Misalan Waƙafi Ababen Koyi A Tarihin Musulunci

0
490

1. Zamanin Halifofi Shiryayyu ba shakka an samiu nau’o’i daban-daban a wannan lokaci, kaɗan daga cikin misalan su sun haɗa da:

Waƙafin da sayyidina Umar ya yi da kasonsa guda ɗari dake Khaibar, wanda ya rubuta wasiyya da kansa da cewa:- “Da sunan Allah Mai rahama Mai jinƙai, wannan takarda sheda ce ta wasiyyar da bawan Allah Umar shugaban muminai ya yi ko wani abu zai faru da shi (yana wasiyya da cewa) Samgah da Sirmata bn Al-Akwa (gonaki biyu) da dukkan bayin da suke cikinsu da kasona guda ɗari dake Khaibara da dukkan bayin da suke cikinsu”..

Waƙafin da Sayyidina Ali Bn Abi-Ɗalib Allah Ya yarda da shi ya yi, wanda ya rubuta shi kamar haka:- “Wannan takardar sheda ce bisa abin da Ali bn Abi-Ɗalib ya yi, ya kuma hukunta da dukiyarsa cewa; na sadaukar da (amfanin gonakinsa) na Yanbu da Wadil-Kura da Azinah da Ra’ah a cikin hanyar Allah; kuma ga ‘yan uwa na kusa da na nesa, kamar yadda ba za a yi kyauta da su ba, kuma ba za a gaje su ba, a lokacin rayuwa ko bayan raina”.

Ba shakka wannan kaɗan ne daga cikin misalai da yawa na waƙafi; a lokacin halifofi shiryayyu, Allah ya yarda da su.

2. Zamanin Mulkin Banu Umayya

Ba shakka akwai misalai masu ƙayatarwa matuƙa na irin nau’o’i daban-daban na waƙafi da aka yi a wancan lokaci. Ga kaɗan daga cikinsu:-

Gina babban masallacin nan na birnin Dimashk wanda har zuwa wannan zamani namu yana nan daram, wanda kuma muka ambata a baya cewa an gina shi a zamanin Halifa Walid ɗan Abdul – Malik wanda aka ruwaito cewa; a lokacin da zai gina wannan masallaci, sai da ya sa aka kawo masa ƙwararru daga ko’ina; waɗanda yawan su da sauran ma’aikatansu ya kai kimanin mutum dubu goma sha biyu.

Ya kuma kashe kuɗi kimanin akwati ɗari huɗu; kowane akwati yana ɗauke da kwabbunan tataccen zinare guda dubu ashirin da takwas. Sai da ya shafe tsawon shekaru ashirin yana ginin wannan masallaci.

Gina Asibitoci Da Hanyoyi Da Rijiyoyi

Haka nan kuma shi dai wannan bawan Allah; shi ne mutum na farko da ya gina asibitoci na musamman don amfanin mutane.

Haka kuma ya gina waɗansu na musamman da ya keɓance su ga masu ciwon kuturta; waɗanda a lokacinsa ya killace su, ya hana su bara; ya kuma ware maƙudan kuɗaɗe don yi musu magani da ba su cikakkiyar kulawa. Haka kuma, ya bayar da umarni ga gwamnansa mai kula da Madinah a wancan lokaci Umar ɗan Abdul-Aziz cewa ya gyara unguwanninta ya kuma gina rijiyoyi, ya kuma ɗauki ma’aikatan da za su rinƙa janyo ruwa don amfanin jama’a.

Haka nan, ya aikawa dukkan jami’ansa a ko’ina kuɗaɗena suke cewa; su ware musamman ga mabuƙata tare da shimfiɗa hanyoyi da gidaje domin saukar baƙi kyauta. Bugu da ƙari kuma, wani kyakkyawan misali na waƙafi don amfanin al’umma shi ne ; yadda halifofin Banu Umayyah na wancan zamani suka bayar da muhimmanci matuƙa wajen gina madatsan ruwa, alal misali, a lokacin halifancin Umar ɗan Abdul- Aziz haka madatsan ruwa a wurare masu ɗumbin yawa kamar su Basra, da Arnmenia, da Dimashk da sauransu.

