma alloli ne. Watau suna layi ɗaya da Allah, a ɗa’ar da suke yi wa Allah. 

  1. Tana Bai wa shugabanni haƙƙin Allah: (Allah’s right given to leaders) 

Damakwaraɗiyya tana sa talakawa dogaro ga shugabanni, maimakon Allah. Abin da yake janyo wannan shi ne, a tsarin damakwaraɗiyya shugabanni ne suke yi wa talakawa alƙawuran abin da za su yi musu idan suka zaɓe su. A tsarin siyasar Musulunci babu irin waɗannan alƙawuran.

Alƙawarin da shugaba zai ɗauka shi ne, ya tafiyar da talakawansa a kan tsarin littafin Allah da sunnar Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam) Shi kuwa wannan tsarin cike yake da adalci da dukkanin jin daɗi na duniya da na lahira. Domin Allah ya fi kowa son bayinsa da tausayin su. Haka nan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). 

Mu sani cewa, yana daga cikin rukunan Imani, Musulmi ya yarda cewa, abu mai daɗi da marar daɗi duka daga Allah suke. Duk da dai cewa shi marar daɗi ɗan’ adam ne yake sabbaba shi. 

To amma sai gashi damakwaraɗiyya ta sa Musulmi sun mayar da lmaninsu na samun jin daɗi ko shan wuya kacokan, a hannun shugabanni. Maganganun da mutane suke yi suna nuna cewa, yunwa da ƙoshi, daga shugabanni suke zuwa. 

Su suke janyo arziki da talauci. Walwala da ƙunci, shugabanni ne suke farar da su. Abin nufi a nan shi ne, za ka ga mutane suna ɗora duk wadannan abubuwan a kan jam’iyyar da take mulki, ko shugaban da yake mulki, ba Allah ba. 

A tsarin siyasar Musulunci duk wani jin daɗin ɗan’adam Allah ya tsara shi a Al-Ƙur’ani da sunnah. Na taɓa jin wani babban ɗan siyasa a wannan ƙasar tamu (Najeriya), yana yin wata magana kamar haka: Yana cewa PDP ce ta mayar da shi minister. lta ta mayar da shi gwamna. 

Don haka idan ka ga bai zama shugaban ƙasa ba. to Allah ne bai ba shi ba. Ka ga a nan jahilci ya sa shi ya danganta jin daɗi da nasara ga PDP, rashin jin daɗi kuwa da faɗuwar zaɓe daga Allah ne. 

Wannan yana da matuƙar haɗari. Domin ya shafi Imani da ƙaddara. Abu mai daɗi daga Allah ne, sai bawa ya godewa Allah. Marar daɗi ma daga Allah ne amma ɗan’adam ne yake sabbaba shi. Ko kuma Allah ne ya jarrabe shi. Sai bawa ya koma ga Allah ya gyara kurakuransa. Kuma ya yarda cewa, Allah ya san rashin ba shi wannan abin shi ya fi alhairi a gare shi, shi ya sa bai ba shi ba.

Abin nufi dai a nan shi ne, mu sani cewa Allah yana da ta cewa, kuma yana da ruwa da tsaki a tafiyar da harkokinmu. Idan muka saɓa wa tsarinsa, to komai daɗewa, kuma ko da mun ga kyan lamarin da muka tsara wa kanmu da farko, to za mu gamu da taɓarɓarewar Al’amura daga baya. Allah (SubahanahuWata’ala) yana cewa: 

“Idan da mutanen gari (ko ƙasa) za su yi imani, su ji tsoron Allah, da mun buɗè musu albarkatu daga sama da ƙasa Amma sun ƙaryata, Sai muka riƙe su da abin da suka kasance suna aikatawa” (Suratul A araf, aya ta: 96). 

Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

“Allah ya buga misali da wani gari, wanda yake cikin aminci,cikin nutsuwa, arzikinsu mai yawa, yana zuwar musu daga ko na. Sai Suka kafirce wa ni’imomin Allah Sai Allah ya ɗanɗana musu tufafin yunwa da tsoro, sabo da abin da suke aikatawa (Suratun Nahli, aya ta:112). 

