Ga ta nan ga ta nan ku.
Wata rana, an yi wani mutum wanda ya ke da ‘ya’ya goma. Shi kuwa maharbi ne. Kullum ya je daji yawon harbi sai ya kamo tsuntsu guda ɗaya. Shi ke nan kullum ya kamo tsuntsun sai ɗansa Na-Goma ya gasa shi ya cinye shi kaɗai. Kullum haka, kullum haka.
Ran nan sai ubansu ya ce a tafi kogin rantsuwa a yi rantsuwa a ga wanda ya ke cinye tsuntsun da ya ke kamowa kullum. Shi ke nan. Sai suka ce, ‘To.’ Suka bi shi zuwa kogi. Da suka je kogin, sai na farkon, watau Na-Ɗaya, ya shiga ya ce:
Ni Na-Ɗaya, na ɗayan Babaye.
In ni na ci tsuntsun Babaye,
Ruwa tafi da ni kar ka dawo da ni.
Sai ruwa ya ƙi tafiya da shi. Sai ya fito. Na-Biyu kuma ya shiga ya ce:
Ni Na-Biyu, na biyun babaye.
In ni na ci tsuntsun babaye,
Ruwa tafi da ni kar ka dawo da ni.”
Sai ruwa ya ki tafiya da shi shi ma, ya fito. Duk sauran suka yi ba su nutse ba har aka zo kan Na-Goma wanda ya ce:
Ni Na-Goma, na goman babaye.
In ni na ci tsuntsun babaye,
Ruwa tafi da ni kar ka dawo da ni.”
Shi ke nan. Sai kuwa ruwa ya tafi da Na-Goma.
Sai ‘yan uwansa suka ce, “To, baba, ka ga wanda ya ke cinye maka tsuntsu.” Uban kuma ya ce, “Na gani. Ku mu tafi gida. Da suka je gida, suka shaida wa uwarsu wannan labari, sai ta fashe da kuka. Ta yi kukanta ta gaji ta share hawaye ta ce, ‘Ba kome. Allah ya ji kansa.’
Shi ke nan. Ruwa yana cikin tafiya da Na-Goma, sai ya zo gaɓar kogi. A nan ne fa ya ga wata dodonniya tana ta cin kwaɗi. Sai ta kama shi ta ce, ‘Kai yaro mutum ne, ko dodo irina?’ Sai yaro ya ce, ‘Ni mutum ne. ‘Sai ta ce, ‘Kai kuwa me ya kawo ka nan? Sai ya ce, ‘Abin da ya sa na zo nan, shi ne, kullum kullum ubana ya kamo tsuntsu ya kawo gida, sai in ɗauka in gasa in cinye ni kaɗai, ba wanda ya sani.
Shi ke nan, sai ran nan ya gaji ya ce mu je kogin rantsuwa tare da ‘yan uwana a gwada a ga wanda ya ke cinye tsuntsun da baba ya ke kamowa. Da muka je muka yi rantsuwar, shi ne kogin ya cinye ni ya kawo ni nan. ‘Sai ta ce, ‘To, yanzu ka ga ni dodonniya ce. In cinye ka ko in ƙyale ka?’
Sai ya ce, ‘Ni dai ina so ki yi mini arziƙi in zama ɗanki. ‘Shi ke nan, sai ta ce, ‘To, tashi mu tafi gida. Sai suka tafi gida. Da suka isa gidan, sai ta soma yi masa abubuwa yana sayarwa. Tana yi masa ƙosai yana talla. Kullum haka har yaro ya girma. Sai ta sai masa doki da kayan doki yana hawa yana tallan ƙosai a kai.
In lokacin cin abinci ya yi, sai ta samo masa irin nasa na mutane. Ita kuma ta samo irin nasu na dodonni. Shi ke nan. Kullum haka, kullum haka, sai rannan ‘yan’uwan Na-Goma suka gan shi yana tallan ƙosai a kan doki. Suka ce, ‘Wannan kamar Na-Goma,’ a zuciyar su. Shi ma kuma ya shaida su. Sai suka ce, ‘Kai mai ƙosai!’
