Ire-Iren Ayyukan Wanzamai

0
45

Cire Belun-Wuya

Belun-wuya tsokar nama ce wadda take tsirowa a cikin bakin mutum liƙe da ƙarshen dasashin sama kusa da maƙogaro.Wannan tsokar nama Hausawa sun ɗauka idan ba a cire ta ba, to idan mutum ya girma ciwo na iya kama ta. Idan kuwa ta kamu da ciwo zai sa mutum ya kasa cin abinci ko shan ruwa, ya kuma yawaita yin amai ya kuma rame. Idan kuma wani abu ya taɓa wurin, mutumin zai ji tsananin zafi. Wannan ne ya sa da an haifi jariri sai a kira wanzami domin ya cire ta (Hira da Alhaji Aliyu Sarkin Aski, a Safana, 16-6-96).

Wasu daga cikin Hausawa ba a cire wa ‘ya’yansu belin wuya, a maimakon cirewa suna amfani da maganin da zai hana su kamuwa da wani ciwo.

Ire-Iren Ayyukan da Wanzamai Kan yi a Farjin Mata

Wanzaman gargajiya suna yin wasu ayyuka a cikin farjin mata domin a yi maganin wasu lalurori da sukan iya matsa masu bayan sun yi aure. Wasu daga cikin waɗannan ayyuka ana yin su tun mata suna jarirai, wasu kuma sai sun fara girma ake gane suna fama da lalurar sai a yi masu aikin.

Akwai kuma waɗanda sai sun yi aure ne za a iya fahimtar suna da lalurin, misali wanzamai suna fahimtar yarinya mai fama da lalurar angurya tun lokacin da aka haife ta sai a cire. Amma lalurar sadadda da mahindi da sarƙa da turu duk sai in yarinya ta girma ne za a iya fahimtar su.

Domin aiwatar da wannan aikin cikin sauƙi da nasara ba tare da samun sha’awa ba wajen yin waɗannan aikace – aikace wanzaman da suke yin aikin suna shan magani, ko amfani da layu da gurayen da za su kawar masu da sha’awa a lokacin da suke yin waɗannan ayyuka. Misali,a lokacin da za a yi aikin wanzamin da zai yi aikin da wanda zai taimaka masa kan shafa farar ƙasa a dukkan gefen idanunsu, kuma su sanya ta cikin baki suna taunawa suna haɗe ruwan har sai sun gama aikin sannan sai su wanke fuskokinsu da bakunansu.

Wannan yana taimakawa ƙwarai wajen kawar da sha’awa ga shi wanzamin da mai taimaka masa. Mutane suna yaɗa jita-jita wai idan wanzami ya zo yin ire-iren waɗannan ayyuka idan azzakarinsa ya tashi, to idan ya kwanta ba zai sake tashi ba. To wannan ba gaskiya ba ne, ana amfani da maganin sha’awa domin kar ɓarna ta faru a lokacin da ake yin wannan aikin, saboda wasu mutane ba sa iya riƙe sha’awa su yi haƙuri idan ta kama su.

Cire Angurya

 Angurya wani tantanin nama ne wanda ake haihuwar mata da shi a cikin farjinsu, wasu kuma sai sun girma yake fito masu. Idan ba a cire shi ba yana iya hana mace saduwa da namiji idan ta girma. Wanzamai suna gane mata masu fama da angurya a lokacin da suka zo cire beli ko hakin-wuya. A nan ne idan budurwa ce sai su binciki farjinta su ga idan tana da angurya sai su cire shi.

Wasu wanzamai suna amfani da yatsa domin cire angurya. Suna sa babban yatsansu ne su tallabo shi daga tushensa sai su sa ‘yar tsaga su cire shi. Wasu kuma suna amfani da allura da zare domin cire shi. Ana tsiro shi da allurar ne da zaren sai a ɗaga sama a sanya askar aski a yanke shi. Wasu wanzaman kuma suna amfani da hantsaki domin cire shi, ana sanya hantsakin a kamo tushensa sai a sa askar aski a yanke shi.

Wasu kuma suna amfani da akaifar babban yatsansu su kama shi daga tushensa sai su sa askar aski su yanke shi. Bayan an cire shi sai wanzamin ya tauna ‘ya’yan bagaruwa ya furza a wurin, daga nan kuma sai ya barbaɗa maganin da zai tsayar da jini da wanda zai hana shi sake tuƙowa.

Gyara Sadadda

Mace mai lalurar sadadda ana haihuwar ta da wannan lalura, domin ana samun ƙofar farjinta ‘yar ƙarama ce wadda fitsari ne kawai yake iya fita ta wurin, amma can daga cikin farjinta lafiya lau yake. Matsalar a wurin ƙofar farjin take. Wasu kuma ana haihuwarsu lafiya lau, amma saboda rashin tsabta da rashin kula daga wurin iyayensu ko masu riƙonsu sai ƙofar ta sake toshewa.

