Hanyar bauta wa wani abu wanda mutum yake tsammanin shi ne zai biya masa bukatun rayuwar yau da kullum shi ne addini. Addinin farko na mutanen ƙasar Hausa shi ne addinin gargajiya, wato tsafi ta hanyar bautar iskoki ko mutanen ɓoye da kuma bori da camfi.
Irin wannan addini ya faru ne ta bin wasu hanyoyi da mutane suka ƙaga wa kansu ta bautar waɗansu abubuwa don cimma biyan buƙatunsu na rayuwa. Wannan hanyar bauta ta daɗe ƙwarai a dukkan sassan duniya ba ƙasar Hausa kawai ba. Mutanen da suka fara zama a duniya ne suka ƙirƙiro ta, daga nan sai abin ya zama al’ada ga sauran ƙabilun da suke biye da su har ya zo ga Hausawa.
A sakamakon shigowar addini Musulunci cikin ƙasar Hausa da kuma karɓar sa da mafi yawancin Hausawa suka yi, irin wannan addini ya sami rauni. Amma duk da haka ba a bar yin wasu abubuwa waɗanda suka danganci addinin gargajiya na Hausawa ba. Don kuwa za a ga yana yin tasiri a kan wasu al’amuran da suka shafi rayuwar wasu Hausawa ta yau da kullum.
Idan muka waiwaya muka duba yadda al’ummar Hausawa suka gudanar da addininsu na gargajiya, za mu ga ba wai suna sassaƙa wani gunki ne suna bauta masa ba, a a, suna yin bautarsu ne ta hanyar yin tsafi. Bauta ta hanyar tsafi tana nufin bauta wa wani iska da aka ɗauka yana zaune a wani wuri na daban. Ire-iren wuraren da aka ɗauka iskoki suna zama sun haɗa da wata kwankwamar dutsi ko cikin wata sarƙaƙƙiya ko wurin wata tsohuwar bishiya, irinsu kuka da tsamiya da marke da dai sauransu.
Misali, a Kano an bauta wa iska Tsumburbura wanda aka ɗauka ya zauna a Dutsen Dala, Kainafara-Arnan Birchi suna bauta wa iska Ɗantalle wanda suka ce yana zaune a cikin Dutsin Birchi. Arnan Kwatarkwashi kuma suna bauta wa Ƙunƙurutu wanda suka ɗauka yana cikin Dutsin Kwatarkwashi, arnan Sauna kuma suna bautar Magiro.
Haka kuma a duwatsun Kufena ta Zariya mazaunan farko a wannan wuri sun ɗauka akwai wasu iskoki da suke zaune a wannan wuri. Saboda suna biya masu buƙatunsu shi ya sa suke bauta masu. A ƙasar Katsina ma akwai wasu arna da suke bautar Magiro a Safana da Ɗan-musa da Ƙanƙara da Dutsin-ma wanda suka ce yana zama a wurin tsamiya mai sarƙaƙƙiya da duhu, kuma ba mai iya zuwa wurin da yake sai masu yi masa hidima
Bayan addinin gargajiya sai addinin Musulunci wanda addini ne da Allah Maɗaukakin Sarki ya aiko ta hannun Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) don ya zama hanyar shiriya ga al’ummomin duniya, ya kuma zama hanya madaidaiciya a gare su. Wannan kuwa ya faru ne a cikin shekara ta 610 Miladiyya.
Addinin Musulunci ne ya biyo bayan addinin Kirista wanda Allah Maɗaukakin Sarki ya aiko ta hannun Annabi Isa, Allah ya ƙara yarda da shi. An sami shekaru ɗari shida a tsakanin waɗannan addinai (Ibrahim, 1982:63 da Gusau, 2005:18-19). Ba kamar sauran addinan da suka gabace shi ba, addinin Musulunci an aiko da shi zuwa ga dukkan al’ummomin duniya don ya zama hanyar shiriya ga kowa.
Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) ya fara da kiran ‘yan’uwansa zuri’ar Banu Hashim don su karɓi wannan addini. Wasu suka karɓa wasu kuwa suka ƙi. Sannu a hankali yana wa’azi shi da waɗanda suka fara ba shi goyon baya, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci sai da dukkan ƙasashen Larabawa suka amshi addinin Musulunci.
Wannan ne ya sa aka kafa Ƙungiyar Al’ummar Musulmi wadda take da cibiya a Birnin Madina, Annabi shi ne shugaban wannan al’umma. Dukkan abin da zai zartar, sai ya yi shawara da sahabbansa. Wajen tafiyar da wannan al’umma ba a nuna ƙabilanci ko fifiko a tsakanin jama’ar da suke cikinta. Abin da ta sa gaba shi ne haɗin kai da son juna da nuna ‘yan’uwantaka a tsakanin Musulmi. Babban tsarin mulkin wannan al’umma shi ne shari’ar Musulunci. Kafin Annabi ya yi ƙaura, ya bar wa al’ummar Musulmi Alƙur’ani mai tsarki da kuma Hadisai don su yi masu jagora dangane da addininsu (Ibrahim, 1982:63).
Manyan shika – shikan addinin Musulunci biyar ne:
- Shaidawa ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) bawansa ne kuma manzonsa ne.
- Tsayar da salla.
- Bayar da zakka.
- Yin azumin watan Ramalana.
- Ziyartar ɗakin Allah don yin aikin Hajji ga wanda ya sami iko.
Bayan ƙaurar Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) da kuma zaɓaɓɓun halifofi huɗu da suka biyo bayansa. An sami wasu daga cikin sahabbai da wasu malamai da suka biyo bayansu, sun kawo hanyoyin da suke ganin ya dace a riƙa yin aikace-aikacen addini don samun sakamako mai kyau a duniya da lahira. Wannan ne ya sa aka sami ɗariƙu da ƙungiyoyin addini mabambanta masu yawa waɗanda suke da magoya baya a ko’ina.
Daga cikin ire-iren waɗannan ɗariƙu akwai Ƙadiriyya da Tijjaniyya da dai sauransu da dama. Haka kuma akwai ƙungiyoyin addini waɗanda suka haɗa da Ƙungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a wa Iƙamatus Sunna wato Ƙungiyar Kawar da Bidi’a da Tsayar da Sunna. Akwai kuma Ƙungiyar ‘Yan’uwa Musulmi (Shi’a). Waɗannan ɗariƙu na Ƙadiriyya da Tijjaniya suna da magoya baya sosai a cikin ƙasar Hausa. Haka su ma waɗannan ƙungiyoyi suna da nasu magoya baya a sassa daban-daban na ƙasar Hausa (Ibrahim, 1982:98-99, ‘Yanɗaki, 1997:46-50 da Suleman, 1997: 58-59).
Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA
MAYU 2009/JUMADA ULA 1430
Edita@rumasau-kallamu