Wannan yana nuna mana cewa, rashin bin Allah a tsarin tattalin arzikinmu da zamantakewarmu shi yake sawa komai namu yake taɓarɓarewa. Kuma mu kasa gano bakin zaren. Allah ya sa mu gane. 

Kuma Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

“Kuma duk abin da ya same ku na musiba, to a dalilin abin da hannayenku suka aikata ne. Kuma (Allah) yana yin afuwa kan abubuwa masu yawa (Suratus Shura, aya ta: 30). 

Kuma dai Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa: 

“Abin da ya same ka Kyakkyawa daga Allah ne. Amma abinda ya same ka mummuna, (to asalinsa) daga gare ka ne” (Suraun Nisa , aya ta: 79). 

  1. Tana Raba kan al’umar Musulmi: (Muslim Nation becomes divided) A tsarin damakwaraɗiyya, ɗan ƙasarka shi ne ɗan’uwanka, wanda kuke al’umma ɗaya. A musulunci kuwa, Musulmi, a ko’ina yake, shi ne ɗan’uwanka, wanda kuke al’uma ɗaya.

Don haka lallai ne kada Musulmi ya so wanda ba Musulmi ba, so har zuci. Kada kuma ya haɗa kai da wanda ba Musulmi ba a cuci Musulmi. Lallai ne mu kula da wannan. 

Domin yana da matukar haɗari. Haɗuwa a jam’iyya daban, haɗuwar addini daban. Kada mu fifita haɗuwar jam’iyya a kan dangantakar mu ta ‘yan uwantakar Musulunci. Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa: 

“Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku riƙi Yahudu da Nasara abokai mataimaka juna. Sashinsu da sashi abokan juna ne. Wanda duk ya riƙe su abokai daga cikinku, to yana cikinsu. Allah ba ya shiryar da mutanen da suke azzalumai (Suratul Ma ‘idah, aya ta: 51). 

Abin nufi a nan shi ne, kada mu yarda a cusa mana son ƙasa, ta yadda za mu daidaita Musulmi da wanda ba Musulmi ba. 

Kada ka yarda ka ƙaunaci Yahudu ko Kirista, balle har ma ta kai ka ga taimaka masa a kan Musulmi. Musulmi shi ne ɗan uwanka. Shi kuwa wancan yana da nasa ɗan uwan, wanda suke addini ɗaya. Don me za ka tafi cikinsu ka ɗakko ɗan uwa , ka bar ‘yan uwanka. Ai ka ƙara musu yawa ke nan. Saboda haka ka zama nasu. 

  1. Tana Farar da ƙiyayya da gaba da tashin hankula a tsakanin Musulmi: (It Promotes enmity and Violence) 

Damakwaraɗiyya tana farar da gaba tsakanin Musulmi. Wannan yana faruwa ne saboda raba kawunan Musulmi . Wannan gaba takan kai har ga ɗaukar makamai da kisan juna. Ka ga ke nan, maimakon Allah ya umarce mu mu yaƙi kafirai, domin yaɗa tsarinsa a bayan Kasa (watau addinin Musulunci), mun ƙi yi, sai damakwaraɗiyya ta umarce mu da mu yaƙi Junanmu, muke ta bin umarninta. Allah ya sa mu gane. Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

Ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗayanku. Kada ku rarraba” (Suratu Ali Imrana, aya ta:103). Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce:

“Wanda duk ya kashe mumini da gangan, to sakamakonsa wutar Jahannama. Zai dawwama a cikinta. Kuma Allah ya yi fishi da shi. Ya la ‘ance shi. Ya tanadar masa azaba mai girma (Suratun Nisa’i, aya ta: 93) 

Daga lbnu Umar (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce : ”Mumini ba zai gushe ba cikin yalwa (ta samun gafara) a cikin addininsa, matuƙar bai zubar da jini haramtacce ba (Bukhari ne uwarto). 

Daga Barra’u bin Azib, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “A ce duniya babu ita, ya fi sauƙi a wajen Allah, da a ce an kashe ran Mumini ba da haƙƙi ba (lbnu Majah yaruwaito). 

