Tarihin Malam Mahmud Manzo Arzai

0
32

An haifi Malam Mahmud ɗan Muhammad ɗan Mahmud dan Muhammad a Damagaran cikin Jamhuriyar Nijar. Malam Mahmud ya zo Kano a lokacin girma ya fara kama shi. Malam Mahmud ya taso a hannun mahaifinsa a inda ya karanci Alƙurani.

Ya shahara da sada zumunci da yawan kyautatawa ga baƙo da ɗan gari. Malam Mahmud ya yi tafiye-tafiye na neman Alƙur’ani izuwa alƙaryu masu nisa irinsu Inkibalwa da tsangayar Kolorum. Don haka ma ya sadu da manyan malamai irinsu Gwani Ahmad da Malam Yahaya da Alaramma Malam Yusuf wanda ake yi wa laƙabi da Malamin Mali da gwani Mahmud halifan Gwani Dipchan (shugaban makaratan Ƙasar Hausa) inda ya naƙalci ilmin Alƙur’ani da Rasmu da Tajwidi.

Malam bai gushe ba yana kutsawa cikin neman Alƙur’ani da fannoninsa, har sai da ya sauka birnin Kano. A lokacin da ya iso kuwa almajirai suka riƙa dandazo don su sha daga tafkin ilminsa. Abu ne mai wahala ƙwarai da gaske ƙididdige yawan almajiran Malam Mahmud Manzo Arzai.

Kaɗan daga cikinsu sun haɗa da Malam Muhamud Danja Zuwo, da Malam Lawan Saleh da Malam Gali Adhama.

Wannan makaranta ta Malam Manzo ba ta gushe ba tana wanzuwa a hannun zuriyarsa cikc da ɗaruruwan almajirai, lokacin da Malam Manzo ya rasu babban ɗansa Malam Muhummad Mahmud wanda aka fi sani Malam Usman shi ya jagorance ta tare da taimakon ‘yan uwansa Malam Muktari Manzo mai koyar da ilimin Tajwidi da Malam Laminu shi ne mai darasu sai Malam Mustafa da Malam Abba da Malam Sunusi da Malam Ibrahim.

Tsokaci

Makarantar Malam Manzo Arzai ta shahara da ladabtar da kangarrarun yara ta hanyar addu’o’i da yi musu tarbiyya da karatun Alƙur’ani da lazimta musu addinin. A inda ake sanya su a mari. Mutane kan taso gari da gari don kawo ‘ya’yansu. Da yawa wannan tsari na tarbiyyantarwa ya kan taimaka wajen gyara tarbiyyar kangagararru har sai ka ga sun wayi garisun kintsu.

Wasu ma sun zama malamai, albarkacin addu’o’i da lazimta musu Sallah akan lokaci da sauransu.

Domin karanta cikakken bayani akan Tarihin Sheikh Muhammad Barnoma danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Takaiceccen Tarihin Rayuwar Dr. Yahaya Tanko danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceTarihin Sheikh Muhammad Barnoma
Labarin na GabaTatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum