An haifi Malam Muhammad Barnoma ɗan Gwani Muktari a garin Misau. An ce bayan mahaifinsa Gwani Muktari ya yi hijira daga Barno shi ne ya kafa Masarautar Misau bisa tsantsar Shari’ar Musulunci a wancan lokacin.
Malam Muhammad Barnoma ya taso a garin Misau cikin kulawar mahaifinsa, kuma ya yi karatun Alƙur’ani da sauran fannoni wurinsa. Mahaifinsa Gwani Muktari ya fita da shi daga ƙasa Misau har suka sauka a garin Kila cikin ƙasar Bauchi. Daga nan ne ya dawo Kano ya sauka wurin Mashahurin malamin ilmi Malam Mahmud Salga.
A lokacin kuwa da Sarkin Gumel Nakuta ya nemi Malam Salga ya tura masa wani daga almajiransa don ya karantar da su AIƙur’ani da ilmi, sai ya umarci Malam Muhammad Barnoma da ya wakilce shi. Malam Barnoma ya kafa makaranta a Gumel ya kuma yaɗa ilmi har tsawon shekaru 60. Malam Barnoma ya haifi manyan ‘ya’yansa a Gumel. Da ga bisani ya dawo Kano ya cigaba da ba da karatu har ya rasu.
Bayan rasuwar Sheikh Barnoma, ɗansa Malam Usman Barnoma ya cigaba da jagorantar wannan gida da makaranta.
An haifi Malam Usman a garin Aikawa da ke Gumel a shekarar 1943. Ya haddace Alƙur’ani yana ɗan shekara goma sha huɗu, Malam Usman Barnoma ya yi karatu wurin Malam Sani Lukoro a Unguwar Gyaranya da ke Kanon Dabo.
Malam Usman ya shahara da kyawawan halaye da yawan karamci, ga shi kuma ma’abocin bincike da nazari cikin littafan Musulunci. Saboda irin himmarsa an ce yana karanta izu arba’in a kowace rana. Manyan malamansa sun haɗa da Shehu Atiku da Malam AbdulMajid Salga da Malam Sani Mahmud. Manyan almajiransa kuwa sun haɗa da.
– Dr. Muhammad Nuruddeen Musa
– Dr. Abdullahi Saleh Pakistan
– Malam Mahmud Barnoma
– Malam Hamza Abdullahi
Makarantarsa ta shahara da shigar da tsarin zamani cikin karantarwarta musamman ma sanya kayan makaranta da azuzuwa da sauransu.
Domin karanta cikakken bayani akan Tarihin Alaramma Malam Aliyu Ɗan Kadawa (1868- 1998) danna nan.
Domin karanta cikakken bayani akan Tarihin Fati Nijar danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.
Edita; Rumasa’u M. Kallamu