WikiHausa ta kai ziyara zuwa ENGAUSA GLOBAL TECH HUB a inda shugaban wikiHausa (Isah Uba Chamo); ya haɗu da shugaban cibiyar ENGAUSA GLOBAL TECH HUB (Engr Mustapha Habu Ringim); a inda suka tattauna muhimman abubuwa akan bunƙasa ilimi da sana’o’in hannu a ƙasar Hausawa.





ENGAUSA GLOBAL TECH HUB; Gidan hikima ne kuma babbar katanga ta sabbin fasahohin zamani da ke neman canza labarun dijital a Najeriya; ta hanyar STEM da hanyoyin koyarwa na tushen fasaha na sabbin fasahohi masu tasowa.