Maganar gaskiya ana sanyi yau garin
Tin a daren jiya na san yau za ai abin
Iska ce kamar da rani ta game garin.
Daga jin fil-fifil na iska sai tausayin
Kaina Auwalan ya zo mini tin Ajiyan
Dan na san abin da zai faru da ni kurin.
Yo ɗakin da anka ba ni gida dukkanin
Bango nai ina zaton sanyi nan yakan
Zauna yai watanda kafin ya game garin.
Ga tagarsa babu ƙofa sai labulan
Da idan nai fishi aradu ina cinye ɗan
Malafar uba da bai kare sanyi ko kaɗan.
Ga ƙofarsa ba ta rufuwa gam wai dukan
Wanda ya ce fa zai rufe ta rubuk sai idan
Zai ƙarawa kansa caji na rabin galon.
Da ma can samansa lau ne to da da ɗan
sauƙi dan kwa na yi imani zai ragen
Sanyi tinda ai rufi da silin ba sa barin.
To fauƙas-samawatin ma tin jiyan
Na ji ta fara ba ni saƙon kar nai jiran
Sai wani ya yi min bayani kan nai iyon.
Ga bargon da ke yi min hidima ya yi min
Ƙanƙanta dan kwa ƙwabrina ko kaɗan
Bai samun shiga cikin halara ko kaɗan.
In na sanya kai ƙafata ita ke wajen
In kwa na sa ƙafar fa to kaina sai ya zan
Ya bullo ta ɓangaren titin shonekan.
An ce ba ku jin dukan sanyi wai hakan?
Tattabaru da ku nake magana kun yi jim!
Ko dan na mu lokacin muma is kwamin.
Allah ga su Abba Yusuf nan na biɗan
Canjin rayuwa da Bargo Ɗanlibiyan
Da idan na shige ciki bai mai takuran.
Danna nan don karanta waƙar halin da muke ciki
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu