Kamannin Jariri

0
50

Sakamakon binciken kimiyya na asibiti bai tabbatar da cewa idan namiji ya riga mace yin inzali, ko kuma idan mace ta riga namiji fitar da ruwan saduwa, to, jaririn da suka haifa zai yi kamannin jiki irin na wanda ya riga kawowa ba.

Abin da ilimin kimiyya na likitanci ya tabbatar shi ne gadon kamanni yana da alaƙa ne da ƙwayoyin halittar gado waɗanda ake kira “genes”. Duk lokacin da ma’aurata suka sadu kuma har juna biyu ya shiga, to kowanne daga cikin ma’auratan zai bai wa jaririn ƙwayoyin halittar gado guda biyu.

Waɗannan ƙwayoyin halittar gadon ne suke ɗauke da umarnin yadda nau’in halittar jikin jaririn za ta kasance ta ɓangaren fuskarsa, launin idonsa, gashin jikinsa, launin jikinsa, muryarsa, tsawon jikinsa, da sauransu. To, amma akan samu wasu ƙwayoyin halittar gadon su zamo sun fi wasu karfi.

Don haka, idan ƙwayoyin halittar gadon da namiji ya bai wa jaririn sun fi na macen ƙarfi, to, jaririn zai yi kama da mahaifinsa. Idan kuwa ƙwayoyin halittar gadon da mace ta bai wa jaririn sun fi na namijin karfi, to, jaririn zai yi kama da mahaifiyarsa.

In kuma ƙarfinsu daidai da juna ne, to, zai ɗebo kamannin jikin mahaifinsa, ta wani ɓangaren, sa’annan ya ɗebo kamannin jikin mahaifiyarsa, ta ɗaya ɓangaren. Kuma ba saurin kawowa ne yake sanya ƙwayoyin halittar gadon miji su fi na mace ƙarfi ko na mace su fi na namiji ƙarfi ba. A a, wannan tsarin Allah SWT ne.

Game da cewa ko akwai wani yanayin kwanciyar jima’i wacce take zaburar da samun juna biyu? Amsa ita ce babu wata kwanciyar da sakamakon binciken kimiyya na asibiti ya tabbatar da cewa lallai idan aka yi ta a lokacin jima’i, to, za a iya samun ciki.

Sai dai, ana tsammanin cewa kwanciyar jima’i wacce namiji zai hau kan mace, alhalin ita kuma tana kwance a kan gadon bayanta (missionary style), ko kuma akasin shi wanda namiji zai kwanta akan gadon bayansa ita kuma mace tana samansa (cowgirl style), sun fi bayar da damar shiga can ciki (deeper penetration) afwan .

Ita kuwa shigar can ciki za ta iya sanya ruwan maniyyin namiji ya shiga kusa da bakin mahaifa (cervix), kuma hakan zai taimaka wajen haɗuwar ‘ya’yan maniyyin namiji da ƙwan haihuwar mace, domin samun sauƙin ƙyanƙyashe ƙwan haihuwar.

Amma ƙa’idar da ya kamata mu fahimta, ita ce cewa samun juna biyu ya danganta ne da saka ƙwan haihuwa (ovulation), lafiyar halittun haihuwar mace (female’s reproductive organs health), ingancin ‘ya’yan maniyyin namiji (sperm cells health), isasshen ruwan maniyyi (adequate sperm count), da kuma uwa-uba yin jima’i a daidai lokacin da mace take yin ovulation (timed intercourse).

Members kuyi hakuri fa, karatun ne wani lokacin yana da ‘yar wahala.

Danna nan don karanta Zinariyar Awa Ga Jariran Mu

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceWasu Daga Malaman Alƙur’ani A Jihar Zamfara
Labarin na GabaFassarar Huɗubar Juma’a daga Masallaci mai Alfarma 7th February 2025