Ga ta nan, ga ta nanku.
A can wata ’yar unguwa da ke dab da wani tsauni, an yi wasu’yan biyu, Awa da Dawi. Tun suna yara mahaifiyarsu ta rasu, suka ci gaba da taimakon juna. To, amma shi Dawi hatsabibin yaro ne, kuma duk sanda ’yar’uwarsa Awa ta dafa abinci, sai ya cinye. Kullum ana haka har ta kai sai da ta tona rami domin ta riƙa ɓoye rabonta na abincin a ciki, amma sai ya tono ya cinye.
Wata rana Dawi ya ce da Awa: “Ni fa na gaji da zaman garin nan. Ina so ki goya ni mu yi ƙaura mu je mu zauna a wani gari inda za mu sami kwanciyar rai.” Bayan Awa ta yi ɗan tunani, sai ta amince, ta goya shi, kuma ta ɗauki ’yan tarkarcensu a ka, suka kama hanya.
Suna cikin tafiya sai Awa ta ce: “Na ga inda za mu tafi yana da nisa kuma ga shi ina jin yunwa.” Can sai Dawi ya hango wani ɗaki a gefen hanya, ya ce su shiga ciki. Da suka shiga, sai suka tarar da abinci a ciki. Dawi ya ce: “To ga shi Ubangiji ya ji kukanmu, ai sai mu ci.”
Ba da wata-wata ba sai Awa ta yarda. Suka cinye abincin nan duka, duk da yake ba su san mai shi ba. Suka sha ruwa, suka sake kama hanya. Suna tafiya har suka isa wani
gari. Dawi ya ce: “Albishirinki, ni fa ina da wata dabara.” Awa ta ce: “Kawo ta mu gani.” Sai kawai Dawi ya tara yaran garin nan ya ce shi fa ɗan dabo ne, kuma zai yi wasanni iri-iri domin ya ɗebe musu kewa.
Daga nan sai ya ce a kawo turmi, domin ya yi musu wasan daka mutum irin yadda ake yi a garinsu. Dawi ya fara shiga turmi, yara suka daka shi, kuma ya fito jiki lafiya lau. Wani daga cikin yaran ma ya shiga, aka daka shi, amma sai ya fito da jikinsa jina-jina. Da yaran suka ga haka, sai wasu daga cikinsu suka tsere.
Sauran da suka tsaya kuwa, sai suka riƙa shiga turmi ɗaya bayan ɗaya ana laƙada su, suna fita jiki a kumbure. Da mutanen garin suka ga abin da yake faruwa da yaransu, haushi ya kama su, suka yi ca a kan Awa da Dawi. Dawi ya ce da su: “Don Allah ku dakata.
Idan kun yi haƙuri, za ku ga abin mamaki.” Mutanen suka tsaya, suna jira su ga abin da Dawi zai yi. Sai ya yi wani irin siddabaru na hatsabiban yara, nan take duk yaran da aka yi wa rauni a turmi suka warke sarai. Mamaki ya kama jama’a, suka ce sai shi da Awa su zauna a garin nan tun da suna da abin mamaki da asiri haka.
Suka yarda. Suka zauna a garin. Dawi da Awa suka girma, ya zama sadaukin matashi. Awa kuma ta zama kyakkyawar mace, son kowa. Dawi ya kama noma da farauta. Ya tara dukiya mai yawa kamar ba maraya ba. Ita kuma ta zauna da shi suna cin duniyarsu.
Mutanen gari suka yi wa Dawi laƙani: “Dawi Mai Turmi.” Shi kuma yakan ce: “In da mai son mu daka shi ya zo.” Duk sanda ya faɗi haka sai a bushe da dariya, labarinsa ya bazu a duniya. Shi yasa ma kuke jin duriyarsa a taskar tatsuniyoyi. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Maza irin gujiya ne, sai an fasa akan san na ƙwarai.
- Tausasa wa ɗan’uwa shi ma wani jari ne.
- Kar a yi saurin yanke hukunci ga abin da ba a san haƙiƙaninsa ba.
- Arziƙi a ƙafa yake.
- Motsi ya fi zama
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Zinari A Bakin Kwano
Edita@rumasau-kallamu









