Ga ta nan, ga ta nanku.
A can cikin wani ƙungurmin daji akwai wata Zomanya mai ciki, wadda gidanta yake kusa da na wata Kura, ita ma mai juna biyu. Suna zaman lafiya da junansu irin na maƙwabta. Wata rana sai Zomanyar nan ta je wurin Kura ta ce mata: “Kin ga ni da ke mun kusa haihuwa, ya kamata mu nemi wurin da za mu rinƙa ɓoye ‘ya’yanmu.
“Sai Kura tace: “E, gaskiya ne, to amma bari mu tona rami babba domin mu saka ‘ya’yanmu a ciki.” Da suka tona rami sai suka zauna tare, har lokacin haihuwarsu ya yi. Da suka haihu, sai suka tara ‘ya’yansu a rami ɗaya, kuma suka yi alƙawari cewa Kura za ta rinƙa samo musu abinci, ita kuma Zomanya za ta rinƙa renon ‘ya’yansu.
Suka zauna, in Kura ta tafi neman abinci ta dawo, sai ta miƙa wa Zomanya ta ci, kuma ta raba wa ‘ya’yansu. Kullum haka. Amma ita kuwa Zomanya, in an kawo mata abinci sai ta ba ‘ya’yanta su ci, in sun ƙoshi sai ta cinye sauran, ta hana ‘ya’yan Kura. Kullum haka, kuma in Kura ta zo ta ce za ta duba lafiyar ‘ya’yanta sai Zomanya ta ce ai sun ci abinci sun ƙoshi, suna barci.
Haka suka yi ta yi, har dai wata rana Kura ta ce sai ta ga ‘ya’yanta. Da ta leƙa ramin ta jawo ‘ya’yanta sai ta ga duk sun rame. Sai ta tambayi ‘ya’yanta abin da ya same su, suka rame haka. Sai ‘ya’yan suka ce ai ba a ba su abinci, in an kawo abinci sai Zomanya ta hana su, ta bai wa ‘ya’yanta, su kuwa sai ta sa su yi barcin dole kullum.
Da jin haka sai ran Kura ya ɓaci, ta yi kuka, ta yi gumani da ƙaraji mai tsanani, ta ce tun da Zomanya ta ci amanarta, to ita da ‘ya’yanta za su cinye Zomanya da ‘ya’yanta gaba ɗaya. Ko da Zomanya ta ji abin da Kura ta faɗa, sai ta rasa abin da za ta yi, idanunta suka raina fata.
Tsoro ya kama ta. Sai ta dubi Kura ta ce: “To shi ke nan, tunda kin ce ni da ‘ya’yana mun zama nama, to ki yi haƙuri mu fito daga rami tukunna.” Zomanya ta shiga rami ta gaya wa ‘ya’yanta idan ta fita Kura ta bi ta, to su fita da gudu su yi nasu wuri. Da Kura ta sake magana, sai Zomanya ta haɗa manyan kunnuwanta biyu, ta ɗan miƙo su waje ta ce da Kura: “Don Allah ki riƙe mini takalmana kafin in fito.
“Jin haka sai ya sa ran Kura ya ɓaci, ita a tsummaninta yaya za a yi kamar Zomanya ta ce ta riƙe mata takalmanta, bayan ta zama nama a wurinta. Sai ta kama kunnuwan Zomanya da ƙarfi ta finciko su ta jefar, wai ita a nufinta takalma ne. Sai kunnuwa suka sulluɓe, Zomanya da ‘ya’yanta suka ranta a na kare.
Kamar wasa, Kura ta kasa kama ko ɗaya daga cikinsu. Da ba domin Gizo ba da na shara muku ƙarya. Ƙurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka.
- Ƙarshen maci amana jin kunya.
- Kowa ya ci zomo, ya ci gudu
Danna nan don karanta Tatsuniyar Mace Mai Ciki
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Edita@rumasau-kallamu









