Nasihohi Goma Ga Masu Kula Da Dukiyar Al’umma

0
18

Duk shugaba ko ma’aikaci ko wani wakilin jama’a da dukiyar al’umma take gilmawa ko shigowa hannunsa, to haƙiƙa yana cikin babban haɗarin da babu abinda zai ƙwace shi sai tsananin yaƙi da zuciya wajen

Kau da kai da haƙuri da kaucewa cin wannan dukiya ta hanyar da ba ta halattaba, tare da yawaita addu’ar Allah Ta’ala ya ba shi ikon sauke nauyin da yake kansa da kula da amanar da aka damƙa masa. 

Amfani da wannan nasihohi goma za su taimaka ƙwarai da gaske wajen tabbatar da haka; 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

1) Ka kasance mai imani da cewa dukkanin dukiya ta Allah ce shi kaɗai kai matsayin wakili kawai kake, shi ne ma ya sa aka shata maka dokoki da sharaɗai kan yadda za ka yi mu’amala da wannan dukiyar kuma za a bincike ka akan hakan ranar lahira. Saboda haka ka tabbatar duk abinda zai zo hannunka ka tabbatar halal ne tsantsa kuma ka yi amfani da shi ta hanyar da ta dace da shari’ar Allah Ta’ala. 

2) Ka kasance mai imani na gaskiya mai amana da kamewa da wadatar zuci sannan ka san hukunce-hukuncen musulunci, da suka shafi harkokin dukiya da kula da ita da kuma yin aiki da su. 

3) Ka sani cewa dukkanin ɗan ƙasa yana da haƙƙi a cikin dukiyar ƙasa kai ma ɗaya ne daga cikinsu, saboda haka, kada ka nuna son kai ko son zuciya da bambanci wajen bai wa mai haƙƙi haƙƙinsa. 

4) Ka sani cewa kare dukiyoyin al’umma daga sata, salwanta da lalacewa wajibi ne akan kowa, musamman ma’aikata da shugabanni. Saboda tsaron dukiyar al’umma yana daga cikin manufofin shari’ar addinin musulunci. 

5) Ka guji cin amana da ɓarnatar da dukiyar al’umma ka sani ranar ƙiyama za a bincike kan duk abinda ka mallaka ka yi bayanin ta yadda ka same shi da kuma yadda kayi amfani da shi. 

6) Ka guji yin amfani da dukiyar al’umma akan buƙatunka na ƙashin kanka wanda ba su shafi aikinka ba. Misali kada ka rinƙa amfani da motar ofis wajen kai mata ko yara unguwa ko makaranta, ko ka ɗauki wani abu ka kai gidanka kana amfani da shi, ko kuma ka rinƙa amfani da injina ko kayan aikin ofis ɗinka ko ma’aikatarka.

7) Ka yi mu’amala da dukiyar al’umma kamar yadda ake mu’amala da dukiyar maraya. Duk abinda mutum ya ci daga dukiyar marayu ba tare da haƙƙi ba, ya ci wuta balbal. Wajibi ne a rinƙa juya dukiyar marayu tana ƙaruwa, kuma a yi saboda Allah ba don neman a biya ka ba, sai dai in ka kasance mabuƙaci to sai a rinƙa biyanka ladan aikinka. To albashin ma’aikaci da shugabanni shi ne a matsayin ladansu. 

8) Ka sani cewa kare dukiyar al’umma wajibi ne akan kowa da kowa da kowa ba wai sai shugabanni ba kawai, saboda haka ya wajaba kowa ya bayar da gudunmawarsa wajen yaƙar ɓarnatar da dukiyoyin al’umma gwargwadon ikonsa. 

9) Ka guji ƙoƙarin tara kuɗi ta hanyar amfani da ofishinka, kada ka yi sata, kada ka danne haƙƙin kowa, kada ka karɓi na goro, kada ka ci hanci da rashawa. 

10) Ka sani cewa Allah Ta’ala zai yi maka hisabi kan duk abinda ka aikata a ranar da dukiya da ‘ya’ya da ‘yan uwa ba za su yiwa mara gaskiya wani amfani ba. 

Yi ƙoƙari ka bar wa ‘ya’yanka halal komai ƙanƙantarsa sai Allah ya sanya masa albarka ya inganta bayanka. Kada ka tara haram ka mutu ka bar magada, ba za su yi albarka ba, kuma bayanka ba zai yi kyawu ba. 

Ɗan uwa ka kula da wannan nasihohi ka yi aiki da su za su amfane ka a duniya da lahira. Allah ya sa mu dace amin.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan 

labarin da ya wuceHanyoyin Tabbatar Da Adalci
Labarin na GabaWasu Daga Cikin Hanyoyin Ɓarnatar Da Dukiyar Al’umma