WakaWakar HausaWikiHausa Waƙa Mai Taken Ɗan Achaɓa Daga Nasiru G. Ahmad - 15/01/2026 0 20 1. Salamu Alaikumu barka da yanzu, Gaishe ku nake da fatan za ku karɓa. 2. Batu zan yo da fatan za ku so shi, A kan goganku wato Ɗan Acaɓa. 3. Mutum mai taimakon jama’a a kullum, Cikin sanyi da rana har da raɓa. 4. Da yin asuba ka leƙo za ka gan shi, Da rana haka dare kwai Ɗan Acaɓa. 5. Idan tafiya ta kama za ka yi ta, Cikin sauri ka nemo Ɗan Acaɓa. 6. Wuri in ya zamo nisa da titi, Shigar sa mutum guda ne Ɗan Acaɓa. 7. Idan hanya ta zam mai “go slow” ce, Idan sauri kake ɗau Ɗan Acaɓa. 8. Shi ne zai kai ka kai gararin gabanka, Ya mai da ka idan haka nan ka zaɓa. 9. Mutum ɗaya har biyu ɗauka yake yi, Ya kai ya zube ya juyo Ɗan Acaɓa. 10. Tsananin sanyi ba ya hana ɗan acaɓa, Tsakar rana ruwan sama za ya caɓa. 11. Akan jinga da shi a biya shi mako, Ko ko a wata in ya cika sai ya karɓa. 12. Kamar yara ya kai su ga makaranta, Uba ko wuri na aiki ba shi saɓa. 13. Wannan su ne wasu daga fa’idoji, Na wannan taliki mai yin acaɓa. 14. Akwai kuma aibuka jingim gare shi, A muninsu da wari sun fi jaɓa. 15. Masifar son kuɗi Jimina kira shi, Kai ya fi makauniya nema a caɓa. 16. Bai ɗau rai nasa komai ba bare ma, Na fasinjansa goga Ɗan Acaɓa. 17. Tafiyar hauka da ganganci gare shi, Dukan runtsi ya je sai ya laɓaɓa. 18. Sanin doka ta hanya ba ruwansa, “Shiga a haka” yake yi Ɗan Acavɓa. 19. Shigarsa kwana ƙafa tai za ya harba, Siginar ya ciccire domin a kwaɓa. 20. Mota ƙarama da bas har gingimari, Ratsa su yake gaba-gaɗi mai acaɓa. 21. Burinsa kawai ya kai fasinja nasa, Ya karɓi kuɗin ya ɗau wani mai acaɓa. 22. Idan ya yi ma karo babur ya lotse, Taron dangi suke maka ‘yan acaɓa. 23. “Ɗan uwa namu ka cuta ba mu yarda, Biya za kai asara ba mu karɓa! 24. “Domin ba nasa ne ba wanga babur, “Waninsa ka mallaka shi ko acaɓa.” 25. Ɗaruwwan famfamai kullum ka samu, Biyansa balas a nan ne za a saɓa. 26. Tun kan ranar yake ta cika ya batse, Ganin ƙyashi yake yi Ɗan Acaɓa. 27. “Mutum na zaune ni ko ga ni rana, Ina nema shi ko sai dai ya karɓa! 28. “Tsananin sanyin Disamba duk a kaina, Ya ƙare ni ka yin aikin acaɓa. 29. “Wannan ɗanyen hukunci ba ni yarda, Kura a buga kuɗin gardi ya karɓa!!” 30. Da ya ɗan fara zowa sai ya noƙe, Ku ɗaura burum-burum ho Ɗan Acaɓa! 31. Ya ɗauke wuta wata har sai ya shuɗe, Bai zo da balas ba goga mai Acaɓa! 32. Idan ko an yi sa’a zai ta kai wa, Zuwa wasu ‘yan watanni ba shi saɓa. 33. Daga nan babur yakan ce ya yi tsufa, A sayar a sayo wani don yai Acaɓa. 34. Idan har ka ƙiya wani za ya nema, Ya aje ma naka sabo za ya karɓa. 35. Ka nemi sayar da shi in an taya ma, Abin ba kyau gumi za kai ta sharɓa. 36. Wannan halinsu kenan aksarinsu, Marasa kishi na zuci ‘yan a kwaɓa. 37. Amma fa akwai nagartattu cikinsu, Da ke neman halal hanyar acaɓa. 38. Tuƙin nutsuwa sanin doka ta hanya, Abin da ka ba shi duk shi za ya karɓa. 39. Ba ya wasa da kai haƙƙi na babur, Wurin mai shi amintaccen acaɓa. 40. Albarka Rabbana kan sa wa wannan, Cikin samun da zai hanyar Acaɓa. 41. Idan ka tashi neman Ɗan acaɓa, Mutum mai hankali nutsuwa ka zaɓa. 42. Guji mai karkacewa in ya zauna, Ya sa hana-salla ɗan gararin acaɓa. 43. Idonai ya rufe da baƙin gilashi, Danja ko ta tsayar shi za ya raɓa. 44. Takensu irin waɗannan “Sai ka kai shi!” “Ko ba rai!” za ya amsa Ɗan Acaɓa. 45. Muna roƙon ka Allah taimake mu, Ka sa gyara cikin sana’ar Acaɓa. 46. Gwamnati dole ta yo wani agaji kai, Domin samun rage haɗuran acaɓa. 47. Haka su ma masu babur kar su ba da, Sai ga mai nutsuwa da zai aikin Acaɓa. 48. A nan zan dakata sai an jimanku, Salamu Alaikumu har Ɗan Acaɓa. 49. Muhammadu Nasiru G. Ahmadu ne, Ya yo waƙar bayanin Ɗan Acaɓa. 50. Baiti Ashirin biyu daɗa goma kansu, Hamsin ke nan a kan sana’ar Acaɓa. Alhamdu Lillah. Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Alƙawari Kaya Edita@rumasau-kallamu