Matan da suke da irin wannan matsala idan za su yi fitsari sai ya riƙa fita kamar na namiji. Idan iyayensu suka fahimci haka sai su sanar da wanzamin gidansu domin ya binciki yarinyar don ya gyara ta. Ana yin irin wannan gyara ne ta yadda aka fahimci matsalar.

Ga waɗanda aka haifa da matsalar, sai an sanya askar aski a ƙara buɗa ƙofar farjin, daga nan sai a barbaɗa maganin da zai tsayar da jini da wanda zai sa wurin ya yi saurin warkewa. Ga kuma waɗanda suka sami matsalar sakamakon rashin kula ko rashin tsabta, ana amfani da hannu ne a sake buɗa ƙofar, daga nan sai wanzamin ya gargaɗi iyayen yarinyar ko masu kula da ita da su riƙa tsabtace farjinta ta hanyar wanke mata a duk lokacin da ta yi fitsari ko ta tashi daga barci.

Gyara Sarƙa

Sarƙa lalura ce da ake samu a farjin mace a inda za a tarar leɓatun farjinta sun sarƙe yadda ba za ta iya ganin ƙofar farjinta ba. Irin wannan matsala ba kasafai ake samun ta ba, akan daɗe ba a sami mace mai fama da irin wannan matsala ba. Idan an sami mace da lalurar sarƙa aka kai wa wanzami domin ya gyara yana amfani da hikimar da ya gada kuma ya ƙware a kanta domin gyara ta.

Ba dukkan wanzamai ne suke iya gyara mace mai matsalar sarƙa ba, ko a cikin wanzaman gado sai waɗanda suka koya wajen tsofaffin wanzamai suke iya gyara mace mai matsalar sarƙa. Wanzamai suna gyara mace mai matsalar sarƙa ta amfani da hannuwansu su raba leɓatun farjin su kawo magani su shafa a wurin yadda kowane zai tsaya a wurin da yake ba tare da ya sake sarƙewa da ɗan uwansa ba. Wanzamin zai yi ta yin haka har sai wurin ya zauna daidai ƙofar farjin ta fito sosai.

Cire Mahindi

Mahindi shi ma wata lalura ce wadda ake samu ga farjin mata wadda ta yi kama da angurya amma suna da bambanci. Shi mahindi tsokar nama ce take tsirowa ta toshe ƙofar farjin mace ta hana ta saduwa da namiji. Wajen cire shi ana amfani da askar aski ne ko askar tsaga (‘yartsaga), a sanya akaifa a ɗago shi sama, sai a sanya askar a yanke shi.

Gyara Turu

Wata matsalar wadda wanzamai suke gyarawa a farjin mace, ita ce ta turu. Shi turu ana samun matsalar shi ga mata ƙalilan. Matan da suke da wannan ciwo idan suna saduwa da namiji azzakarin ba ya wucewa duka a cikin farjin saboda turun da yake ciki ya tare ƙofar.

Mata masu irin wannan lalura suna iya ɗaukar ciki, sai dai idan sun zo haihuwa sukan fuskanci matsalar da kan kai ga sai an yi masu yankan gishiri, wanda wani al’amari ne mai haɗari. Ita ma wannan matsalar ba dukkan wanzamai ne suka iya gyara ta ba, sai wanzamai da suka koya ga wanzamai na da can.

Wanzamai suna gyara turu ta hanyar sanya yatsunsu biyu manuni da na kusa da shi a cikin farjn mace mai wannan matsala, su kama shi da yatsun su buɗe shi yadda ba zai tokare azzakarin namiji a lokacin da ake saduwa da matar ba.

Kaciya

Kaciya tana nufin yanke ko cire fatar da ta rufe kan azzakarin mutum. A ƙasar Hausa wanzamai ne suke yin kaciya, kuma mafi yawanci an fi yin kaciya a lokacin sanyi. Dalilin da ya sa aka fi yin kaciya a lokacin sanyi shi ne, a wannan lokaci jikin mutum ya fi saurin tohuwa, don a wannan lokaci ko rauni mutum ya yi zai yi saurin warkewa.

A lokacin sanyi kuma an kai ga amfanin gona, abinci ya wadata, yaran da aka yi wa kaciya za su sami wadataccen abincin da za su ci, jikinsu ya tohu da sauri su yi saurin warkewa, kuma a wannan lokaci aiki ya yi sauƙi za a sami wanda zai tsaya ya riƙa kula da su.

A al’adar Hausawa yawanci sai yaro ya kai shekara bakwai abin da ya yi sama da haka nan za a yi masa kaciya. Hausawa ba su faye yi wa yaro kaciya yana da shekara takwas da haihuwa ba. Saboda an camfa wai idan aka yi wa yaro kaciya yana da shekara takwas, to wani bala’i na iya faɗa masa. Wannan ne ya sa idan ba a yi wa yaro kaciya yana da shekara bakwai ba, to ba za a yi masa ba, sai ya kai shekara tara ko goma.