3. Zamanin mulkin Abbasiyyawa

Ba shakka halifofin zamanin Abbasiyya sun bayar da muhimmanci ga waƙafi a fannin gina asibitoci; da samar da littattafai don horar da ƙananan likitoci, tare da hayar ƙwararru da za su koyar da su duk ta hanyar waƙafi. Kaɗan daga cikin misalan asibitoci da aka gina a wancan lokaci; sun haɗa da asibitocin nan da ake kira Almustashfà Al-adudiy (wanda muka ambata a baya) wanda Haifa Adudud – Daulah al-Buwaihiy ya gina a birnin Bagdad a shekara ta (366 Hijiriyyah /976 Miladiyya) ya kuma ɗauki ƙwararrun likitoci a fannoni daban-daban waɗanda kimanin yawansu ya kai 24.

Komai na asibitin kyauta ne, ga kulawa da marasa lafiya wajen abinci; da abin sha; da ɗinka musu sababbin tufafi, baya ga tsarin bayar da guzurin komawa gida ga duk wani marasa lafiya da aka sallama. Kamar yadda kuma ya zo a littattafan tarihi cewa, waɗansu daga cikin gwamnoni na wannan daula, sukan kashe kuɗaɗe maƙudai wajen yin irin waɗannan nau’o’i na waƙafi kamar yadda aka samu cewa, Ahmad ɗan Dolon gwamnan Masar a wancan lokaci, ya gina asibiti a lokacin da ya kammala, sai ya sadaukar masa da kuɗaɗen shigar da ake samu daga dar addiwan da kasuwar bayi da waɗansu gidaje nasa.

Haka kuma ya kafa ƙa’idar cewa; a cikin waɗanda za su amfana da wannan asibiti ban da manyan hafsoshinsa da fadawansa da ‘ya’yan sarauta; haka kuma duk wanda za a kwantar a asibitin, sai an ba shi sababbin kaya ya sa, tsofaffin kuma za a adana masa su ne har zuwa lokacin da Allah ya ba shi sauƙi sai a damƙa masa kayansa.

Haka kuma akan yi masa sabuwar shimfiɗa a kula da cin sa da shan sa, da yi masa magani, kuma ba za a sallame shi ba, har sai ya warke sarai; ya dawo yana cin duk wani abinci da ya saba ci kafin rashin lafiyarsa.

Haka kuma a waɗansu lokuta akan gayyato likitoci daga wurare daban-daban don bayar da kulawa ga marasa lafiya, wato kamar dai abin nan da muka sani a wannan zamani da ake kira “medical tour”; (wato likitoci ‘yan sha-ka- tafi tare da biyansu haƙƙoƙinsu da ɗaukar ɗawainiyar duk wata buƙata ta su).

Misalai na waƙafi da aka yi wancan zamani ba wai ya tsaya ne kawai ga gina asibitoci ba; haka kuma bai tsaya ga ɓangaren hukuma kawai ba. Wani ɗan ƙaramin misali da zai tabbatar mana da hakan shi ne, wani waƙafi da wani attajiri ya yi mai suna Fakhruddaula bn Almuddalib a birnin Bagdad (ya rasu a shekara ta 578 bayan Hijira ); ya gina wata katafariyar makaranta mai suna Dar Adhdhahab, ya damƙa ta a hannun wani mashahurin malami mai suna Jamaluddin bn Fadlan Ash- Shafi’i ya kuma sadaukar mata da wata dukiya tasa da abin da take samarwa kowace shekara, ya kai kimanin dinare dubu ɗaya da ɗari biyar.

Bugu da ƙari, su kansu mata ba a bar su a baya ba; wajen wannan ayyuka na alheri, domin kuwa ya zo a littattafan tarıhi cewa Sayyida Zubaidah bnt Ja’afar bn Mansur; matar Halifa Harun Ar-Rashid ta haƙa rijiya da ake kira da “ainul mashash a Hijaz” ta kuma sa aka yi wa ruwanta hanya a tudu da gangare; har tsawon tafiyar mil goma sha biyu zuwa garin Makkah; wanda wannan aiki ya lashe kuɗi kimanin dinare miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai; (wanda ƙiyasin kowanne dinare ɗaya a zamaninmu shi ne nauyin giram 4.25 na tataccen zinare).

