Akwai matan da suke fahimtar cewa ba su kawowa a lokacin jima’i, wanda ake kira “anorgasmia” a likitance. Domin fahimtar wannan yanayin da kuma tasirinsa, ya kamata mu san menene ake nufi da kawowa a lokacin jima’i, wanda ake kira “ejaculation” ko “releasing” a turance.
Kawowa shi ne fitar da ruwan maniyyi. Ba dole ba ne ma’aurata su kawo a lokacin jima’i. Sai dai kawowar tana da matuƙar muhimmanci.
Ga namiji, kawowa tana nuna kai wa ƙololuwar gamsuwarsa da jima’i, sa’annan dole sai ya yi ta sa’annan zai iya yi wa mace ciki, domin ƙwayoyin halittar haihuwarsa (sperm cells) suna a cikin ruwan kawowar ne. Ga mace kuwa, ita ma kawowa tana nuna matuƙar gamsuwarta da jima’i ne, amma ruwan kawowar ta baya ɗauke da ƙwayoyin halittar haihuwarta (ova).
A kimiyyance, daga lokacin da mace ta balaga zuwa lokacin da al’adarta za ta ɗauke saboda nisan shekaru (menopause), tana samar da ƙwayoyin halittar haihuwarta (ova) kimanin 300,000 zuwa 400,000 waɗanda ba su ƙosa ba (underdeveloped ova).
Wasu daga cikinsu ne za su ƙosa, kuma za ta riƙa fitar da su a duk bayan lokacin da ta gama al’adarta (ovulation) da kwanaki 13, 14, 15, ko 16. Kafin ɗaukewar al’adarta, za ta yi ovulation kimanin 300 zuwa 400, su kuma sauran ƙwayoyin ova ɗin da ba ta saka su ba, za su narke su bi jikinta, kuma shi ne ake kira “follicular atresia”.
Abinda nake so in nuna a nan shi ne, ba dole ba ne a duk lokacin da namiji yake jima’i da mace ya zamo sai ta kawo, kuma rashin kawowarta ba zai hana ta samun juna biyu ba. Amma rashin kawowar mijinta zai iya hana ta samun juna biyu. Wani lokacin mace za ta iya kawowa amma ita ba za ta gane ba, sai dai mijinta ya gane. Dalilan da za su iya sanya hakan su ne:
1. Bambance-bambancen halitta (anatomical differences): Wasu mata ba su jin fitar ruwan saduwar aure daga gabansu saboda bambance-bambancen halittar jijiyoyin lakarsu (nerve endings) ko kuma yadda jikinsu yake sarrafa jin daɗi yayin jima’i.
2. Tunanin zuciya (psychological factors): Tashin hankali (anxiety), damuwa (stress), ko rashin mayar da hankali ga yadda ake jin daɗi a lokacin jima’i yana iya rage fahimtar fitar da ruwa ko samun inzali ga mace.
3. Raguwar jin daɗi (reduction of sensitivity): Canje-canjen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikinta, kamar lokacin da ta haihu, ko lokacin da take shayarwa, ko lokacin da shekarunta suka yi nisa, duk suna iya shafar jin daɗin jima’i kuma ya haifar mata da raguwar jin abubuwa a jikinta.
4. Rashin fahimtar fitar da ruwan kawowa (misunderstanding of female ejaculation): Yawancin lokaci mata sukan rikice su kasa bambanta fitar ruwan santsi (vaginal lubricants) da kuma fitar ruwan kawowa (ejaculate). Hakan zai iya sanyawa mace ta ga kamar ba ta kawowa, alhalin kuwa tana yi.
Magani da Shawarwari:
1. Tattaunawa: Akwai buƙatar mace ta riƙa tattaunawa tsakaninta da maigidanta don su fahimci juna da yadda jikin kowannen su yake amsawa yayin jima’i.
2. Mayar da hankali a lokacin jima’i: mace ta riƙa nutsuwa yayin jima’i tare da mayar da hankalinta a kan yadda take jin abubuwa a jikinta, ma’ana ta daina tunanin wasu abubuwa can daban. Hakan zai iya taimakawa wajen fahimtar jikinta sosai.
3. Yin atisayen ƙarfafa tsokokin mara: Yin atisaye kamar Kegel yana iya ƙarfafa tsokokin mararta da inganta jin daɗin gabanta.
A yawancin lokuta, wannan ba wata matsalar lafiya ba ce, sai dai bambancin yadda mace ke jin daɗin jima’i. Amma idan akwai damuwa, to, a je asibiti domin ganin likitan mata (gynecologist) domin ayi bincike a tabbatar da abinda yake faruwa.
Domin karanta Ciwon Hanta (Hepatitis) 2 danna nan
Edita@rumasau-kallamu