Yadda Zaka Bada Agajin Gaggawa Ga Wanda Ya Sha Kananzir (Kerosene)

1
118

Kananzir, petir da sauran dangogin su duk irin agajin gaggawa su iri daya ne. Bayan tambayar da muka yi a wannan shafi, mafi yawancin sakonnin da muka samu ya nuna mutane suna bawa Wanda yasha kananzir wasu abubuwa kamar manja da madara ko a sa yaro yayi amai Wanda duk hakan babban KUSKURE NE!!! 

Me Ya Kamata Ayi?
  • Na farko wanke inda kananzir ya taba da sabulu.
  • Kar ayi kokarin sa yaro yayi amai, saboda kananzir abune mai naso wanda idan aka sa yaro yayi amai zai iya wuce bututun iska ba tafi hunhu (lung) wanda hakan kan haddasa ciwon da ake kira Chemical Pneumonitis, illar sa takan iya fin ta kananzir din da aka sha.
  • Kar a bawa yaro wani abu kamar madara ko manaja, domin basu ta tasiri wajen rage karfin kananzir da aka sha.
  • A kai yaro asibiti

Don haka a gida ba a bawa wanda yasha kananzir komai,wancin abinda mutane keyi shine  ke ta’azzara lamarin.

Jan Hankali Ga Ma’akatan Lafiya Matakin Farko.(for health personnel only)

Lokacin da aka kawo yaro ya  sha kananzir, ya kamata ku sani cewa

  • Ba a bayar da activated charcoal, sai dai idan an hada kananzir din da maganin kwari.
  • Ba a bayar da antibiotics, sai dai idan akwai evidence of infection!
  • A bawa mara lafiya O2 sannan ayi 8observing symptoms (treat the symptoms)

Domin karanta bayani akan Warin Baki (Mouth Odour) Danna nan

labarin da ya wuceWarin Baki (Mouth Odour)
Labarin na GabaAllurar Tsarin Iyali Ta Maza (Male Family Planning)

SHARHI ƊAYA