A ɓangare na makarantu kuwa, tarihi ba zai taɓa mantawa da jerin gwanon makarantun nan da ake yiwa laƙabi da makarantun Nizamiyya ba; waɗanda waziri Nizamul Mulk Addardusi (ya rasu shekara ta 485 Hijiriyya) ya kafa, waɗanda da yawa daga cikinsu suka zamo a sahun farko a tarihin jami’o’i a duniya baki ɗaya. Haka nan ya ci gaba da gina irin waɗannan makarantu a ko’ina a cikin daular Musulunci, kamar yadda aka sami mashahuran malamai da suka koyar a waɗannan makarantu. Alal misali, a daidai lokacin da Imam Al-Ghazali yake koyarwa a reshenta na Bagdad, shi kuwa shahararren malamin nan mai suna Imam Al-Haramain Abu Al-Ma’ali Al-Juwaini yana koyarwa a reshenta na Naisabur.

4. Daular Musulunci Ta Andalus

A haƙiƙanin gaskiya ana iya cewa waƙafi na ɗaya daga cikin alamomin wuraren da daulolin Musulunci; suka kafu a ko’ina a faɗin duniya; domin kuwa shi ne kamar wata alama da ta zama ruwan dare a waɗannan dauloli a tsawon tarihinsu; duk da kasancewar sun kafu ne a wurare daban-daban kuma a lokuta mabambanta. Dalilin faɗin hakan kuwa shi ne, duk da cewa daular Musulunci da ta kafu a Andalus(Spain) ta yi nisa matuƙa; daga ƙasashen Larabawa waɗanda suke gabashin duniya.

Domin kuwa Andalus tana cikin nahiyar Turai ne, to amma duk da haka, nau’o’i daban-daban na waƙafi da aka yi a cikinta, ko kaɗan bai gaza ga waɗanda aka yi a ƙasasshen gabas ɗin ba, a Alal misali, an samu Waƙafi a fannoni da dama a zamanin sarakuna irin su sarki Alhakam ɗan Abdur-Rahman An-Nasir wanda a lokacinsa ne wannan al’amari ya kai ƙololuwar bunƙasarsa, domin kuwa a zamaninsa ne ya sa aka jawo ruwa daga wurare masu matuƙar nisa zuwa ga wuraren buƙatar jama’a, waɗanda suka haɗa da masallacin Ƙurdubah.

Kamar yadda ya yi waƙafi a fannin bunƙasa ilmi tun daga matakin koyon karatu da rubutu; har zuwa ga matakin ƙwarewa a fannonin haddar Alƙur’ani da Hadisi da Fiƙhu da sauransu.

Hakazalika, an sami malamai da yawa waɗanda suka yi waƙafin litattafansu ga manyan cibiyoyin ilmi mai zurfi, kaɗan daga cikinsu sun haɗa da; Al Imam Abul-Ƙasim Abdul-Khaliƙ bn Abdil- Warith as-Sayuri (ya rasu a shekara ta 462 Hijiriyya) da al-Imam Kasim bn Isa bn Naji (ya rasu a shekara ta 839 Hijiriyya).

Wani abin al’ajabi shi ne, ganin cewa yankin Andalus yanki ne mai yawan rafuka; wanda hakan yakan daƙile walwalar mutane matuƙa, sai musulmai na wancan lokaci suka yawaita yin waƙafi wajen gina gadoji. Littattafan tarihi sun ruwaito cewa gadar da ta fi kowacce girma da shahara a wancan lokaci ita ce gadar da sarki Hisham ɗan Abdur-Rahman ɗan Mu’awiya (ya rasu a shekara ta 180 hijiriyya) ya gina wacce ya kashe kuɗi matuƙa wajen gina ta.

Kamar yadda ya ɗauki nauyin sa ido a kan aikin gina ta shi da kansa, wanda saboda da ganin haka har sai da waɗansu mutane suka fara gunagunin cewa; ya gina ta ne don amfanin kansa, a lokacin da labari ya kai gare shi, sai ya yi rantsuwa da cewa, “Ba zai yi taɓa bi ta kan wannan katafariyar gada ba, har sai idan tafiya yaƙi ko wani dalili ne ya tilasta masa yin hakan”.

Kamar yadda kuma waɗansu daga cikin irin waɗannan gadoji sun yi ƙarƙo matuƙa; har zuwa wannan zamani namu, misali gadar da Mansur ɗan Abi Amir ya gina a shekara ta 389 Hijiriyya; wacce ya kashe mata kimanin kuɗi dinare dubu ɗari da arba’in.

Wani abin mamaki dangane da yawaitar nau’o’in waƙafi a daular Musulunci ta Andalus; shi ne wani waƙafi da aka yi na musamman don sayen wani irin nau’i na kifi wanda ake kawowa a wani lokaci na shekara don raba shi ga matalauta; waɗanda ‘ya’yansu ƙanana na iya shiga cikin damuwa ganin yadda ‘ya’yan attajirai suke wadata da shi.

