Abubuwan Da Suke Haifar Da Mura Wacce Ba Ta Warkewa (Causes Of Chronic Rhinitis)

0
29

Mura ita ake kira “cold” a turance. Ƙwayoyin cutar virus su ne suke haddasa mura. Amma yana da kyau mu fahimci cewa akwai ƙwayoyin cutar virus daban-daban waɗanda suke haddasa mura, wasu suna sanya mura maras tsanani, wasu kuma suna haifar da mura mai tsanani. 

Misali ƙwayoyin cutar mura su ne: rhinoviruses mai haifar da mura ta yau-da-kullum, corona viruses mai haifar da mura mai tsanani da sarƙewar numfashi, respiratory syncytial virus (RSV) mai haifar da mura ga ƙananan yara, adeno viruses mai haifar da sarƙewar numfashi da ciwon ciki da ciwon ido, entero viruses mai haifar da zazzaɓi, human parainfluenza viruses (HPIV) mai haddasa tsananin zazzaɓi ga yara ƙanana, metapneumo virus mai kama yara ƙanana da manya da kuma haifar da sarƙewar numfashi tare da zazzaɓi.

Yawanci cututtukan da ƙwayoyin virus suke haddasawa ba su da magani na kai-tsaye. Ma’ana, babu maganin da mutum zai sha domin magance su na din-din-din (complete and permanent cure), sai dai a shawo kansu su lafa ƙwarai ta yadda ba za su iya yin tasirin haifar da rashin lafiya a cikin jikin mutum ba.

Misali, idan mutum yana da cutar HIV/AIDS, har yanzu ba a gano maganin cutar na din-din-din ba, sai dai a ɗora shi akan magungunan da za su kashe kaifin ƙwayar cutar har ta zamo ba ta da tasirin cutar da shi ko abokan zamansa (antiretroviral therapy).

Haka nan ƙwayar cutar hanta (hepatitis virus), ba ta fita daga cikin jikin mutum gaba-ɗaya, sai dai ta yi sauƙin da ba za ta iya haifar masa da matsala ba ko kuma abokan zamansa, matuƙar an yi masa allurar riga-kafinta kafin ta kama shi, ko kuma maganinta bayan ta kama shi.

Ita ma cutar mura haka take, lafawa yake yi, ma’ana magungunan mura ba su kashe ƙwayar cutar mura kwata-kwata. Abinda suke yi shi ne su magance alamomin da mura take zuwa da su (symptomatic treatment or supportive care). A nan ina nufin abubuwan da magungunan mura suke warkarwa su ne ciwon kai, toshewar hanci, zazzaɓi, tari, ciwon ido, da sauransu.

Amma ba ƙwayar cutar virus ta mura suke magancewa ba. Kuma ƙwayoyin cutar virus na mura sun fi hayayyafa a lokacin da mutum yake yin zirga-zirga, amma da zarar ya kwanta wuri daya, to, za su rage hayayyafa. Wannan shi ne babban dalilin da yasa yawanci magungunan mura suke ƙunshe da sinadaran kashe jiki ne (sedative agents), kamar diphenhydramine ko chlorpheniramine.

Sa’annan, abin lura shi ne, a lokacin da mutum ya kasance yana fama da mura na tsawon lokaci ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, to, abubuwan da za su iya haddasa hakan su ne:

  1. Kamuwa da ciwon mura mai tsanani (chronic rhinitis) ko kuma cututtukan bututun hanci (nasal passages issues).

2. Kamuwa da cutar asma (asthmatic attack) ko bijirewar hanci sakamakon yin mu’amala da wasu abubuwa da suke jawo mura akai-akai (allergies), kamar mu’amala da ruwan sanyi, ko ƙanƙara, ko iska, ko ƙura, ko hayaƙi, ko turare, ko yaji, da sauransu.

3. Matsalar raunin garkuwar jiki (weak immune system) sakamakon kamuwa da wasu cututtuka na daban, wanda hakan yake sanya garkuwar jiki ta kasa dakushe kaifin ƙwayar cutar mura.

Saboda haka, idan mutum ya ga yana fama da cutar mura, kuma ya ga duk maganin da ya sha ba ya warkewa na dogon lokaci sai murar ta dawo, to, sai ya lura da abubuwan da yake yin mu’amala da su yau-da-kullum. Idan ya gane abinda yake haddasa masa murar, to, sai ya daina yin mu’amalar da su. Kenan mutum ba ya buƙatar yin amfani da wani magani.

Idan kuwa bai gane ba, to, yana da kyau ya je asibiti domin ganin ƙwararren likitan kunne da hanci da makogoro (Otolaryngologist), saboda ya yi masa gwaje-gwaje ya tabbatar da abinda yake faruwa da shi.

Danna nan don karanta Larurar Sanyin Gaba  (Genital Infaction)

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceTarihin Marigayi Malam Mammada Kudan
Labarin na GabaMenene Motsin Rai?