A da idan za a yi kaciya ana tara yaran unguwa ɗaya a gida ɗaya domin yi masu kaciya, a sanya mutum ɗaya ya tsare su yana kula da su don kar su fama kaciyar. Amma a yanzu wasu suna yin haka, wasu kuwa da sun tashi yi wa ‘ya’yansu kaciya, sai su kira wanzami ya yi kaciyar ba tare da sun gaya wa kowa ba.

A ranar da za a yi wa yaran kaciya wanzamin da zai yi kaciyar tare da yaransa masu taimaka masa kan yi sammako zuwa gidan da za a yi kaciyar. A al’adar Hausawa an fi son a yi sammako domin a wannan lokaci yaran da za a yi wa kaciyar ba su farka daga barci ba.

An fi son a yi kaciyar da sun farka sun wanke idanunsu, watau ba su kai ga motsa jikinsu ya tashi ba. Wani dalili da yake sa a yi kaciya tun da sassafe shi ne, a wannan lokaci rana ba ta fito ba bare ta yi zafin da zai sa jinin yaron da za a yi wa kaciyar ya tashi, wanda zai sanya idan an zo yi masa kaciyar ya zubar da jini da yawa.

Idan za a yi wa yara kaciya ba a gaya masu ranar da za a yi don kar su sami fargaba ko su gudu su ɓuya. Haka kuma a lokacin da za a yi masu kaciya an fi son wani daga cikin ‘yan’uwansu ya riƙe su don kar su yi tsammanin cuta masu za a yi. Ana kuma ba su wani abu mai daɗi kamar alewa da makamantanta wadda za ta ƙara kwantar masu da hankali su ƙara yarda da ba cutar su za a yi ba. A lokacin da za a yi kaciyar ana rufe wa yaron da za a yi wa kaciyar idanu don kar ya ga jini na zuba daga jikinsa hankalinsa ya tashi.

A lokacin da za a yi wa yaro kaciya idan ya nuna kasala abokan wasansa da kakanninsa kan riƙa yi masa dariya, a wani lokaci sukan tambaye shi, idan ba ya son a yi masa kaciya ya ba da wani abu a ƙyale shi. A irin haka wasu kan ce sun ba dukkan dabbobin da ke gidansu da gidan duka, wasu ma kan ce sun ba da wani daga cikin ‘yan gidansu ko wani daga cikin mahaifansu.

Idan wanzami ya yi kaciya, bayan kuɗin kari waɗanda ‘yan uwa da abokan arzikin iyayen yaron da aka yi wa kaciya suka bayar, su ma iyayen yaron suna ba wanzamin tasu sallamar. Irin wannan sallama ta haɗa da kuɗi daidai arzikin iyayen yaron, bayan kuɗi ana kuma ba da damen dawa da zakara domin wanzamin ya sami hatsin da za a riƙa yi ma abinci ba tare da ya sha wahalar neman abinci ba.

Shi kuwa zakara da ake bayarwa ana ba da shi wai ladar jinin da ya fitar a jikin ɗan kaciyar. A da can idan aka yi wa yaro kaciya ya zama dole a ba wanzamin damen dawa da zakara, amma a halin yanzu saboda juyawar zamani wannan al’adar ta fara ƙaura, wurare kaɗan ne ake bayarwa. A maimakon su ana ba da kuɗi gwargwadon arzikin iyayen yaron da aka yi wa kaciyar.

Bayan waɗannan kuma a da can kayan da suke jikin yaron da za a yi wa kaciya idan an tuɓe su, bayan wanzamin ya gama kaciyar, sai ya ɗauke su ya kai wa ‘ya’yansa.

Kaciyar sa-Wandonka

Wannan kaciya ƙarin hikima ce da wanzamai suka samu a gargajiyance, wadda ake yi wa yaro kaciya da an gama ya sanya wandonsa ya yi tafiyarsa ya ci gaba da yin harkokinsa na yau da kullum. A irin wannan kaciya ba a tsare yaro domin yin jinya kamar yadda ake yi kafin zuwan wannan hikima. A taƙaice a iya cewa kaciyar sa-wandonka ci gaba ne wasu wanzamai suka samu a gargajiyance.

Ita wannan kaciya babu wani bambanci wajen yin ta da irin kaciyar da wanzamai suke yi, wurin da bambancin yake shi ne wajen sanya magani. A wannan kaciya ba a tauna bagaruwa a furza ruwan, a maimakonta ana shafa ruwan magani mai mai, sai kuma a naɗe kaciyar da wani farin ƙyalle kamar yadda ake yi wa kaciyar asibiti.  Wannan farin ƙyalle da ake naɗawa ba zai fita ba sai a lokacin da kaciyar ta warke.

Karanta Yadda Askin Sarauta Yake

Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA

MAYU 2009/JUMADA ULA 1430

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Askin Sarauta Yake
Labarin na GabaYadda Wanzamai Suke Tsaga
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.