5. Daular Uthmaniyyah

Daular Musulunci ta Usmaniyya wacce Turkawa suka kafa, ita ce daula ta ƙarshe da ta faɗi. Ba shakka tarihin wannan daula cike yake da nau’o’i daban-daban na waƙafi; waɗanda lokaci ba zai ba mu dama mu yi bayanin su a wannnan ɗan ƙaramin littafi ba, to amma a taƙaice duk wani nau’i na waƙafi da muka ambata a baya, to su ma Turkawa ba a bar su a baya ba.

Sannan kuma bugu da ƙari, muhimmancin da suka ba al’amarin waƙafi kai an samu cewa; akwai nau’o’i’ da dama a waƙafi da aka yi a lokacin mulkin wannan daula, kula da dabbobi marasa lafiya.

6. Daulolin Musulunci na Nahiyar Afirka

A haƙiƙanin gaskiya, abu ne mai matuƙar wahala a ce za a ƙididdige irin rawar da daulolin Musulunci na nahiyar Afirka; suka taka wajen bunƙasar al’ummarsu ta hanyar waƙafi. To amma hakan ba zai hana mu ɗan bayar da misalai na kaɗan daga cikinsu ba. Daga cikin mafiya muhimmancin irin waɗannan nau’o’i daban-daban na waƙafi sun haɗa da:

Daular Musulunci ta Songhai

An yi wani shahararren sarki na wannan daula mai suna Mansa Musa wanda ya yi gine-gine masu yawa da suka shafi na makarantu; domin bunƙasa harkar ilmi, ya gayyato tawaga ta musamman ta manyan masana a lokacin da ya je aikin Hajji da kuma gina masallatai guda biyu; na Gao da na Tumbuktu bisa taswirar da ɗaya daga cikin ƙwararru da ya zo da su a fannin gini mai suna Ishak el-Teudjin ya zana masa. Wannan masallaci ne daga baya ya zama shahararriyar jami’ar nan ta Sankore, duk a zamanin wannan sarki, a farkon ƙarni na goma sha huɗu na Miladiyya.

Kamar yadda kuma an samo a tarihi cewa; a shekara ta 988 Miladiyya, an sami wani malami mai suna Al-Kadi Aƙib ɗan Mahmud ɗan Umar; wanda ya lashi takobin cewa; sai wannan gari na Tumbuktu ya tafi kafaɗa da kafaɗa da sauran manyan garuruwa na duniya a fagen bunƙasar ilmi mai zurfi. Domin aiwatar da wannan aniya tasa, sai ya nemi masu hannu da shuni da su taimaka da kuɗaɗe; don katafaren aikin faɗaɗa masallacin Tumbuktu da muka ambata a baya, ta yadda zai ɗauki malamai da almajirai masu yawa.

Wani abin mamaki da ban sha’awa shi ne, sai aka sami wata mata mai dukiya; ta ɗauki nauyin gudanar da aikin ita kaɗai, a cikin dukiyarta a matsayin waƙafi.

Daga baya wannan jami’a ta yi matuƙar shahara; har sai da ta zamo ɗaya daga cikin manyan jami’o’i na duniya a wancan lokaci; wanda har sai da yawan ɗalibanta ya kai kimanin dubu ashirin da biyar (25,000); haka nan katafaren ɗakin karatu da wannan jami’a take da shi daga littattafan da suka kama daga; dubu ɗari huɗu zuwa dubu ɗari bakwai (400,000 – 700,000). Nagartar karatunta ya zarce da yawa daga cikin manyan jami’o’in duniya na wancan lokaci.

Dangane da al’amarin bunƙasa rayuwar al’umma kuwa, wannan daula ta bar wannan abin alfahari da dama; domin kuwa an samo cewa a lokacin wani sarki mai suna Muhammad Askiya, ya yi abubuwa a fannoni daban-daban da suka haɗa da kulawa; da jin daɗin matafiya masu keta hanyoyin sahara da suka gifta ta waccan ƙasa.

7. Tsohuwar Daular Ghana

Wani abin ban sha’awa dangane da ayyukan waƙafi a wannan daula shi ne; bayan Musulunci ya shiga wannan daula ba da daɗewa ba, al’umomin wannnan yanki suka fara aiwatar da abubuwa daban-daban da suka shafi; jin daɗin al’umma ta hanyar waƙafi.