  1. Tana Sa Yin Alƙawura, har ma da na ƙarya: (False Promises & Lies) 

Wannan addinin namu ya wajabta mana cewa, idan mutum ya yi alƙawari lallai ya cika. Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: “Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku dinga cika alƙawura na mu’amaloli (Suratul Ma idah, aya ta: 1). 

Haka nan addininmu ya koyar. da mu cewa, maƙaryaci babban munafiki ne. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: 

“Alamar munafiki uku ce: “Idan ya yi zance ya yi ƙarya. Idan ya yi alƙawari, ya saɓa. Idan aka amince masa, ya yi ha’inci” (Bukhari da muslim suka ruwaito). 

  1. Tana Sa Bayar da Rashawa Da Yin Ƙage A Yayin Zaɓe (Bribery & Blackmailing) 

Rashawa ita ce abin da a ke bai wa ma’aikacin gwamnati, na kuɗi ko wani abin, domin ya yi abin da bai halatta ba, ko ya ƙi yin abin da yake shi ne wajibi a mas’alar da take gabansa. 

Daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya tsine wa mai cin rashawa da mai bayar da ita a hukunci” (Tirmizi ne ya ruwaito).

Daga Abdullahi bin Amr (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Allah ya tsine wa mai cin rashawa da mai bayar da Ita” (Tirmizi da waninsa suka uwaito). 

A Najeriya ana kiran wannan ɗabi’a da sunan, cin hanci da rashawa. Wannan ya haɗa abin da muka faɗa a sama, da ma duk wata hanya ta satar dukiyar jama’a. Mu sani cewa, a Musulunci satar dukiyar gwamnati babban laifi ne. Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

Wanda duk ya ɗauki dukiyar jama’a a ɓoye (watau dukiyar gwamnati zai zo da abin da ya ɗauka ranar ƙiyama “(Suratu All lmrana, aya ta: 161) 

A Hadisi, Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya nuna cewa, duk wanda ya zo ranar al Ƙiyama da dukiyar gwamnati a rataye a wuyansa, to kada ma ya kusanto shi. Domin ba-shi, ba-shi2 

Kuma yana da kyau mu sani cewa, akwai wasu hanyoyi na zalunci a Najeriya waɗanda suke halattattu a dokar ƙasa amma a Musulunci Misali: Maƙuɗan kuɗaɗen da ‘yan majalisun tarayya da na jihohi suke yanka wa kansu da sunan albashi ko alawus. 

Haka nan abin da ake yanka wa gwamnoni da mataimakansu, wanda ya wuce ma aunin hankali da adalci, bayan sun bar aiki. Waɗannan duka, da ire- irensu haramun ne a Musulunci. Domin a Musulunci duk abin da za a yi sai an ɗora shi a kan ma’aunin adalci. Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa: 

” (Allah) Ya ɗaukaka sama, ya Sanya ma auni. Domin kada ku yi fin ƙarfi a ma auni. Ku tsayar da ma’auni da adalci, kada ku tauye ma ‘auni (Suratur Rahman, aya ta: 7-9). 

Allah yana gaya mana cewa, ya ɗaukaka sama ya sanya ma`auni, watau ya daidaita ta (nauyinta bai sa) ta faɗo a kan ƙasa ba. Don haka kada ku yi fin ƙarfi a ma’auni. Watau ku ƙara shi, idan za ku auna wa kawunanku. Ku rage shi idan za ku auna wa wasu.

A nan ba ma’aunin kwano da na sikeli da na yadi da ma’unin ƙasa kaɗai, ake nufi ba. Wan nan ya haɗa ma’unin mu’amalolin jama’ a gaba ɗaya. Watau a tsakanin shugabanni da talakawa ya zamo akwai ma’aunin adalci. 

