Description
Sunan Fati Nijar na yanka shi ne Fatima, Mahaifinta kuma Abdurrahman wanda ake yi wa sunan rana Labaran; mahaifiyarta kuma A’ishatu ‘yar Hassan ɗan Tanko.
Fatima (Binta) ta sami sunan fati Nijar daga Sadi Sidi Sharifai a lokacin da take yi masa amshi na waqoqin finafinai.
Labaran bisa asali mutumen Madawa ne cikin Jihar Tawa; kuma xan kasuwa ne mai zagayen garuruwa da qauyuka a ranekun cin kasuwanni a Jamhuriyyar Nijar.