Sallar kisfewar rana da wata sunna ce mai ƙarfin gaske. Ana yin sallar kisfewar rana a cikin jam’i tun daga lokacin da hasken ta ya dusashe har zuwa dawowar hasken.
Ga yadda ake yin wannan sallah:-
1- Ayi kabarar harama, a karanta addu’ar buɗar sallah (Istifah) ayi a’ uzu billahi, a karanta fatiha sannan a yi dogon karatu kimani suratul Baƙara.
2- Sai a yi dogon ruku’u kwatankwacin wannan tsayuwar.
3- Sai a ɗago daga ruku’u a ce: Sami allaahu li hamidahu, rabbana walakal hamdu.
4- Maimakon, a tafi sujjada sai a karanta fatiha da doguwar sura kwatankwanci Ali – imaran.
5- Sai a sake dogon ruku’u kwatankwacin tsayuwar ta biyu
6- Sai a ɗago daga ruku’u a ce: Sami allaahu li hamidahu rabbana walakal hamdu”.
7- Sai sujjada, sai zama, sai sujjada ta biyu.
8- Sannan sai a tashi zuwa raka’a ta biyu, a yi kamar yadda aka yi a raka’a ta farko sai dai ana rage yawan tsayuwa da tsawon ruku’u.
Idan aka gama hasken ranar bai dawo ba, sai a sake yi har dai hasken rana ya dawo; kuma a bayyane ake yin karantun ta. Amma Kisfewar wata wanɗansu malamai suna cewa ana yin irin wannan Salla in ya faru; waɗansu kuma suka ce a’a raka’a biyu ko fiya kawai za a yi kuma ba a jam’i ba.
Amma babu inda aka ce a fita ana ihu da kururuwa da kade- kadde da raye-raye da waƙe-waƙe; wai don wata ko rana suna zazzaɓi wannan bidi’a ce mummuna.