Alal misali addinin Musulunci ya shiga wannan daula ne a kashi na farko na ƙarni na ɗaya bayan Hijira; to amma sai ga shi a cikin shekaru goma da shigarsa; wato a shekara ta 60 bayan Hijira an samu cewa; yawan masallatai dake babban birnin wannan daula; waɗanda aka gina a ɓangarorin da musulmai suke; sun kai kimanin masallatai goma sha biyu; kowannen su cike yake da manyan malamai da ɗalībai a fannonin ilmi da dama.

8. Zamanin Da Muke Ciki

Kamar yadda muka ambata a baya cewa waƙafi wata babbar alama ce ta samuwar al’ummar musulmai a duk inda suke; ba shakka za mu iya ganin hakan har a wannan zamani da muke ciki; domin kuwa an sami mutane masu son aikin alheri da ƙungiyoyi waɗanda suka bayar da misalai ababan koyi na waƙafi. Ƙadan daga cikin waɗannnan misalai sun haɗa da:

Tsarin Hannun Jarin Waƙafi Na Annur

Wannan wani tsari ne da waɗansu bayin Allah suka yi. Reshen wannan gidauniya yana ƙasar Malaysia, to amma tana aiwatar da ayyukan waƙafinta a ko’ina a faɗin duniya. Ta hanyar da wannan gidauniya kuwa take gudanar da ayyukanta shi ne, ta tsattsara ayyukan da take son aiwatarwa; sannan sai ta rarraba shi a sigar hannun jari kowanne da farashinsa; wato abin nufi, iyaka yawan hannayen jarin da mutum ya saya, su ne gudunmawar da ya bayar wajen aiwatar da waɗannan ayyuka; waɗanda ake fatan ladansu zai ɗore har bayan rayuwar wanda ya bayar da taimakon.

Wani misali na irin waɗannan ayyuka shi ne, wani tsari na juya kuɗaɗen taimakon da aka tara a cikin gidauniyar, ta hanyoyi masu sauƙin asara; idan ƙarshen shekara ta yi, sai a buga Alƙur’anai a raba da sunan wanda ya zuba jarin don yin haka kowacce shekara.

Gidauniyar mai Martaba Muhammad Rashid Al Makhtum.

Wanda ya kafa wannan cibiya shi ne sarkin Dubai wanda sunansa ne take ɗauke da shi. Manufar wannan cibiya shi ne, bunƙasa fannonin ilmi na Musulunci da fannonin ilmin kimiyya da fasaha; ta hanyar bayar da tallafi ga ‘ya’yan talakawa ‘yan baiwa, don su sami ilmi da horo a waɗannan fannoni. Wani abu da zai ba mai karatu sha’awa dangane da wannan gidauniya shi ne, irin maƙudan kuɗaɗe da ake ware mata; waɗanda sun kai dubunnan miliyoyi a kowacce shekara.

Hubusin al Rajhi ɗan ƙasar Saudıyya, a inda kafin rasuwarsa ya yi wasicin dukkan dukiyarsa, a matsayin waƙafi ga talakawa da ayyukan alheri, bayan fitar da haƙƙin magada. Ubangiji Maɗaukaki kaɗai ne Ya san adadin talakawan dake rayuwa da iyalinsu cikin wannan dukiya mai albarka.

Waƙaful Umm:

Wannan wani sabon tsarin waƙafi ne na zamani kamar Annur na Malaysia. Da farko akan shata wata kadara mai nauyi, sannan a kasa ƙimarta zuwa ƙananan kaso na mai ƙaramin ƙarfi; don ‘ya’ya masu albarka su saya wa mahaifansu rayayyu ko marigaya. Jimillar kuɗin ita ce za a sai waccan kadara a bayar da hayar ta ga kamfanonin kasuwanci. Ribar ita za ake aiwatar da ayyukan alheri da ita. A halin yanzu wannan tsari na gudana a wasu daga ƙasashen Larabawa; Don ƙarin haske sai a duba littafinmu Jagorar ayyukan Cigaban Al’umma Mai Ɗorewa.

Domin karanta cikakken bayani a kan Nau’o’in Masu Amfani Da Waƙafi Ko Hubusi danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmowar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceYadda Ake Turaren Sikari
Labarin na GabaAbubuwan Da Suke Hana Wadatar Zuci