Sunnonin Ranar Juma’a

0
65

Mubarak Abubakar

Ranar Juma’a, rana ce ta musamman a wurin Musulmai, rana ce babba, mafi daraja daga sauran ranakun mako. Rana ce da Allah ya zaɓa, kuma aka farlanta ibada ta sallah mai daraja a cikin ta. Rana ce da Allah SWT ya saukar da surah guda da sunanta.

Saboda muhimmancin ranar, akwai wasu ɗabi’u da halaye da ladubba da ake so musulmai su riƙa aikatawa a kowacce ranar Juma’a.

1. Yin wanka
2. Sanya Turare
3. Sanya tufafi masu kyau
4. Yin asuwaki
5. Neman dacewa da lokacin amsar addu’a
6. Karanta Suratul Kahf
7. Tafiya masallaci da wuri.
8. Yawaita salati ga Annabi S.A.W.

Allah ya ba mu albarkar ranar Juma’a.

Danna nan don karanta Shakku a Cikin Sallah

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

 

labarin da ya wuceGudunmawar Mawadata Da Ɗaiɗaikun Jama’a Ga Tsangayu
Labarin na GabaMa’anar Alphanci da Simpanchi