Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah.
A yau zamu koyar da yadda ake yin Biskit ɗin Gyaɗa (groundnut cookies); ku biyoni a sannu domin mu koya tare…
Ko kun san Gyaɗa na rage haɗarin kamuwa da ciwon zuciya wato cardiac disease.
Abubuwan Buƙata
- Fulawar gyaɗa ½ kofi
- Fulawa 1 cup
- Bota ½ cup
- Siga ½ rabin kofi
- Filebo flavor babban cokali daya
- Baƙin hoda Baking powder ½ tablespoon
- Bicarbonate soda ½ teaspoon ƙaramin chokali
Yadda Ake Haɗawa
- A buga siga da bota sai aukin ya ninku
- A saka sauran kayan (fulawa, filebo, baking powder, bicarbonate soda da sauransu). A juya har sai yayi tauri.
- A murza da rolling pin sai a saka cookies cutter a yayyanka zuwa shape kala-kala
- A gasa cikin abun gashi na minti 15 sai a fito dashi
Domin koyan Yadda Ake Kek Ɗin Gyaɗa (Groundnut Cake) danna nan