A tsakanin masu kuɗi da matalauta ya zamo akwai ma’aunin adalci. A tsakanin mai gida da iyalinsa ya zamo akwai ma’unin adalci. Haka nan tsakanin mai saye da mai sayarwa, da mai yin aiki da mai bayar da aiki, da sauransu. Wannan ne ya sa Allah ya ce: 

Watau “ya sanya ma`auni domin kada ku yi fin ƙarfi a tsakaninku da juna” Wannan yana nuna mana cewa ma aunin adalcin da Allah ya sa a tsakanin sama da ƙasa , shi ya sa saman ba ta faɗo a kan ƙasa ba. 

Don haka idan ba mu yi adalci a harkokinmu na rayuwa ba rayuwarmu za ta hargitse ko ma ta ruguje baki ɗaya. Mu rasa yadda za mu daidaita ta. Shi kuwa adalcin ba wani ba ne illa bin tsarin Allah (Subahanahu Wata’ala). 

Halin da muke ciki a Najeriya na satar mutane da kashe-kashe da tashin hankula iri-iri, a wannan zamani na damakwaraɗiyya, ya isa ya ja hankalinmu mu, mu dawo kan hanya. 

  1. Jam’iyyar Da Ta Yi Nasara Tana Komawa Kamar Sarautar gado: (Winning Party beconmes the Monarchy) 

Wannan yana nuna cewa an koma a gidan jiya, wadda masu ƙago damakwaraɗiyyar suka guda tun asali. Watau tsarin mulukiya na din-din-din Akwai wani karin Magana da ake cewa an ƙi cin biri an ci dila. 

  1. Tana Fifita Yawa A Kan Hankali Da Nagarta: (Majority is right ) 

Sanin kowa ne cewa, rinjaye a tsarin damakwaraɗiyya yana ga tarin jama’a. Duk inda jama’a suka fi yawa to su suke da rinjaye. 

Amma ya wajaba Musulunci yawa ba shi ne ma’auni ba Nagarta ita ce ma’auni a Musulunci Ayoyin al – Ƙur’ani suna nuna mana cewa duk inda yawa yake da wuya a sami abin kirki. Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa:

“Mafi yawan su (su kafirai) ba sa yin imani da Allah, face suna mushrikai” (Suratu Yusufà, aya ta: 106). Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa

“Gaya mu su: Ku yi tafiya a bayan ƙasa, ku duba ku ga yaya ƙarshen waɗanda suka gabace ku ya kasance, mafi ya wansu sun kasance mushrikai (Suratur Rum, aya ta: 42) Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa: 

“Mafi yawan mutane ba za su yi imani ba, ko da ka yi kwaɗayin hakan (Suratu Yusuta, aya ta: 103). Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa: 

Alif, Lam, Ra, Waɗannan ayoyin littafi ne. Wannan da aka saukar a gare ka daga ubangijinka gaskiya ne Sai dai mafi yawan mutane ba za su yi ba“(Suratr Ra a’di, aya ta: 1). 

Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa: 

“Haƙiƙa a cikin wannan akwai aya. Mafi yawan su ba za su yi imani ba” (Suratush Shu’ara i, aya ta: 8). 

Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa: 

“Haƙiƙa azaba ta tabbata a kan mafi yawansu, haƙiƙa su ba za su yi imani ba (Surat Yasim, aya ta: 7). 

Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa

“Haƙiƙa alƙiyama za ta zo. Babu kokwanto a ciknnta. Amma mafi yawan mutane ba sa yin imani (da ita) (Suratu Gafir, aya ta: 59). 

Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa: 

Idan ka biya ta mafi yawan waɗanda suke bayan ƙasa za su ɓatar da kai ga barin tafarkin Allah. Ba sa bin komai sai zato. Kirdado kawai suke yi” (Suratul An ‘am, aya ta: 116).

Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa: 

“Kuma kaɗan ne daga cikin bayina masu godiya (Suratu Saba, aya ta: 13) Wannan duka yana nuna cewa, yawa ba shi ne yake nuna mutane suna kan daidai ba. Bin tsarin Allah shi yake nuna daidai. 

Domin karanta cikekken littafin  Danna nan 
labarin da ya wuceWuraren Da Ake Zaton Damakwaraɗiyya Ta Yi Kama Da Musulunci
Labarin na GabaDamakwaraɗiyya A Tsakanin Dabbobi