Cutar Maƙoƙo

0
35

Maƙoƙo shi ne ake kira “goiter” ko “thyromegaly” a likitance. Maƙoƙo wani kumburi ne a cikin jakar sinadarin din thyroid (thyroid gland inflammation) wanda yake kasancewa a ƙasan wuya. Ba lallai ba ne maƙoƙo ya zamo ciwon daji, amma yana iya zamowa alamar matsalar jakar sinadarin thyroid.

Abubuwan da suke iya haifar da maƙoƙo su ne:

1. Ƙarancin sinadarin iodin a cikin jiki (iodine deficiency): Wannan shi ne mafi yawan dalilin samuwar maƙoƙo a faɗin duniya. Iodin yana da matuƙar muhimmanci wajen samar da sinadarin iodine na thyroid, kuma rashin shi zai iya sanya jakar thyroid ta kumbura don ƙoƙarin cike wannan giɓin.

2. Graves’ Disease: Wannan cuta ce ta garkuwar jiki (autoimmune disorders) wacce take sanya jakar thyroid ta samar da sinadarin iodine fiye da kima (hyperthyroidism), kuma hakan yana haifar da kumburin maƙoƙo.

3. Hashimoto’s Thyroiditis: Wannan ita ma wata cuta ce ta garkuwar jiki (autoimmune disorder) inda garkuwar jiki take kai hari ga jakar sinadarin thyroid, kuma hakan yana sanya ta kasa samar da sinadarin iodine yadda ake buƙata (hypothyroidism). Wannan yana iya haifar da kumburin maƙoƙo.

4. Tsirowar Kari a Cikin Jakar Thyroid (Thyroid Nodules): Wannan wani kumburi ko ƙurji ne da yake fitowa a cikin jakar sinadarin thyroid, wanda yake haifar da kumburin maƙoƙo.

5. Ciwon Daji na Thyroid (Thyroid Cancer): Ko da yake ba ya faruwa sosai, amma ciwon cancer yana iya haifar da kumburin jakar thyroid idan ya shafi tsarin halittar jakar.

6. Juna Biyu (Pregnancy): Canje-canjen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone da sauransu, yayin da mace ta ɗauki ciki, yana iya haifar mata da kumburin maƙoƙo na wucin-gadi (temporary goiter) saboda jikinta yana buƙatar ƙaruwar sinadarin thyroid.

7. Kumburi (Inflammation): kumburin jakar sinadarin thyroid (thyroiditis) yana iya haifar da kumburin maƙoƙo.

Za a iya magance kumburin maƙoƙo ta hanyoyi kamar haka:

1. Ƙarin Iodin (Iodine Supplementation): Idan ya samo asali ne daga rashin isasshen iodin a cikin jiki, to, ƙara yawan cin abincin da yake ɗauke da iodin ko shan magungunan ƙarin iodin yana iya rage kumburin.

2. Yin Amfani Da Magunguna (Medications): Idan maƙoƙo ya samo asali ne daga ƙarancin sinadarin thyroid (hypothyroidism), to, shan maganin ƙarin sinadarin thyroid, kamar levothyroxine zai iya rage kumburin. Idan kuwa maƙoƙon ya samo asali ne daga yawan sinadarin thyroid fiye da kima a cikin jiki (hyperthyroidism), to, shan magungunan da ke rage yawan sinadarin thyroid ɗin (antithyroid medications) zai iya rage kumburin.

3. Magance Maƙoƙo ta Hanyar Hasken Radiation (Iodine Radioactive Therapy: Ana amfani da wannan dabarar ta hasken radiation don rage girman jakar thyroid ɗin a lokutan hyperthyroidism.

4. Aikin Tiyata (Surgery): A wasu lokutan, idan maƙoƙo ya yi girma sosai har ya kai yana kawo matsala wajen numfashi ko haɗiyar abinci, ko kuma idan ana zargin ciwon daji ne ya haddasa shi, to, ana iya cire wani ɓangare ko dukkan jakar sinadarin thyroid ɗin (thyroidectomy).

5. Kulawa Ta Akai-Akai (Regular Observation): Idan maƙoƙon ba ya haifar da wata matsala, to, likita yana iya bayar da shawarar a cigaba da lura da yanayinsa ba tare da yin magani nan-take ba.

A taƙaice, in mutum yana ɗauke da maƙoƙo ko alamunsa ya kamata a je asibiti domin a yi bincike a tabbatar da abinda ya haddasa wannan maƙoƙon, sannan a ɗauki matakin da ya dace.

Domin karanta Cutar Damuwa danna nan
Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceCutar Damuwa (Depession)
Labarin na GabaYadda Za Ki Yi Funkaso