Gaskiyar Abinda Ya Faru Na Shahadar Husaini (Radiyallahu Anhu)

0
13

A wannan gaɓa zan bayyana gaskiyar abinda ya faru a taƙaice dangane da shahadar husaini (Radiyallahu Anhu) kamar yadda amintattun masana tarihi suka bayyana.

Mutanen Iraƙi sun sami labarin cewa Hussaini (Radiyallahu Anhu) bai yi wa yazidu mubaya’a ba a shekara ta 60 daga hijira, saboda haka suka yi ta aika manzanni da wasiƙu zuwa gareshi, suna gayyatarsa ya zo don su yi masa mubaya’a, saboda su ba sa bayan yazidu har ma da halifofin da suka gabace shi, su kawai Aliyu da jikokinsa suke buƙata yawan waɗannan wasiƙu ya kai ɗari biyar.

Da husaini (Radiyallahu Anhu) ya ga haka, sai ya tura Muslim ɗan Aƙilu don ya binciki gaskiyar lamarin. Da farko da ya je sai ya ga dubban mutane suna kan wannan ra’aiyi kuma da alama da gaske suke kuma gidan Hani ɗan Urwata shine ya zama cibiyar yin mubaya’a ga husaini (Radiyallahu Anhu).

Da yazidu ya sami labari, sai ya tura gwamnansa na Basra Ubaidallahi Ibn Ziyad Kufa, ya kuma kuma haɗa masa da Basrar, domin ya shawo kan wannan matsala, ya hana mutanen Kufa yin tawaye, amma bai ba shi umarnin ya kashe Husaini ba.

Da ya je Kufa ya yi zurfin bincike har ya gano cewa a gidan Hani Ibn Urwah ake kitsa komai. Ubaidullah Ibn Ziyadu ya yi fito-na-fito ya yi jawabai ga waɗannan dakaru yana razana su da ƙarfin rundunar Sham, yana kuma lasa masu zuma da yi musu alƙawarirrika na kuɗi da muƙami nan dai dakaru suka rinƙa zare jiki suna komawa cikin rundunar zaiyadu, kafin ƙanƙanin lokaci cikin mutum dubu huɗu sai mutum talatin kacal ne suka ragu a bayan Muslim, suma kafin faɗuwar rana sun canza sheƙa.

Shine ya sa aka kama Muslim Ubaidullah ya ba da umarni a kashe shi sai ya nemi a bashi izini ya rubuta wasiƙa zuwa Husaini (Radiyallahu Anhu) sai aka ba shi izini ya rubutawa Husaini cewa: “ka koma gida da iyalanka, kada ka ruɗu da ƙarerayin mutanen Kufa, makaryatane”. Bayan kuwa a da ya rubuta masa cewa yayi sauri ya taho Kufa saboda komai ya yi dai dai. Ubaidullah ya sa aka kashe Muslim Ibn Akil.

Shi kuwa Husaini (Radiyallahu Anhu) tuni ya fito, duk da yunƙurin da manyan sahabbai suka yi domin su hana shi tafiya Kufa, sun yi masa iya nasiha, amma ƙaddara ta riga fata.

Ibn Umar. (Radiyallahu Anhu) ya ce: da shi “Bari in gaya maka wani hadisi, jibrilu ya zo wurin manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ba shi zaɓi tsakanin duniya da lahira, sai ya zaɓi lahira, kai kuwa tsoka ne daga gare shi, saboda haka, wallahi babu wani a cikinku, da zai sami mulki har abada, kuma Allah ya yi muku haka ne, saboda ya tanadar muku abinda ya fi Alheri a gurinku.

Amma husaini bai gamsu da wannan ba ya yi gaba sai Ibn Umar ya rungume shi ya fashe da kuka, yace ina bankwana da wanda za a kashe.

Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce da shi: “ba don kar mu yi abin faɗa ba, da sai na hana ka tafiya, koda kuwa za mu yi kokawa”.
Abdullahi Ibn Zubair ya ce: “me za ka yi a wurin waɗanda suka kashe mahaifinka, su ka soki wanka da wuƙa a cinya?

Abdullahi ɗan Amar ɗan As (Radiyallahu Anhu) yace: “Husaini ya yi gaggawa zuwa ƙaddararsa, wallahi da na tarar da shi da na hana shi tafiya, sai dai in ya fi ƙarfi na”.

Tun akan hanya Husaini (Radiyallahu Anhu) ya sami labarin an kashe Muslim Ibn Aƙil da kuma yadda mutanen Kufa suka ba da shi, sai ya juya akalar tafiyarsa zuwa Sham wurin Yazid, amma sai ya yi kiciɓus da rundunar ɗan Ziyadu a ƙarƙashin jagorancin Umar Ibn Sa’ad da Shimmar Ibn Zil Jaushan da Husaini Ibn Tamim.

Sai Husaini ya sauka daga dokinsa yana yi musu magiya su dubi girman Allah su ƙyale shi da ya kai kansa wurin Yazidu ya yi masa mubaya’a, saboda ya san ba zai so a kasha shi ba, ko ya koma Madina ko ya tafi jihadi har ƙarshen rayuwarsa.

Amma suka ƙi bashi ɗaya daga waɗannan abubuwan guda uku, suka ce sai dai ya yarda yana ƙarƙashin hukuncin ɗan Ziyadu sai abin da ya ga dama ya yi da shi.

Har sai da wani daga cikin kwamandodin ɗan Ziyadu mai suna Al-Huff Ibn Yazid ya ce: “Don me za ku ƙi yarda da wannan tayi da suka yi muku? Ai ko Turkawan Lailamawa suka nemi ɗayan waɗannan abubuwa kwa yi musu”? Amma a banza ba su saurare shi ba. Da ya ga haka, sai ya miƙa wuya ga rundunar Husaini (Radiyallahu Anhu) har ya kashe mutum biyu daga cikin rundunar ɗan Ziyad, sannan suka kashe shi. Ya Allah ka yi masa rahama.

In ana maganar yawa ne, ba za a iya kwatanta yawan rundunar ɗan Ziyad da dakarun Husaini (Radiyallahu Anhu) ba, amma fa duk inda jarumai suka kai sun wuce nan, sun yi bajinta sai da suka ƙare gaba ɗayansu akan bada kariya ga Husaini (Radiyallahu Anhu) ƙarshe ya rage sai shi kaɗai kamar zaki a cikin dubban mayaƙa, ya yi kansu amma sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi.

Duk da haka kowane ɗaya daga wannan runduna yana shayin, afkawa Husaini (Radiyallahu Anhu) har sai da wani tsagera mai suna Shimmar Ibn Zil Jaushan ya yi tsaurin ido ya cakawa husaini mashi, ya faɗo ƙasa daga kan dokinsa, daga nan suka rufar masa da sara da suka har suka kashe shi. An ce shi Shimmar ɗin nan shine ya ciro kan Husaini waɗansu kuwa sun ce Sinan Ibn Anas Annakh’i ne.
Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”.

Haƙiƙa Husaini (Radiyallahu Anhu) da waɗanda suke tare da shi sun rubauta sun kasa sun sayar sun ci riba. Su kuwa waɗannan ‘yan ta’adda sun yi hasara. Ya Allah ka jaddada rahama ga Husaini (Radiyallahu Anhu) da waɗanda suka yi shahada tare da shi amin.

Domin karanta cikakken bayani akan Sauran Waɗanda Suka Yi Shahada Tare Da Husaini (Radiyallahu Anhu) danna nan.

Wannan bayanin anciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana Akan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceSharhin Littafin Ina Son Sa Haka
Labarin na GabaTarihin Sheikh Malam Muhammad Ɗan Almajiri