Abu ne mai matuƙar mahimmanci akan kowane mutum ya iya sarrafa tasarrafin ragamar kwamfuta (na’ura mai ƙwaƙwalwa) ta hanyoyi da dama, domin yin ninƙaya a cikin ko ina a duniya ta hanyar karatu ko kasuwanci ko sadarwa. Haka kuma kwamfuta ana iya amfani da ita wajen ganin yadda ran mutum yake fita da sauran su.
Kwamfuta na da amfani da yawa tun daga yara ƙanana har zuwa manya. Kowace masana’anta na buƙatar kwamfuta, don gudanar da ayyukanta cikin sauƙi. Yin amfani da kwamfuta mai inganci zai haifar da ci gaban duniya baki ɗaya. Kwamfuta na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da mutum ya ƙirƙira.
Sannan kuma ba zai yiwu ba ga mutum ya yi hasashen yanayi ba tare da amfani da kwamfuta ba. Na’urorin kwamfutoci suna sauƙaƙa ayyuka da dama, saboda suna iya sarrafa bayanai da yin wasu ƙididdiga waɗanda za su ba da sakamakon abin da ake buƙata.
Kwamfuta tana amfani ta ɓangaren sadarwa ko shigar da bayanai ta ɓangarorin daban-daban, tana ba da manya da ƙanana harkar kasuwanci tare da kayan aikin da ake buƙata, don dai-daita mahimman ayyuka kamar ajiyar kuɗi da ƙirƙirar takardu. Har ila yau, su ne maɓalli a cikin masana’antar tallace-tallace, inda suke taimakawa wajen sarrafa kaya daga shigarwa zuwa fitar su.
Don karanta me ake yi da kwamfuta danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu