1. Muna godiya ga Rabbi sarki ubangiji,
Da ya ba mu hankali yake ba mu lafiya.
2. Salati da sallama su duma ga Musɗafa,
Da ya ƙarfafe mu kan mu nemo halaliya.
3. Batuna a yau baƙar sana’a ce zan faɗa,
Da ke damun dukkanin musulmi na duniya.
4. Sana’ar da ke zub da mutuncin mutum duka,
Ya zam ba shi ƙima a idanu ko da ɗaya.
5. Sana’ar da ke zubar da ƙimar Arewacin,
Ƙasarmu Nijeriya anai mana dariya.
6. Sana’ar da Manzonmu ya ce mu guje mata,
Don kame mutuncinmu dare har da safiya.
7. Sana’ar BARA gami da ROƘO nake nufi,
Da yara suke yi har da manya a rariya.
8. Akwai yara ƙolaye na ƙauye da ke zuwa,
Birane suna bara a kowacce nahiya.
9. Akwai masu naƙƙasa ga hannu ko ko ƙafa,
Sun ɗauke ta lasisin bara sun ƙi moriya.
10. Abin ban takaici wai bara har gidan giya,
Jagora da dare ke zuwa da makauniya.
11. Akwai masu yawo ma da katin asibiti,
Suna ƙaryar ciwo za su sai wai dawa’iya.
12. Akwai masu bin masallatai an yi haihuwa,
Gare su suna biɗar abin yin aƙiƙiya.
13. Akwai masu ƙaryar sun shigo Islamu wai,
Dangi sun kore su ba abin ci da rataya.
14. Akwai ‘yan gefen tasha suna wai kuɗinsu ne,
Na mota bai cika ba zuwa Gombe Zariya.
15. Akwai mata masu ɗiban yara raɓe-raɓe,
Suna neman na abin kalaci a rariya.
16. Ko ko wai kuɗin mota ne babu suke biɗa,
Zuwa Rijiyar Zaki ta Lemo Birgediya.
17. Kawai sai ka ga mutum ƙaƙƙarfa da lafiya,
Bara wai yake domin macewa ta zuciya.
18. Ran nan nai sayayya sai kawai ga wani mutum,
Cikin duk kamala a shigarsa ba kushiya.
19. Ya ce min “Ni ne Sharu Naira goma za ka ban,”
Na ce ban yi niyyar sadaka sai ka zagaya.
20. Da ƙarshe ake faɗan cewa ai halinsa ne,
Yana ɓata sunansu sharifai ‘yan Sidiya.
21. Abin tambaya ina dalili na yin bara,
Da roƙon mutane kullu yaumin a rariya?
22. Dalilai ba sa wuce biyu ni a nau gani,
Macewar zuci da ƙin zakkar masu dukiya.
23. Macewar zuci kan sanya ƙato ya langaɓe,
Wai shi ya naƙasta ba shi neman halaliya.
24. Macewar zuci kan sanya mata na ƙauyuka,
A birni ba ƙodago sai yawon barar tsiya.
25. Macewar zuci kan sa mutum yai zaman kawai,
Ba nema sai raraka da maula duk safiya.
26. Macewar zuci kan sa ɗan boko ba zai dako,
Ko yai leburanci sai ya zauna ba moriya.
27. Macewar zuci in tai ƙamari ke haihuwar,
Aƙidar Allah ba ku mu samu abin miya.
28. Rashin ba da zakkar dukiya yadda anka ce,
A Qur’ani shi ka sa talauci annakiya.
29. Zakka ba sai wanda an sani za a bai wa ba,
Dukkan mai buƙata na da haƙƙi na bai ɗaya.
30. Zakka in an fid da ta haƙƙin fuƙara’u ce,
Lallai ne a ba su dunƙule babu wariya.
31. Mece ce ɗari biyar? A ba shi dubu biyar,
Ko goma ya ja jari ya kauce wa shan wuya.
33. Zakka har gwala-gwalai na mata sai an fitar,
In sun kai nisabi shekara in ta dawaya.
33. Idan har ana bashe ta zakka a kan kari,
Ga wanda sun cancanta roƙo za ya sanyaya.
34. Ka ɗauki lauje ka yo ciyawa ka zam sayar,
Shi yaf fi yawon roƙo a ba ka ko a ƙiya.
35. Idan har ɓera sata an ce wai halinsa ce,
Wari ne halinta daddawa babu tankiya.
36. Ta yaya mutum ƙalau madokin kare da shi,
Zai zo ma bara ka ba shi ba yin tunaniya.
37. Roƙo bai halatta sai idan an matsu ƙwarai,
A hanzarta bar shi in buƙata ta zam biya.
38. Yaƙi da macewar zuci lallai a kanmu duk,
Bara ba sana’a ce ba roƙo haramiya.
39. A nan zan tsaya kishi Allahu ba mu shi,
Mu zam masu dogaro da kai dukka safiya.
40. Sunana Muhammad Nasiru G. ɗan Ahmadu,
Baiti Arba’in na shirya wannan ƙasidiya.
Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafi mai suna TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad ya wallafa.
Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Abokin Tafiya
Edita@rumasau-kallamu










