Tarihin Garin Rimin Gado

0
15

Akan yi wa garin Rimin Gado kirari da cewa “Rimin Gado garin ‘yan lalle”, silar hakan kuwa shi ne, Allah ya ba wa garin yalwa ta bishiyoyin lalle, wanda a zamanin baya ya kasance itace mai daraja wanda mutane ke rububin neman sa domin yin amfani da shi a matsayin sinadarin tsaftace jiki da magani da sauran su.

Wannan gari, a zamanin baya, ya zamo kasuwa matattarar fatake inda mutane ke niƙo gari daga mabambantan sassa domin siyen lalle da sauran hajoji. A binciken da Mallam Muhuyi Magaji Rimin Gado ya yi, ya sanya kafuwar garin Rimin Gado da kimanin shekaru 300 da suka gabata.

Kafin zamowar Rimin Gado gari, inda Rimin Gado yake a yanzu ya kasance (zango ne) wurin saukar matafiya ne masu kara-kaina tsakanin birnin Kano da biranen da ke yamma da ita misalin Sokoto.

KAFUWAR RIMIN GADO

An ce akwai wani mutum mai suna Magili, mabaraci ne, wanda ya taso daga Degel; wani ɗan ƙaramin gari da ke jamhuriyar Nijar a yau zuwa inda garin Rimin Gado yake, don haka ana iya cewa shi ne asalin kafuwar wannan gari.

Bisa al’ada ta mabarata, sukan samu gefen turbar da mutane ke shigewa su fake suna addu’a ko zikirai ko waƙoƙin nasiha ga matafiya da makamantansu, da nufin neman sadaka daga masu shigewa. Magili ya gina gadon ƙasa a inda garin Rimin Gado ya ke a yanzu, a gefen turbar da matafiya ke wucewa zuwa birnin Kano, a kan wannan gado yake zama yana bara a ko-da yaushe.

ASALIN SUNAN RIMIN GADO

An ce Magili, wanda yake zama a kan gadon da ya gina na turɓaya yana bara da rana sai kuma ya kwanta bacci idan dare ya yi, ya samo ƙwanson Rimi da ya tattara a matsayin matashin kai wanda yake ɗora kansa yayin bacci.

A kwana a tashi sai ‘ƴa’ƴan rimin da ke cikin ƙwanson ya rinƙa zuba daga gadon nasa zuwa ƙasa, har kuma aka yi sa’a tsiron bishiyar rimi ya fito a wajen wanda daga bisani ya girma ya zama bishiya gagaruma wadda ake zama don hutawa ko don gudanar da cinikayya a ƙarƙashin ta.

Daga nan ne fa aka samo sunan ‘Rimin Gado’ wajen nuni da bishiyar Rimin da ya girma a ƙarƙashin ko a kusa da gado. Sannu a hankali wannan wuri ya haɓaka ainun tare da zamowa dandalin ya-da zangon fatake masu son shiga Kano waɗanda akasarin su suke tafiya a ƙafa, ko a jakuna da sauran ababen hawan lokacin daga birane irin Alƙalawa, Sokoto da sauran su.

TURBAR KANO TA SASHEN RIMIN GADO

Wannan turba ta soma ne daga ƙofar Kabuga wadda take a yammacin kano, ta keta ta shacin Janguza, ta wuce ta Yalwan Ɗan ziyal har zuwa wannan gari na Rimin Gado. Daga nan kuma sai ta cigaba da nausawa sashen yamma har ta keta Gwarzo zuwa wasu sassan ƙasar Katsina.

Kuma kamar yadda tarihi ya nuna, ta wannan turbar ne aka rinƙa samun sadarwa a tsakanin biranin Kano da biranen da suka kafu a zamanin baya waɗanda a yanzu suke cikin jihar kanon kanta, da Katsina da Zamfara da Sokoto da Kebbi har zuwa sassan ƙasashen Mali da  Nijar. Kuma haƙiƙa, ba iya Rimin Gado ba, akwai garuruwa da dama da kafuwar su ya samu ne daga albarkar wannan turba.

Danna nan don karanta Tarihin Garin Gurin Gawa

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Danya (Molluscum Contagiosum) Take
Labarin na GabaWaƙa Mai Taken Haƙƙin Dabbobi
Sadiq Tukur Gwarzo
Sadiq Tukur Gwarzo marubuci ne mai binciken tarihi da son taskance ilimi da taimakon al'umma.