Sai ya waigo. Suka ce, ‘Ko kai ne Na-Goma? Sai ya ce, ‘I. Ni ne. ‘Sai suka rungume juna suna ta kuka. Shi ke nan, sai suka ce, ‘To, mu tafi gidan da ka ke. ‘Sai ya ce, ‘To, ai ni babata dodonniya ce. ‘Sai suka ce, ‘Mu tafi haka. Ba kome.’
Sai suka je suka yi sallama. Suka gaisa da dodonniya, suka ce ‘Mun zo ne mu tafi da ɗan’uwanmu Na-Goma.’
Sai ta ce, ‘Ni ba zan ba ku shi ba.’
Sai suka ce, ‘Ki yi haƙuri ki ba mu shi.’
Sai ta ce, ‘To, ku gaya min dalilin da ya sa ya zo ya same ni a nan.’
Sai suka gaya mata kamar yadda Na-Goma ya gaya mata, tun farkon haɗuwarsu a bakin kogi. Sai ta ce, ‘To na ji. Amma yanzu sai ku je ku kawo duk irin abin da za ku iya na dangin abincina. ‘Sai suka ce, ‘To.’ Suka tafi gida suka ce wa babansu, ‘Baba, yau dai mun ga Na-Goma yana tallan ƙosai a kan doki.’
Sai babansu ya ce, ‘Kai ku tafi can masu ƙarya, wanda ruwa ya cinye ina za ku gan shi? ‘Sai suka ce, ‘Ai gaskiya mu ke faɗa. Har ma wadda ta ke riƙonsa ta ce sai mun kai mata kayan abinci, sannan za ta ba mu shi. ‘Shi ke nan sai uban ya ce, ‘To a kai mata taikin gero ɗari da gomiya bakwai.
Taikin dawa ɗari da gomiya bakwai. Taikin shinkafa ɗari da gomiya bakwai. Kai da duk dai irin abincin da mutane su ke ci a yi mata ɗari da gomiya bakwai-bakwai.’Da aka kai mata, sai ta ce:
Ba cina ba, Na-Goma Ba cina ba.
Je ka ka dawo, Na-Goma Je ka ka dawo.
Shi ke nan sai suka koma suka ce, ‘Baba, ta ƙi karɓa. Ta ce ba ta cin irin wannan abincin. ‘Sai ya sa aka yi mata taikin ƙuda ɗari da gomiya bakwai. Taikin tsutsa ɗari da gomiya bakwai. Taikin kyankyaso ɗari da gomiya bakwai. Haka kuma taikin su gwano, da na tururuwa, da kiyashi, da jaba, da gafiya, da ɓera, da ƙadangare ɗari da gomiya bakwai-bakwai.
Sai aka kai mata su. Da ta ga wannan gara zango-zango, tsibi-tsibi na irin abincinta, sai ta ce:
Ga cinan nan, Na-Goma,
Ga cinan nan.
Ga shanu nan, Na-Goma,
Ga shanu nan.
Madalladai, Na-Goma,
Madalladai.
Dau wandonka, Na-Goma,
Dau wandonka.
Sa rigarka, Na-Goma,
Sa rigarka.
Sa hularka, Na-Goma,
Sa hularka.
Hau dokinka, Na-Goma,
Hau dokinka.
Sai wata rana, Na-Goma.
Sai wata rana.
Sai wata rana, Na-Goma,
Sai ka dawo.
Shi ke nan, sai suka rabu, dodanniya tana kuka, Na-Goma yana kuka. Aka kai Na-Goma gida, ya yi zamansa. Bai sake cinye wa babansa tsuntsu ba. Shi ke nan.
Kurunƙus kan ɗan ɓera. Ba don Gizo ba da nai ƙarya. Ba don ƙarya ƙarya ce ba, wa zai ci tuntuɓe da tuwon shinkafa, ya dauje baki da tsokar nama, ya faɗa rijiyar zuma, a ciro shi da nakiya da alkaki?
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafi mai taken TATSUNIYOYI DA WASANNI wadda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa
Danna nan don karanta Tatsuniya Mai Taken Marainiya









