Abubuwan Da Suke Hana A Karɓi Gaskiya

0
20

Haƙiƙa Allah Ta’ala ba ya barin bayinsa cikin ɓata, face sai ya kawo wanda zai bayyana musu gaskiya. Masu rabo sai su bi gaskiyar, wasu nan take, wasu kuma sai an turza.

Amma marar rabo sai su kafe a kan ƙarya duk duhunta, su ki karɓar gaskiya komai haskenta. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Irin waɗannan mutane suna fama da waɗansu cututtuka waɗanda su ne suke hana su karɓar gaskiya bayan ta bayyana a gare su, waɗannan cutuka, suna da yawa, muhimmai a cikinsu su ne: 

1- Jahilci mugun ciwo. 

2- Shiga cikin ruɗun da ƙarya za ta cakuɗa da gaskiya. 

3- Maƙaryaci ya ɗauki kansa a matsayin mai gaskiya. 

4- Sakaci wajen neman gaskiya. 

5- Tsoron wanin Allah in an bi gaskiya. 

6- Son girma da ɗaukaka. 

7- Makauniyar biyayya ga jagorori ko iyaye ko malamai 

8- Jiji da kai. 

9- Girman kai rawanin tsiya. 

10- Hassada ga wanda gaskiyar ta bayyana a hannunsa. 

11- Bin ra’ayin ƙungiya ko jam’iyya ko mazhaba. 

12- Aikata zunubai suna sa tsatsa a zuciya ta hana gaskiya shiga. 13- Rashin roƙon Allah shiriya. 

14- Sakacin malamai wajen bayyana gaskiya har mutane su saba da ƙarya su yarda da ita. 

15- Sabo da tasowa a kan abin da ba na gaskiya ba. 

16- Yi wa addinin Allah ɗauki ɗaiɗai. 

17- Rarar magana da ci da sha da kallo da sauransu. 

18- Ganin yadda masu gaskiya suke shan wahala a duniya. 

19- Idan aka maƙala ɗan wani abu ƙanƙani na gaskiya a jikin ƙarya sai rabuwa da ƙaryar ya yi wahala. 

20- Cuɗanya da marasa gaskiya. 

21- Rashin sauraron ra’ayin waɗanda suka saɓa wa mutum da auna nasu da nasa da ma’auni na gaskiya. 

22- Yawaitar marasa gaskiya da rinjayensu. 

23- Ɗabi’ar ran ɗan’adam, takan ji ɗacin gaskiya.

24- Fara yarda da abu, kafin a tabbatar da hujjarsa, kamata ya yi sai ka ga hujja ka ƙarfafa bayyananniya sannan ka yi imani da abu. 

25- Rashin sanin halaye da maganganun marasa gaskiya. 

26- Rashin fahimtar haƙiƙanin ƙarya. 

27- Bin gurɓatattun aƙidu, da hanyoyin ɓata. 

28- Idan malami mai faɗa a ji ya kasance a kan ɓata zai yi wuya a bi gaskiya sai fa in shi ne ya yi mi’ara koma baya. 

29- Goyan bayan manya ga matasa gaskiya. 

30- Nauyin baki da kasalar masu gaskiya wajen yaɗa gaskiyar. 31- Rashin bin hanyoyin hikima wajen faɗar gaskiya. 

32- Neman gàskiya a wurin marasa gaskiya, kamar wurin wani ɓatacce ɗan bidi’a. 

33- Rashin Neman shawara ta gaskiya. 

34- Makirce-makircen marasa gaskiya wajen yaɗa ɓarnarsu da farautar mutane.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceMatakan Zaman Lafiyar Kishiyoyi, Haƙuri Da Junansu A Kan Kurakurai
Labarin na GabaIngantattun Hadisai Kan Falalar Ranar Ashura Da Azumin Ranar