Yadda Za Ki Yi Wa Namiji Mai Shiru-shiru

0
2799

Wani Namijin halitta ce shiru-shirunsa. Ba damar canja shi. Ba zai miki hira ba, kuma ba zai saurari hirarki ba.

Sai ki yi nazari ki fahimci ke kadaice ba yawa hira? Ko ke kaɗai ce bai damu da ya saurara ba?
Idan a ko’ina ma haka yake, ba ya son magana. Sai ki yi haƙuri. Rashin miki hira ba zai hana ki samun rahamar Allah ba.
Sai ki daina kallo da damun kanki a kan hirarsa.
Ki mayar da hankalinki a kan sauran halayensa na kirki. Abubuwa da yawa waɗanda wasu matan da yawa ba su samu ba. Ke kina samu , Kuma ki gode wa Allah .

IDAN MIJINKI MAI MAGANA NE.

Idan mai magana ne, ke ce kaɗai ba ya son yi da ke?

Na farko ki koma ga Allah wajen yawaita istigfari.
Na biyu ki yi ta nacin addu’a .Tashi ƙiyamul layl a kan Allah ya warware miki matsalarki.
Na uku: ki yi tunani daga wajenki za a samu gyaran ko kuma daga wajensa ne?
Wato ko ba ki fahimci irin hirar da ya fi so ba?
Ki yi nazarin rayuwarsa. Misali :
Mai son labarai: Kullum yana karanta jarida. sai ki rinƙa karanta jaridu, da sauraron labarai a radiyo.
Idan kun zauna, sai ki fara ba shi sabbin labaran wannan rana .
Mai kiwon kaji ne, sai ki karanci ire-iren kaji  da abincinsu, da magungunansu.
Ɗan Kwallo: Sai kin karanci ƙungiyoyin ball. Da labaran ‘yan ƙwallo da suke tashe a yanzu.
A ƙarshe dai yana da muhimmanci mace ta karanci irin sana’ar mijinta. Da mafi yawan abubuwa da suka shafi mijinta. Hatta labarin rayuwarsa . Zai taimaka sosai wajen rage yawaita matsaloli.
Wallahu A’alam .

Domin karanta yadda ake da mai gida lokacin al’ada ko yadda ake shagwaɓa mai gida lokacin hutu

labarin da ya wuceYadda Ake Boga (Burger)
Labarin na GabaYadda Ake Biredin Kwakwa (coconut Bread Rolls)
Amin Yusuf Gwamna
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.