Cabbage sauce miya ce wadda ake yinta da kabeji da jajjagen kayan miya, tana da daɗi da lafiya a jiki musamman ma idan aka kula da tsabtace da kayan girkin.
Abubuwan da ake buƙata
- Cabbage
- Green pepper
- Peas
- Green beans
- Taruhu
- Tattasai
- Seasoning
- Gishiri
- Man gyaɗa
Yadda ake haɗawa
- Farko za a yi granding din taruhu da tattasai da albasa a yanka lawashi a ajiye a gefe.
- A yanka cabbage da green pepper su ma, a ajiye su gefe.
- Sannan a zuba man gyaɗa a tukunya, idan ya yi zafi, sai a zuba albasa a juya.
- A zuba taruhu da tattasai ana juyawa.
- Sai a ɗan rufe na mintina biyu sai a wanke veggies a zuba, amma ban da cabbage da albasa su ne na ƙarshe.
- A juya, a sa seasoning a sake rufewa.
- Za a buɗe idan ya dahu, sai a zuba cabbage da albasa.
Ita wannan sauce ana ci da abubuwa da yawa, tun daga farar shinkafa, da chapati, Fateera, har ma su jollof rice.
Domin sanin Yadda Ake Moi-moi danna nan