Muhimman Abubuwan Da Suke Inganta Lafiya

0
99
  1. Ganyayyaki da kayan marmari na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suke inganta lafiyar jiki.
  2. Kwanciyar hankali babban jigo ne game da kyautatuwar lafiya da ingantar ta. 
  3. Motsa jiki a kai a kai, shi ma muhimmi ne game da ɗorewar lafiya da ingantuwar ta. 
  4. Ƙauracewa abubuwan da suke sa damuwa da abubuwan ci ko sha da suke barazana ga lafiya, kamar giya, taba da sauransu
  5. yawaita shan ruwa don ɗaurayo tinbi da hanji, da kuma sauƙaƙa niƙuwar abubuwan da ake ci saboda waɗanda suka gama aiki su fice su bar jiki cikin sauƙi.
CUTUTTUKAN DA BA SU DA MAGANI

Cikin Suratu Yaasiin aya ta (68) Allah (Subhanahu Wata’ala) ya ce: 

Duk wanda muka tsawaita rayuwarsa, za mu tauye shi a halitta, shin ba sa hankalta ne”.

Don haka, duk wanda shekarunsa suka zarce shekarun ganiyar ƙarfi (wato shekara arba’in (40) ), to fa baya zai rinƙa yi ba gaba ba. 

An karɓo hadisi daga Usamatu ɗan Sharik Allah ya yarda da shi ya ce: “Ƙauyawa sun ce: Ya Manzon Allah! Ko ma yi magani? Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; I, ku bayin Allah ku yi magani, haƙiƙa Allah bai sanya wata cuta ba, face sai da ya sama mata waraka (da magani), sai dai ciwo ɗaya, suka ce wane ciwo ne? ya ce, “Tsufa.” Ahmad, Abu Dawud da wasun su ne suka rawaito shi. 

ALAMOMIN TSUFA

Da zarar tsufa ya cim ma mutum, alamominsa za su bayyana a tare da shi, kamar:

  1. Yanƙwanewar fata da tattarewa. 
  2. Tsanantar cututtukan gado kamar hawan jini, hawan shuga, olsa mai riƙe baya da ƙirji (basir).
  3. Raunin ƙwayoyin da ke ba wa jiki garkuwa.
  4. Ciwon gaɓoɓi. Da dai sauransu.

Saboda haka, babu wanda zai tsufa wani mai ba da magani ko likita ya ba shi maganin da zai tafiyar masa da tsufansa ko gajiyawar da ya yi.

Domin karanta Yadda Ake Zaman Jiran Liman Bayan Nafila Danna nan

Bayan haka, an karɓo Hadisi daga Abu Hurairi Allah ya yarda da shi ya ce: “Haƙiƙa ya ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa “Tabbas a habbatus sauda (baƙin algaru) akwai waraka daga kowane ciwo sai dai mutuwa.” Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. 

Wato babu wani magani da yake hana mutuwar bawa idan lokacin mutuwarsa ya yi, kuma yadda tsufa ba shi da magani, to haka ma mutuwa ba ta da  magani. 

Bayan haka, malaman Hadisi suna fuskantar da maganar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi ta cewa, akwai waraka daga kowane ciwo a tattare da habbatus-sauda cewa, wannan bayani ba Manzon Allah ya shafi cututtukan da sanyi yake sabbabawa ne, ba kowane irin ciwo ba. 

JIGA-JIGAN MAGUNGUNA

Ga abin Allah (Subhanahu wata’ala) ya ce game da  mafificin littattafansa Alƙur’ani mai tsarki. 

Kuma muna saukar da abin da yake waraka da jinƙai a wannan Alƙur’ani ga muminai kuma ba ya ƙarar azzalumai (wato kafirai) da komai sai taɓewa”. 

Kuma Allah ya ce da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam):

“…. ka ce shi (Alƙur’ani) shiriya ne da waraka ga waɗanda suka yi Imani”. 

A sakamako wannan bayani na Allah (Subhanahu wata’ala) Alƙur’ani waraka ne game da matsalolin zukata kuma magani ne game da cututtukan jiki. 

Kuma shi ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake karanta Ƙulhuwallahu da Falaƙi da Nasi ya shafe jikinsa duk dare. 

kamar yadda Hadisi ya inganta cewa ɗaya daga cikin sahabbai ya yi wa wani mutum da kunama ta harba ruƙuya da Fatiha ya warke nan take. 

Kuma an karɓo Hadisi daga Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda da su daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce “Waraka na tare da abubuwa Uku:

  1. Jinin da aka jawo da ƙaho
  2. Maƙwararar zuma 
  3. Lalas (sakiya) da wuta. Sai dai ni ina hana al’ummata yin lalas.” 

Bukhari ne ya rawaito shi. 

Domin karanta Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su Danna nan 

sannan kuma ƙwayoyin baƙin algaru (habbatus-sauda) suna ba da gagarumar gudunmawa wajen kawar da cututukan sanyi, kamar yadda bayani ya gabata.

Nonon raƙumi da fitsarinsa magani ne da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da kansa ya yi umarni da a sha su don samun waraka daga cuta. kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito. 

Bayan haka, addu’a ma na maganta matsaloli da cututtukan da suka addabi bayi, kamar yadda bayani ya gabata cewa, Annabi Ayyub (Alaihis-Salam), ya roƙi Allah ya warkar da ciwon da ya same shi, Allah ya amsa masa ya yaye masa ciwon.

Haka kuma sadaka na maganta cututtuka; ta kuma tafiyar da zunuban bawa kamar yadda ruwa yake kashe wuta. kamar yadda hadisai tabattatu suka tabbatar. 

Amfani da ruwan Zam-zam yana maganin cutar da aka sha shi dominta, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faɗa. 

Domin Dauko Cikekken Littafin Danna nan
labarin da ya wuceYadda ake Rice Chocolate Cookies
Labarin na GabaAmfanin Ƙaho A Jikin Ɗan Adam
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.