Addu’ar Ƙin Shu’umci

0
34

khairatu.shehu

 

اللهُمَّ لاَ طَيْرَ إِلا طَيْرُكَ وَلَا خَيْرَ إِلا خَيْرُكَ وَلاَإِلَهَ غَيْرُكَ

Allahumma la ɗaira illa ɗairuka wala khaira illa khairuka wala ilaha gairuka

Ya Allah! Babu shu’umci sai abin da Ka halitta, kuma babu alheri sai alherinka, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba.

Ƙarin Bayani; Shu’umci shi ne mutum ya kudurce cewa wani abu mummuna zai faru gare shi saboda ganin wani abu ko jin sa. Wannan haramun ne, saboda abin da ke cikinsa na jingina tasiri ga wanin Allah, da kuma munana zato ga Allah. To wanda irin wannan ya afku gare shi, kar ya bar aikata abin da ya yi nufin yi; sai ya tuba ga Allah, sannan kaffararsa ita ce ya faɗi wannan addu’ar. [Bayanin mai tarjama].

Don karanta Addu’ar Wanda Ya Ji Wani Ciwo A Jikinsa danna nan

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTarihin Malam Attahiru Shehu Na Liman (Limamin Masallacin Shehu)
Labarin na GabaAddu’a Ga Wanda Aka Zo Biyansa Bashinsa